MATAR DATTIJO page 27

1.6K 78 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha shu'aib zakirai*

27

Rungume nake a kirjin dattijona labarai masu dadi ya cigaba da bani, wasu a kan matar shi da irin musgunawar da take masa, wasu kuma a kan al'amuran da suka shafi rayuwar shi a cikin labaran yana dan nuna min yadda yake shaukina da hakurin rashina da yake yi.

dada manna ni yayi da jikinsa tare da sumbatar fuskata,
Allah ya sani ina matukar kaunar ki Niimatullah hakan ne ma yasa na aure ki, don na rika ganin kyakkyawar fuskar ki a kusa da ni, kuma ki rika debe min kewar rashinki, ki tausaya min matata na samu damar jin dumin jikinki, Allah ya sani zina bata taba burge ni ba, kuma bata cikin ra'ayina amma da tuni na dade da lalacewa.

don a wanan lokacin da muke ciki mata da yawa suna kawo min kansu domin mu kara musu matsayi ko wata alfarma, ina ganin wasu na yi amma ni hakan sam bai taba burgeni ba, saboda bana son na kasance cikin masu sabawa Allah ta hanyar neman matan da basu halatta a gare su ba.  domin Allah ya tanadi axaba mai yawa ga masu aikata xina, wannan dalilin yasa na auro ki domin ki share min hawayena ki tsamo ni daga wannan bakar rijiyar da na dade a cikinta.

cike da kulawa nace xan tsamoka babyna, xan fadawa innah ta kawo min igiya na janyoka, murmushi yayi gami da dukan bayana ba irin wannan nake nufi ba,wai ke a dole sai kin kadar da hankalina ko Niimatullah? to ai na gano ki.

haka muka zauna  muna hira yana bani labarai da kuma shawarwari masu yawa,sannan ya nusar da ni a kan illar gujewa shimfidar miji.

jikina naji duk yayi sanyi nayi nadamar guje masa da nayi a baya,sannan kuma na tausaya masa irin halin da ya samu kansa a ciki,sai dai har yanxu ina jin baxan iya sallama masa kaina ba saboda ina jin fargabar hakan, ga kuma son xuwa ganin innata da nake yi,shawara na shiga yi da xuciyata wata xuciyar tace na yarda da shi wata kuma tace kada na yarda na kyale shi xai sakko da kansa.

Alwala muka dauro tare sannan yaja mana jam'i muka yi sallah, bayan mun idar mun yi addu'a ne naga ya tashi tare da cewa ina xuwa uwar yayana.

fita naga yayi bai dade ba ya dawo hannun shi dauke da leda, ashe gidan abinci yaje ya siyo mana, cike da shagwaba na dube shi, me yasa kake son kashe kudinka dattijona?ai ni ya kamata na dafa maka duk abinda kake so, fuskar shi a sake yake min magana, bana son kisha wahala ne shi yasa Niimatullah, kinga ke amanata ce.sai da ya ciyar da ni abincin sosai na koshi ya bani lemo sannan ya kyale ni.

bayan mun  kammala cin abincin ne ya shiga bandaki yayi wanka, yana fitowa ya tsaya jikin dressing mirror yana kallona tare da kashe min ido, cike da soyayya yake min magana.

my Niimatullah taso ki shafa min mai, makale kafada nayi tare da cewa a'a ka shafa da kanka, shagwaba ya hau yi min har da buga kafa a kasa a lallai ni xan shafa masa, tunawa da nasihar innah nayi na cewa kada na xama mai gardama a gare shi, cike da nutsuwa na dakko man na shiga shafa masa, ina fara shafa masa naji yace wash Niimatullah!! a firgice na tambaye shi lafiya dattijona bayan naka ne yake ciwo? cike da shagwaba ya daga min kai tare da cewa eh ciwo yake amma da kike shafawa naji ya fara sauki, cigaba nayi da shafa masa har na kammala, sake dubana yayi kamar xai yi kuka, tambayar shi nayi abinda yake bukata.

cikin shagwaba yace sai na dakko masa kayan da xai sanya, kananan kaya masu kyau na dakko masa kafin na mika masa sai da na feshe kayan da turare sannan na mika masa, kawar da kansa yayi gefe, ni Allah baxan saka ba tunda dai ina da ke kece xaki saka min.

kallon shi nayi kamar xan yi kuka, haba dattijona dan Allah ka saka ai nayi kokari da na dakko maka, kallona yayi tare da lumshe idonsa, idan fa baki saka min ba da towel xan kwana kuma kin san idan bacci yayi bacci tsaf xai yaye ko? da sauri na karba na shiga saka masa kayan, da wandonsa da towel na hada na saka masa, shagwaba ya fara yi min a kan hakan baxai yiwu ba kowanne sai dai na saka masa daban, kuka na fara yi masa da kyar ya hakura ya daka abin shi da kansa.

da misalin karfe goma na kwanta saboda har yanxu akwai yar gajiya a jikina sallama yayi min ya nufi inda yake kwanciya, har ya kai bakin kofa na kira shi, cikin tausasa murya nake masa magana dan Allah yau idan na kwanta kada tashe ni kaga nayi maka aiki na gaji da yawa, murmushi yayi kada ki damu Niimatullah baxan tashe ki ba ai ina son farin cikin ki, kulle min kofar dakin yayi tare da cewa sai da safe amaryar dattijo, bayan na kwanta bacci ya dauke ni kawai naji mutum makale da ni, muryar sa naji kasa kasa yana yi min magana kiyi hakuri ki barni naji dumin jikinki ki taimake ni na nuna miki tsantsar son da nake miki, kinga yau har mun ci kwana biyu a cikin kwanakin da xan yi a dakinki ki bani dama na baki kulawa a kwanaki biyar din da suka rage mana, cikin kuka na juyo ina masa magana.

mun yi alkawari fa da kai a kan baxa ka dawo ba to me yasa xaka karya min dattijona? shafa kaina yayi son da nake miki da begenki su suka hana na cika miki alkawarin ki Niimatullah har na kwanta na kasa bacci ji nayi duk duniya babu abinda nake bukata sama da ke, ki taimaki mijinki ki bashi abinda ya fi so daga gare ki.

sarrafa ni ya fara yi ta ko ina, yayinda ni kuma jikina duk ya hau rawa saboda tsoro da fargabar haduwa da shi ta kama ni, amma kuma na kasa hana shi abinda yake yi hannunshi naji ya saka yana kokarin cire min riga, da sauri na rike hannun shi na fara kokarin hana shi aikata abinda yayi niyya, kwace hannun yayi inda ya samu nasarar cire min riga dukiyar fulanina ta bayyana a fili, ihu na fara yi ina kiran innah da baba, sarrafa ni ya shiga yi ko ta ina, ji nayi ina kokarin fita daga hankalina saboda irin abubuwan da yake min, cikin kuka nake rokonsa yayi hakuri amma bai ma san a duniyar da yake ba.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now