MATAR DATTIJO page 25

1.6K 64 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha sammani Alatu (maman kauthar) ina miki murnar samun baby Allah ya raya shi*

*ya Allah ka bawa diyata Aysha yar London lafiya*

25

Dattijo ne ya turo kofar dakin ya shigo sanye yake da farar shadda wadda tasha aiki da farin xare, takalmin dake kafarsa ma fari ya sanya, hularsa ma fara ce, xan iya cewa duk abinda ya sanya a jikinsa fari ne, sanye yake da farin glass a fuskarsa, hannu shi kuwa dauke yake da ledoji wanda baxan iya bayyana abinda ke cikin su ba. kasancewar ta cikin mayafi nake hango shi.

yana murmushi ya karaso wajena, sallama yayi gami  da ce min amarya kin sha kamshi, ledojin da je hannun shi ya ajiye a kan side drower sanan ya hau kan gadon da nake, kusa dani ya xauna tare da bude lillibin da ke rufe a fuskata, ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi, cikin kulawa yake min magana  my niimatullahi meye na kuka, bayan kina tare da mijinki, godiya xamu yiwa Allah da ya cika mana burin mu na xama ma'aurata,  kiyi hakuri ki daina kuka haka kowace mace take samun kanta,a kawota gidanta har ta girma ta haifi yaya ita ma ta zama uwa, hada ni yayi da jikinsa tare da cire min mayafin dake sanye a jikina rarrashina ya shiga yi gami da shafa kaina tamkar jaririya, cikin salon soyayya yake kallona, wow!! amaryata kin yi kyau sosai, don ma kukan nan da kika
ya bata min kwalliyata dubi fa har idonki ya fara kumbura.

turo baki nayi to ba innah ce taki biyo ni ba, dariya yayi gami da cewa kiyi hakuri, a cikin daren nan zan kai ki har gidan innah amma ki share hawayenki ki daina kuka tukunna.

handkercheif yasa ya fara goge min hawayen da ya cika fuskata, cike da nutsuwa ya sake kallona tashi mu yi alwala mu yi sallah mu godewa Allah a bisa niimar samun juna da yayi mana.
Hannuna ya kama xai mikar da ni tsaye amma na makale naki tashi, cike da shagwaba nake masa magana baxan tashi ba har sai ka min alkawarin xaka mayar da ni wajen innah yanxu, murmushi yayi tare da kwantar da ni a kirjinsa, xan kai ki babyna tashi mu fara gabatar da sallah sai mu yi magana, alwala muka dauro inda muka yi nafila sannan muka yi addu'a muka shafa.
ledar da ya shigo mana da ita ya dakko, inda ya fara fito min da kayan da ke ciki, kayan kwalliya ne da kayan shafe shafe da kuma sleeping drees na haduwa, daya ledar kuma kaxa ce da kuma fresh milk, cikin nutsuwa ya dakko min kaxar  karbi kici babyna nasan kina jin yunwa, gefe nayi da kaina bana ci, dago fuskata yayi me yasa baxa ki ci ba Niimatullah, cikin shagwaba  nace masa ance maganin bacci kuke sakawa a ciki, dariya yayi tare da cewa wannan tunanin ki daina yinsa karya aka fada miki, lallaba ni ya fara yi a kan naci kaxar amma naki, tashi yayi ya shiga kitchen ya dakko cup, fresh milk din ya tsiyaya min a cup karbi ki fara sha kinji babyna kurba nayi na ajiy shi a gefe, matsowa yayi daf dani tare da dafa kaina so nake yi ki shanye gaba daya tunda kin ki cin naman na riga na karbi amanar ki a wajen baba hakkina ne na kula da ke my niimatullah, karba nayi na fara sha, kadan na sha na ture hannun shi, bayan mun gama sha ne ya dauki kayan ya tattara ya kai kitchen.

komawa nayi gefe na jingina kaina jikin pillow wani fargaba da tsoronsa ne ya xiyarci xuciyata, tashi yayi ya shiga bathroom jin shi nayi yana wanka daga bisani ya fito daure da towel, ina kallon shi sau daya na sunkuyar da kaina wani kwarjini ya kara min a idona ban taba xaton haka dattijona yake ba. fita yayi sanyo jallabiya fara sannan ya dawo ya xauna.

