MATAR DATTIJO page 49

807 16 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*jeeddah Tijjani*
       *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

49

Fitowa suka yi daga gidan suna tafe suna tattaunawa a kan yadda xasu bullowa halin da hajiya Maryam ke ciki, sun yi tafiya mai nisa, sannan suka fara tunanin inda xasu nufa don warware matsalar, kasancewar dukannin su suna cikin damuwa da al'ajabin yadda niimatullah ta rikita maryam dare daya ta kasa gane kan mijinta, kawarta ce ta dube ta, yanxu so nake na kai ki inda xa a baki shawarwari da kuma hanyar da xaki bullowa wannan shaidaniyar amaryar taki,saboda idan kika barta illah mai yawa xata yi miki watan wata rana ma korarki xa a yi daga gidan gaba daya, ke da mijinki sai kallo. mai adaidaita sahu suka tare inda suka fada masa suna bukatar ya kai su unguwar farawa, gidan kawar su suka nufa suna zuwa suka fada mata abinda ya kawo su, shawarwarin yadda xata cutar da niimatullah ta bata da irin musgunawar da xata yi mata, har ta koreta daga gidan sannan kuma cikin da take takama da shi ya xube, ba tare da sun shirya  faruwar hakan ba.

bayan sun gama kulle-kullen da xa su yi suka ci abinci suka yi hira,Hajiya maryam bata dawo gida ba sai bayan sallar isha.

A waje ta ci karo da yayanta tun daga nesa suka hangota, da fara'a suka karaso suna yi mata barka da zuwa, wani mummunan kallo ta watsa musu gaba daya suka koma gefe jikin su a sanyaye, kai tsaye daki ta shige ta dauki waya ta fara kiran dattijo don ta shirya masa makircin da xai sa ya dawo gida bai shirya ba. sai dai tana kiran wayar ta ji ta a kashe, cike da bacin rai tayi jifa da ita tana mayar da numfashi xuciyarta har tafasa take  saboda takaici.

Bandaki ta shiga don yin wanka ko xata ji saukin bacin ran da ke damunta, tana shiga taji wani jiri yana dibanta, rike kofar bandakin tayi don kada ta fadi, gaba daya ta daina ganewa saboda jirin da ke dibarta, fasa wankan tayi ta koma ta xauna a hankali ta rarrafa ta fito waje,kiran yayanta ta shiga yi da hanxari suka karaso don ganin abinda ke faruwa da ita.

ganinta suka yi kwance har ta fara galabaita cike da damuwa suka karaso suna tambayarta abinda ya faru da ita, sai dai bakinta ya kulle ta kasa magana, kinkimarta suka yi suka kaita asibiti don gano abinda ke faruwa da ita.

Bayan likitoci sun gama bincike ne suka tabbatar da cewa tana fama da matsananciyar damuwa wanda idan ta cigaba da kasancewa a wannan halin xai yi sanadiyyar rasa rayuwarta gaba daya, cikin kuka yayanta ke mata magana ki taimake mu mama ki raba kan ki da wannan damuwar, ki daina tashin hankalin ki a kan abinda bai kai ya kawo ba, ki mikawa Allah lamarin ki komai yayi xafi maganinsa Allah, nasihohi masu ratsa jiki suka rika yi mata,suna kwantar mata da hankali  tun daga wannan lokacin kullum cikin rashin lafiya take yau da dadi gobe ba dadi kuma duk da haka xuciyarta cike take da jin haushin niimatullah ko kadan bata jin kaunarta a ranta.

******
Tsaye nake na jingina kaina a jikin dattijona ina masa kuka, Allah ni babu inda xaka je yau sai ka mayar da ni gidan innata,kai kuma ka tafi gidanka na gaji da wannan xaman yau satina biyu ban ga innata ba sannan ga damuna da kake yi da yawan bukata, ni gara mu koma gida ka sasanta da matarka a raba kwana kowa ya rika shan aiki, ga shi innah ma har tayi fushi ko kiran mu bata yi tasa mana ido ta ga yadda xa mu yi.

tsayawa yayi yana kallona yana murmushi, cike da kulawa ya dube ni, yanxu kina so ki fada min cewa kin gaji da dawainiya da mijinki ne niimatullah, cikin marairaicewa na amsa masa ba gajiya nayi da kai ba, amma hidimarka tana da yawa ni kadai baxan iya kulawa da kai ba, dan Allah yau mu koma gida ka sulhunta da aunty kaga ita ma tana da hakki a kanka.

rausayar da kai yayi yana dubana, xamu koma amma ba yanxu ba ki bari na dawo daga office xa mu yi magana, bakin kofa na raka shi muka yi sallama sannan na dawo, kayana na shiga xubawa a akwati don yau nayi alkawarin baxan sake kwana a wannan gidan ba sai a gidan innah ko a gidansa.

Kaya ya gani na tare a gabana ina buntsure-buntsure a hankali ya tako har inda nake tare da cewa yau ko sannu da xuwa baxa ki yi min ba Niimatullah? Rausayar da kai nayi kaina na sunkuyar sannan na far yi masa magana, ni gida xaka mayar da ni nayi alkawarin baxan sake kwana a gidanka ba, cike da kulawa ya dube ni, idan baki kwana a gidana ba a gidan wa xaki kwana amaryar dattijo?kiran wayar shi da aka yi shi ya katse mana maganar da muke yi, don haka yayi saurin saka hannu a aljihu don dakko wayar.

Number Hajiya maryam ya gani tana kiran shi, mayar da ita aljihu yayi ya dawo da kallon shi gare ni, cikin sanyaya murya na fara yi masa magana, ko baka fada min ba nasan wacce take kiranka amma baka dauka ba, ka daina irin wannan dattijona ba kyau, matsowa yayi daf da ni tare da jan hancina ban san lokacin da kika fara wa'azi ba Niimatullahi kullum sai kin yi min magana a kan matar nan da ita ce fa ko tunawa da ke baxa tayi ba.

Muna cikin maganar ya sake jin shigowar text message, a hankali yasa hannu ya dauki wayar number dan shi munir ya gani, karanta text din ya shiga yi.

'''innalillahi wa innah Ilaihi raji'un Allah ya yi wa mama rasuwa yanzu'''

Hannun shi na gani yana karkarwa,  saurin mikon min wayar yayi bakinsa na rawa ya kasa magana, karba nayi na fara karantawa, Aunty ta mutu dattijo?? wani jiri naji ya debe ni a take na fadi sumammiya.

*Follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*Jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now