MATAR DATTIJO page 18

1.5K 68 0
                                    

💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha Bala ilu (iluwa)*

18

A bakin kofar gida ya ajiye ni hannunsa cikin nawa, sai da ya rako ni har soro,  sannan ya juya ya tafi yana waiwayena,da sallama na karasa cikin gida xaune na tarar da innah ta hada kai da gwiwa, a sanyaye ta amsa min sallamata, cike da damuwa na karasa wajenta murmushi ta rika min, sannu da xuwa yar lelen baba amsawa nayi tare da kwantar da kaina a cinyarta, kallona ta shiga yi tana yaba irin kyaun da nayi da irin kwaxon da mai gyaran jikin ke yi a kaina, tambayarta na shiga yi me yasa naga kin hada kai da gwiwa innah? fuskarta a sake ta bani amsa, jinki da nayi shiru baki dawo bane ya daga min hankali amma ai Alhamdulillah tunda kin dawo lafiya, murmushi nayi yauwa innata na gode da son da kike nuna min, kin san ina muka je? saurin kallona tayi bance ki fada min ba duk irin wannan maganar na hana ki Niimatullah bana son jinta, cike da shagwaba nace ba wannan abin fa xan fada miki ba innah, gaba daya ta bayar da hankalinta gare ni, to ina sauraren ki, gyara xama nayi na fara bata labarin mutuncin da kanwar dattijona tayi min, kayan da ta bani na shiga fito mata da su tarkacen kayan kwalliya ne da turaruka kala-kala godiya innah ta rika yiwa kanwar dattijo tana sa mata albarka har da dan guntun hawayenta,  Allah mun gode maka  da Alhaji ya shigo rayuwar mu ya hana ki kukan maraici Niimatullah, ki rike mijinki da kyau kiyi masa biyayya, kaina a kasa na amsa mata da insha Allah innah.

A ranar ma sai da muka sha waya da dattijo kusan kwana muka yi muna waya sai faman shagwaba yake min.

Washe gari da safe na tashi na fara gyara gida saboda nasan da wuri xai xo ya dauke ni mu tafi gidan gyaran jiki, soron farko na fara sharewa, wata magana naji a nayi kasa-kasa da farko bana fahimtar abinda ake fada sai da na tsayar da hankalina sosai sannan naji abinda ake fada, wata murya naji na cewa, duba gidan nasu da kyau babu komai daga laka sai axara, talauci ya samu wajen xama a gidan amma sai mugun abu da bin malamai, mu shiga daga ciki mu yaga masu rigar arxiki don idan muka tsaya a nan baxa su fahimci komai ba, gabana ne ya rika faduwa naji ina kokarin xubewa a kasa saboda fargaba, ganin mutanen nayi sun shigo soron da nake, a firgice na matsa gefe, saboda matar dattijona na gani ita da wata kawarta.

muna hada ido ta watsa min wata matsiyaciyar harara tare da cewa, yauwa  Hajiya xainab kinga matsiyaciyar nan, kamo ni matar tayi tana dubana sama da kasa, fari tayi da idonta sannan ta dube ta, hmm lallai dole mijinki ya rude mace har mace ta fara jin sinadari ta fara xama cikakkiyar mace ai dole ya susuce saboda yana jin sabon al'amari a jikinta, sakin baki nayi ina kallon su saboda gaba daya ban fahimci ina maganar tasu ta dosa ba.

matar dattijon ce ta ja hannun kawarta taho mu shiga daga ci mu ci mutuncin tsohuwar banxar da ke yiwa wannan jakara yawon malamai, har sun sa kafar su a tsakar gida ta juyo ta dube ni, ki tabbatar da cewa kina shigowa gidana kin shigo makabarta domin duk abinda kike nema baxa ki samu ba fadar mijina tafi karfinki, bin su nayi a baya don ganin inda xasu je dakin innah suka shiga tarar da ita suka yi tana ta faman bacci  cikin tsawa suka yi mata magana wannan dalilin yasa ta farka a firgice tana salati, cikin dashewar murya take musu magana kasancewar tana dan fama da mura.

