MATAR DATTIJO page 16

1.6K 69 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Amina Nasir*

*godiya ta musamman gare ki yar uwa,Suhaima M Bello ban san da irin bakin da xan gode miki ba sai dai nace Allah ya bar xumunci*

16

kirana innah tayi da hanxari na karasa wajenta, ledar kayan da aka bani a wajen gyaran jiki na gani a gabanta, fito da maganin ta shiga yi fara tsiyaya min tayi a cup,ungo karbi ki sha, tunda kika xo da kayan nan baki taba amfani da su ba saboda shiririta, turo baki nayi xan fara kuka ni wallahi innah baxan sha wannan dacin ba, menene amfanin na rika shan abinda babu dadi ni Allah ki kirata ma taxo ta dauki kayanta,ajiye mata cup din nayi na koma gefe na cigaba da buntsure-buntsure na.

lallaba ni ta shiga yi, kisha Niimatullah dama magani ai ba dan dadi ake sha ba, sai don a samu fa'ida kuma nasan xaki ga amfaninsa nan gaba, don xaki samu soyayyar mijinki dari bisa dari.
kallonta nayi ina dan hawayena ni dai baxan sha ba innah, ko ban sha ba xai so ni, yanxu ma fa yana fada min yana sona sosai, ni na bar miki ma ki shanye gaba daya innah tunda yana da amfani.
tsayawa tayi tana kallona, wai yaushe xaki daina wannan taurin kan naki Niimatullah?Kullum sai an yi fama da ke a kan shan magani, xan karbi lambar malamar taku duk ranar da baki sha ba sai na kirata na fada mata, tunda ni bakya jin maganata. kuka na fara yi kiyi hakuri innata wallahi idan kika fada mata wanda xata bani sai ya fi wannan daci.

kiran wayar innah aka yi hannu tasa ta dauka, kirana tayi, xo ki duba ki ga wane ne ya kira, a sanyaye na karaso na karba wayar ina dubawa naga sunan dattijona, bata fuska nayi nace mata shi ne ya kira innah, dubana tayi wanene shi Niimatullah? wannan tsohon mana innah ko kin manta shi, hararata ta yi, bakya jin magana mijin naki kike kira da tsoho, ko ma dai menene ai da shi xa kiyi rayuwa, ki kira shi da abinda ya fi tsoho ma ni ba ruwana.

turo baki nayi to innah ba Gaskiya na fada ba, ke fa kika fada min duk abinda xan fada na rika fadar gaskiya, shiru innah tayi sai kawai girgixa kai da take yi, numfasawa tayi sannan tace xo ki dauki wayar don nasan da ke xai yi magana.

dukan kasa na fara yi da kafata ni Allah baxan dauka ba innah, ina dauka xai fara yi min irin maganar da baba ya hana ya rika yi min, rarrashina ta fara yi nace duk magana iri  wannan ki rika shiru da bakin ki bana so ki rika fada saboda sirrin mijinki ne. duk rarrashin da tayi min a kan na dauki wayar amma naki dauka, sai da ta gaji da ringing ta katse.

sake kiran wayar yayi sai innah ce ta dauka, bayan sun gaisa yake tambayarta ina nake, murmushi innah tayi yau amaryar taka daru take ji, abu kadan sai ta hau kuka wayar ma tace baxa ta dauka ba, kuma taki shan maganin gyaran jikin da aka bata, murmushi yayi ai Niimatullahina akwai rigima, Allah dai ya bani ikon riketa amana, amsawa tayi da ameen, rokon innah ya fara yi dan Allah ki lallaba min ita innah ina so xa mu yi magana da sauri ta kara min wayar a kunnena, cikin kasalalliyar murya ya fara min magana,

Haba matata ta kaina me yasa xaki ce baxa kiyi magana da marayan mijinki ba, ki min magana ko xan samu saukin radadin da ke damuna, maganar ki ita take sawa naji saukin jarabar da ke taso min idan bana tare da ke, lumshe idanuna nayi muryata a kasa nace in wuni, cike da tausasawa ya amsa min da lafiya lau, kiran sunana yayi my Ni'imah!! A hankali na amsa masa, cike da shagwaba ya fara yi min magana.

ki taimaki dan mijinki ki rika amfani da duk abinda aka baki, ko bakya son ki rikita dan dattijonki ne? shiru nayi ba tare da na bashi amsar maganarsa ba, kin yi shiru my Niimatullah a sanyaye na bashi amsa.

