MATAR DATTIJO page 15

1.7K 76 2
                                    

💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*ina matukar godiya da kika bani kyautar page Zahra Galadima, Allah ya bar xumunci*

*masu son dattijo kwalelen ku domin Niimatullah tuni ta dade da mallake xuciyar mijinta, intisar da jeedda har da wani mayar da sunanta Niimatullah Sbd cusa kai, to kwalelanki😜*

15

Da sallama na shiga gida tarar da innah nayi tana tankade, karasawa nayi wajenta na shiga bude mata kayan da aka bani a wajen gyaran jiki, ba karamin farin ciki tayi ba da taga kayan, albarka ta rika sakawa dattijona tana masa fatan Alkhairi.

tsayuwar mota muka ji a kofar gidan mu, da sauri na janyo hijabina na saka saboda nasan dattijona ne ya sake dawowa, da sallama aka shigo gaba daya muka mayar da hankalin mu ga mai yin sallamar tare da amsawa, matar nan da ta taba tare ni a hanyar makaranta muka gani, a firgice na mike tsaye ina dubanta, wani irin kallo take yi min ni da innah, mamaki ne ya kamani ko ta yaya ma tasan gidan mu? wani kallo take mana wanda mu kanmu baxa mu iya fassara na menene ba, innah ce tayi karfin halin tambayarta.

Baiwar Allah lafiya kika shigo kika tsaya ba magana?wata harara ta watsa mata, lafiyar ce ta kawo ni matsiyatan banxa wadanda basu gaji komai ba sai tsiya, ga ki tsohuwa amma tsohuwar banxa kin shiga kin fita kin min asiri kin raba ni da mijina saboda kawai yarki ta shigo ta aure min miji, a kwana biyun nan gaba daya na rasa kansa tunda aka daura masa aure da wannan kaxamar jakar jikar taki, ba shi da aiki sai ya shige daki yana waya da ita, to wallahi ga gida nan ki shigo amma ki tabbatar da cewa irin rayuwar yar bora xa kiyi, ke da mijina sai kallo, tun baki shigo ba ya fara juya min baya ina kuma ga kin shigo, kwadayin abin duniya ne dai yasa kika aure shi, don haka kin yi ban kwana da samun soyayyar mijina mu xuba mu gani tsakanin ni da ke, tana gama fada ta juya har ta kai bakin kofa ta sake dawowa.

Au na manta ma ban fada miki ba idan don soyayya xaki shigo to ki rike a ranki mijina ba namiji bane, kinga kudi kika aura ba namiji ba. gabana ne ya fadi hawaye suka cika idanuna tana gama maganar ta fita ta bar mu cikin jimami. kan innah na fada ina kuka ni wallahi innah baxan iya da matar nan ba, kina ganin dai irin abinda take fada a kan mu tana cewa kwadayi ne yasa na aure shi ni dai wallahi sai an fasa, gashi har tana cewa ba namiji bane, me take nufi da hakan innah? cike da damuwa innah ta dube ni, ki kwantar da hankalin ki Niimatullah duk wannan abin da take yi kishi ne, amma batun tace mijinki ba namiji bane karya take, idan ba namiji bane ya aka yi suka haifi wadannan yayan da take takama da su, kawai dai tana so ne ta karya miki gwiwar shiga gidan mijinki, ki kwantar da hankalin ki babu abinda ta isa tayi miki sai abinda Allah ya kaddara miki.

Haka innah ta rika kwantar min da hankali amma duk da haka ban samu nutsuwa ba, saboda duk abinda xai tayar min da hankali bana son shi, bayan tafiyar matar da kadan yaxo, kirana yayi a waya yace naje na same shi a waje, cikin shagwaba na fada masa baxan iya xuwa ba sai dai shi yaxo da kansa.

A tsakar gida ya same mu gaisawa yayi da innah sannan ya koma gefe ya tsaya, ganin mu yayi duk a cikin damuwa tambayar innah ya shiga yi, cikin nutsuwa innah tace masa ba komai, duk nacin da yayi a kan ta fada masa amma taki fada, juyowa yayi ya dube ni Niimatullah ina so xa mu yi magana, turo baki nayi ka fada a nan kowa ya ji, inna ce ta dube ni tashi kije mana Niimatullah.

daki muka shiga, ina shiga innah ta kira ni, saura ki fada masa abinda ya faru bana son ki hada ma'aurata fitina ki kyaleta duk abinda tayi ita da Allah, amsa mata nayi da to sannan na koma, wani jarababben kallo yake bina da shi, cikin nutsuwa na taka har na isa wajen da xan xauna, gefe na samu na rakube, cikin karamar muryarsa ya kira sunana my Niimatullah, a hankali na amsa masa.

kallo yake min mai cike da alamomin tambaya, me yasa na ganku a cikin damuwa ke da innah, hankalina ya tashi da naga yanayin da ku ke ciki, ki fada min damuwar ku dan Allah. hannu nasa a fuskata na fara murxa idona xan yi kuka, rarrashina ya shiga yi kiyi hakuri ki fada min kada kiyi kuka.
cike da shagwaba nace innah tace kada na fada maka saboda kada na hada ka fada da matarka, yana jin abinda na fada yasan inda maganar ta dosa, Ajiyar xuciya yayi tare da girgixa kai

kuka na fara yi, ka sake ni dan Allah ka daina xuwa gidan mu, na fasa auren nan naji tace kai ba namiji bane, dan Allah ka fada min Gaskiya da gaske ne kai din ba namiji bane? murmushi yayi to idan ni ba namiji bane menene babyna? turo baki nayi nima ban sani ba.
kallona yayi yana murmushi, to ni namiji ne Niimatullah ko baki yarda ba? gyada kai nayi gaskiya ban yarda ba saboda ance akwai mata maxa, dariya na bashi sosai ina sonki my Niimatullah, ni namiji ne gwarxon namiji ma kuwa, ko kina so kiga xahiri, da sauri na amsa masa da eh, hannu yasa xai kamo ni da hanxari na kauce ina ihu.

Dariya ya rika min, tunda kina tunanin ni ba namiji shi yasa xan fara nuna miki yanxu, dago idanu nayi ina duban shi, to ai nasan kai namijin ne tunda kaya ma irin na maxa kake sakawa amma matarka.......har xan karasa na tuno da abinda innah ta fada min, tsare ni yayi da ido amma me? kaina a kasa nace ba komai.

matsowa yayi daf da ni, ki fada min ko kuma nayi miki kuka, sunkuyar da kaina nayi innah tace kada na fada maka, lallaba ni ya shiga yi, fada min yar matata babu wanda xai ji abinda muka tattauna.

matsawa nayi sannan na bashi amsa, matarka ce tace kai ba namiji bane amma dan Allah kada ka fadawa innah,  murmushi yayi baxan fada mata ba my niima, amma xan miki wasu yan tambayo yi.

kin taba ganin mata maxa yayi aure?girgixa kai nayi alamar a'a, to ki kwantar da hankalin ki namiji xaki aura kuma gwarxo a cikin maxaje, ta fada miki haka ne don kiji tsoro ki fasa, ni kuwa bata san cewa baxan iya rabuwa da yar kyakkyawar matata ba, turo baki nayi ni fa masifar matar nan taka ma ta fara isata, tsoro nake ji kada wata rana ta xane ni, murmushi yayi tare da dago fuskata, ki kwantar da hankalinki indai kina tare da ni babu abinda xata yi miki kin ji ko, to nace masa kwantar da ni yayi a kafadarsa yana shafa gashin kaina, sai da ya gama kwantar min da hankali sannan ya tafi.


*jeeddahtulkhair

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now