Ku kuwa lafiya yayan nan ba sallama?cike da rashin kunya suka fara yiwa innah magana, wajen ki muka xo ki fara warware sharrin da kike kullawa na sai kin fitar da ni daga gidan mijina idan ba haka ba kuma yau a yita ta kare don baxan fita daga gidan nan ba har sai an warware auren banxar jikar ki da mijina, girgixa kai innah tayi
kayya! me yasa xaku haramta abinda Allah ya haramta, Allah ne ya bawa mijinki dama ya auri mace sama da daya, me yasa xaki rika jayayya da hukuncin Allah? hannu tasa ta dakatar da innah, dakata min tsohuwar tsiya ke mijinki mata biyu ya aura ba ke kadai kike rayuwar ki ba gashi nan har kun tsufa a haka, ke da kike gidan talauci ma kika guji kishiya ballantana ni da nake a gidan wadata

ina jin abinda take fadawa innah nayi wani tsalle na dawo gabanta ina huci, cikin tsawa nima na mayar mata da martani

Ba innata ce tsohuwar banxa ba
kece babbar banxa wawiya da kika kasa kula da mijinki har sai da yaxo ya like min ya nace na aure shi, ki dube ni da kyau ni ba mummuna bace ballantana kice lika masa ni aka yi,shi ya ganni ya nace don haka ba mu xaki yiwa hauka ba mijinki xaki je ki yiwa, da yaxo nace
idan har kin cika mace mai ji da kanta mai xai sa mijinki ya gano mitsitsiyar yarinya kamata ya nace mata har ya rika kuka a kan na so shi
mun gaji da cin fuskar da kike mana, an gaya miki talauci hauka ne,wlh baxan juri wannan jahilcin da xaki rika yi mana ba, kuma miji sai an aure shi don ba ni nace kiyi sake har ya rika kallon mata ba.

sakar baki suka yi suna kallona, saboda basu taba xaton xan musu haka ba,ni kaina nayi mamakin maganganun da na rika fada mata, ji nayi na fita daga hankalina duk abinda xai faru sai dai ya faru indai a kan a taba innata ne, kamo ni innah tayi ta xaunar da ni tana min nashiha, ki daina rama abinda aka yi miki na rashin kyautawa saboda bai kamata kare yayi maka haushi ba kaima ka bishi ka rama, a fusace matar ta kamo ni ta shake min wuya wanda sai da na kusan suma saboda shakar da tayi min cikin xafin rai take min magana.

dan ubanki har kin yi girman da xaki fada min magana yaushe aka haife ki, shegiya kaxama kucakar banxa, nasan ba haka kika bar min miji ba shi yasa amma da me xai yi da ke shashasha, kuma wlh daga yau idan baki fita a harkarsa ba xaki ga abinda xai faru da ke sakina tayi na ja da baya kamar xan fadi, wani kallon raini na shiga yi mata.

cike da rashin kunya nake mata magana gara ni kucaka ce amma ke kin fi kuca kucakanci kina cewa kina da ilimi amma bakya aiki da shi banda tsabar jahilci da rashin sanin ya kamata kixo kice xa kiyi fada da ni a matsayina na yar cikin ki dube ki fa duk tsufa yaxo miki ko ta ina, amma baki san Annabi ya faku ba,kuma aure da mijinki yau aka fara baxan rabu da shi ba ko dafa ni xa kiyi ki cinye ni sai na shigo gidan ki, xagin mu ta rika yi tana aibata mu innah ce ta dakatar da ni amma ban yi niyyar kyaleta ba saboda a duniya na tsani abinda xai taba min xuciyar innah haka suka gama xagin mu suka tafi.

gaba daya muka fashe da kuka saboda masifar matar tasha kan mu bata gajiya da bala'i abinda ya fi daga min hankali yadda tace xata yi da ni idan na shigo gidanta kuka sosai muka rika yi, a dai dai lokacin baba ya dawo ya tarar da mu a wannan halin cike da damuwa ya dube mu.

meke faruwa na gan ku haka? inna ce ta fara yi masa bayanin komai ba karamin baci ransa yayi ba, cikin damuwa yake magana ina ganin lokaci yayi da mutumin nan xai sauwakewa Niimatullah cin
kashin da matar nan take mana yayi yawa kada yarinyar nan ta tare ta samu damar cutar da ita,tunda tana ganin ba tada wani gata mu kuma Kullum karfin mu karewa yake baxa mu iya biyewa wannan tashin hankalin ba don haka ko yana so ko baya so sai ya sauwake mata baxa mu iya masifa ba, fita baba yayi, ni kaina yanxu nafi son ya sake ni saboda ina jin baxan iya xama da ita ba.

su Hajiya na fita suka bushe da dariya, ina ganin wannan itace hanya mafi sauki da xa mu yi maganin auren nan saboda wlh idan muka bar yarinyar nan ta shigo xaki xama yar kallo dubeta fa tubarkalla komai ya ji ba tada wata makusa, kuma yadda suka ga xata shiga gidan hutun nan dole su rika karfafa mata gwiwa mu kuma ta hanyar yi musu tijara xamu samu mu karya auren kowa ya huta hirar da suka rika yi kenan har suka isa gida.

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO Completeحيث تعيش القصص. اكتشف الآن