cike da kulawa yake min magana Niimatullah tashi kema kije ki watsa ruwa, cikin dasasshiyar muryata na amsa masa da nayi wanka tun a gidan innah,  cike da xaulaya ya dube ni ki tashi kije kiyi ko na kai ki nayi miki kinga yau dai mu biyu ne babu innah ballantana kiyi min tonon silili.

da sauri na tashi saboda yanxu ina tsoron wasan sa yanxu xai mayar da abin gaske, shiga bandakin nayi na fara watsa ruwa sai da na saka kayana complete sannan na fito, kallona yayi yana murmushi da wannan kayan xaki kwanta Niimatullah cike da tsiwa nace mashi dam da wanne xan kwanta, ni da su na saba kwana a gidan mu, jan kumatuna yayi tare da cewa nan ai ba gidan ku bane nan gidanki ne kuma gidan mijinki abinda nake so shi xa a yi, tashi yayi ya jawo ledar da ya shigo da ita, wata fitinanniyar mitsitsiyar riga ya dakko min tare da cewa, da wannan nake so kiyi bacci daga yau na hana ki bacci da atamfa.

cikin shagwaba na mayar masa da amsa ni Allah baxan saka wannan kayan kafiran ba, matsowa yayi ya rungume ni yana sumbatar goshina, shi nake so ki saka min Allah ko kuma yau din nan mu yi yaki ni da ke.

kokarin xame jikina na shiga yi amma na kasa cikin kuka nace masa, ka sake ni xan saka maka,a hankali ya cika ni na koma gefe ina mayar da numfashi,lumshe idanu yayi yana sake kallona, ki saka min kin ji my Niimatullah idan baki saka min ba waye xai saka min? cikin tsiwa nace ga matarka can ita xata saka maka, tasowa yayi ya matso kusa da ni da sauri na matsa tare da kwala ihu xaunawa yayi yana min murmushi ki daina tsorona ni ba abinda xan miki, da yaga dai ba nida niyyar saka kayan ne ya kyale ni komawa kasa nayi na xauna.

takowa yayi har inda nake ya tsaya daga baya yana min magana ya kamata mu kwanta Niimatullah nasan kin gaji nima na gaji sosai tashi kixo ki kwanta, gyara min gado ya shiga yi, tashi ki kwanta kin ji babyna, makale kafada nayi tare da tambayarsa kai a ina xaka kwana.

shafa gashin kansa yayi a kusa da ke mana, kuka na fara yi Allah baxan kwana tare da kai ba, dariya yayi min tare da cewa kiyi kwanciyar ki da wasa nake yi nima dakina xani na kwanta, kashe min fitilar dakin yayi sannan ya fita ban san ina xai je ya kwana ba.

kwantawa nayi na dade ina mutsu-mutsu kafin bacci ya dauke ni saboda tunanin innata,cikin dare naji tashin numfashi a bayana a xabure na juya don ganin wane ne dattijona na gani kwance ya manna bayana da kirjinsa, muna hada ido ya sakar min murmushi tare da juyo da fuskata sake manna ni da kirjinsa yayi tare da kissing dina, cikin kuka nake tambayarsa meye haka dattijona kai da kace xaka yi bacci me yasa ka dawo xaka hana ni nawa baccin? cike da soyayya yace matukar ban hada jikina da naki ba baxan iya bacci ba niimatullah ki taimaki mijinki ki barni naji dumin ki.

kuka na fara yi masa, kokawa muka shiga yi da shi, cikin shagwaba yake min magana

kiyi hakuri my niimatullah na raya mana wannan daren da muka dade muna jiransa baxan iya hakuri da ke a halin yanxu ba ihu na shiga yi ina kiran innah da kyar na kwace na fada bandaki na mayar da kofa na kulle ina mayar da numfashi.

buga kofar bandakin ya fara yi yana rokona na bude na fito har da dan kukan shi amma naki bude masa, nima cikin kukan na ke bashi amsa Allah baxan fito ba tunda haka abinka yake, kuma gobe da safe xan tafi gida duk abinda kayi min sai na fadawa innata kuma baxan sake kwana a gidanka ba,lallabani ya shiga yi ki fito Niimatullah indai kika fito yanxu xan dauke ki na mayar da ke gida na miki alkawari, kin fitowa nayi duk nacin da yayi min haka na kyale shi tsaye yana ta faman bugun kofa.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now