Ni fa a kan na rika shan kayan dacin nan gara na hakura da gyaran jikin gaba daya, dama ai babu abinda take koya min idan ba iskanci ba, duk abinda innata ta hana ni shi take sawa nayi, daga yau ma baxan sake  xuwa ba, na karasa maganar ina son yin kuka.

murmushi yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunnena, yanxu kula da miji da tarairayarsa ne iskanci, lallai da sauranki yarinyar nan, kowace mace da kike gani haka take yiwa mijinta.

kuka na fara yi masa Allah ba haka masu  aure suke yi ba, ga innah da baba nan ai su ma masu auren ne amma ban taba ganin baba yace xai taba hannun innah ba, toshe baki yayi subhanallah ki daina bada misali da baba kinga iyayen mu ne kin ji ko? gyada kai nayi nace to, nasiha ya cigaba da yi min, ki daure ki rika bin duk abinda malama ta sa ki, xa kiga amfaninsa a gaba, ina so muna fara amarci ki rika saka ni kukan dadi, ware idanu nayi dama dattijo yana kuka?

Dariya ya rika yi, sosai ma kuwa xa kiga yadda xan rika kuka idan na fara karbar kulawa daga wajen ki yar yarinyata, nasan idan na same ki na samu aljannar duniya Kullum ina jikin ki ina hutawa ta,  bata fuska nayi, yanxu duk girman nan naka sai ka xauna a jikina tabdi idan na karye fa?

murmushi yayi baxan karya ki ba amanata, idan ma na karya ni xan dora abata.

kukan shagwaba na fara yi ka kashe wayarka bacci nake ji, bacci yanxu Niimatullah? da ina kusa xuwa xan yi mu yi tare don nasan xaki fi jin dadi ga ki ga mijinki.

da sauri nace a'a kayi xamanka, murmushi yayi okay korata ma kike yi ko, to gani nan xuwa yau a hotel xamu kwana sai ki kore ni da hujja, hakuri na shiga bashi don nasan xai iya xuwa ya tafi da ni, bayan mun gama magana ya fada min gobe xai xo da wuri mu je wajen gyaran jiki.

Washe gari da wuri yaxo ya dauke ni muka tafi,yau ma har ciki ya raka ni bayan ta koya min kula da kaina sannan ta fara shafa-shafa min wasu abubuwa wai na gyaran jiki ne, kowane lungu da sako na jikina sai da aka shafa, tana min ina kuka har aka gama, yau ma dai sai da muka yi fada da ita sannan na sha maganin, wasu ta kara bani tace lallai na sha a gida, da misalin karfe biyu na rana yaxo daukana, har bakin motar shi ta raka ni, bayan sun gaisa take xaulayarsa.

Alhaji anya amaryar nan taka tana so ta rikita ka kuwa, Kullum sai na sha fama take shan magani, kunnena ta ja wannan yar tawa ta fiye taurin kai wlh.

da wani shu'umin kallo ya bini yana sakar min wani hadadden murmushi, saboda gyran jikin da aka yi min ni kaina nasan nayi kyau, gaba daya fatata ta canja sai kyalli take, ga wani kamshi da nake yi na musamma. lumshe idanu yayi sannan ya bata amsa.

Hajiya a cigaba dai da hakuri a kula min da babyn tawa haka nake fama da rigimarta kullum, murmushi tayi ai Niimatullah hukuma ce sai rarrashi Alhaji murmushi suka yi gaba dayan su.

hannu ya bude min alamar na shigo kirjinsa noke kafada nayi ....... murmushi yayi tunda baxa ki xo ba to shiga mota mu tafi, sallama tayi mana ta wuce xuwa Office dinta.

Har yanxu bai daina damuna da jarababben kallon shi ba, hannuna ya rike da sauri na kwace na mayar da shi cikin hijab, murmushi yayi yana dubana Niimatullah fadan ki yayi yawa amma xan yi maganin ki, shiru nayi masa ya rika maganganunsa ba tare da na bashi amsa ba.

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now