1

5.6K 124 20
                                    

Labarin kudi ne... Ga 'd'and'ano daga ciki! Mai so sai ya biya naira dari biyu kacal ya karanta👏🏻

*_IGIYAR ZATO_..........💕_*

   
    _*NA_*

_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*

_®️ZAFAFA2020_*
    _(TAKU NA BIYU)_

_*SHAFI NA DAYA_*

*ZARIA*

    *2004*

Zaune nake a 'dan tsukukun gefan kofar dakin mu, gaba na kuwa wani tsohon kwano ne dake 'dauke da sandararren tuwon dawa da miyar kuka koriya shar da ita, ina ci ina korawa da ruwan bunu marar sukari, can gefe na kuwa su Alawiyya ne da Hinde sun barbaje suna afka lomar taliya yar mirji data sha manja sun yayyan ka tumatir da albasa a akai. Kuka na na hadiye ina ko'karin 'karasa cin tuwon gaba na don sauri nake yi zan kai wa yayan mu abinci dake can tsallaken gaban gidan mu can yake bakanikan ci. Fitowar babar su Alawiyya ne yasanya ni hanzarin mikewa na dauke kwanon gaba na, Ai kuwa muna hada idanu ta zabga min harara wadda tazame mata jiki kullum sai ta min.

"Mayya! Aniyar ki ta biki. Kurwar mu kur wallahi, anyi gado awajen uwa. Da shegen idanu kamar na ungulu.."

Can na baro Babar su Alawiyya wacce ake kira da Bintalo tana zuba min kwandon zagi. Na danne bacin rai na na dubi Innar mu dake tsintar hatsi a tire nace,

"Innaar mu bari naje na kai wa yaya abincin sa.."

Na karasa magana hade da d'aukar wata fashasshiyar kular abincin mu wadda itace me kyau acikin kwanukan mu da ake zubawa yayanmu abinci. Innar mu tayi murmushi tana gyarawa autar mu kwanciya dake baccin ta hankali kwance, gefan zaninta ta sunce ta ciro naira hamsin wadda itace dama a kullin zanin duk ta kanannade ta mikomin,

"Ungo ki taho da man gyadan ashirin sai yajin goma, ki biya ta gurin ladiyo mai koko ki sayo kokon da kosai na ashirin."

Rissinawa nayi hannu biyu na karb'i kudin, idanuwa na suka kawo ruwa cikin tsantsar tausayi nace,

"Innar mu to ke mezaki ci? Kinbar mana tuwon ni da yaya Najib, koko da kosan kuma na Aminatu ne."

"Banasan sakarci sanda naci abincin idanuwan ki biyu?"

Girgiza kai nayi alamun a'a. Kafin na janyo kodadden koren hijabi na daya zama tamkar na gado na zura shi cike da tausayin innar mu, Uwa kenan gwara muci ita ta zauna da yunwa har sai mun gama sanwar rana. Sallama nayi mata na fito kai na a kasa na wuce ta gaban bintalo ai kuwa ban gama maganar ta a zuci ba ta zubamin rankwashi ji kake .'kwas'.

Su Alawiyya da Hindatu suka tuntsire da dariya suna gasamin magana, share hawaye na nayi, domin inda sabo na saba da irin rayuwar gidan mu. Dakyar na karasa sauka daga benen gidan mu mune a saman karshe mu dasu Bintalo da Usaiba maman su Larai, wato dakuna na uku acikin d'akuna tara dake gidan. Domin kaf layinmu da unguwoyin gaban mu babu wanda bai san gidan mu ba, wanda akewa laqabi da 'Gidan Mata Tara'.

*HAYIN RIGASA MECHANICS*

Ina tafe a hanya ina bitar haddar Suratul Yasin da za'a karba anjima a islamiyyar mu. Sauri nake yi na 'karasa na kai wa yaya abincin sa. Cikin nutsuwa na 'karasa wurin aikin su. Na gaggayshe da abokanan aikin su kafin na wuce wajen daya ke zama. Can 'karkashin wata mota na hango shi yana gyara notinan taya. Yayi dumu dumu da bakin man fetur. Cike da murmushi na 'karasa wajen sa. Cikin nutsuwa da girmamawa na dan durkusar da kaina yadda zai iya jiwo murya ta nace,

"Yayan mu! Sannu da aiki. Ga abincin ka."

"Na'am Batoul! Sannun mu! Ya innar mu da auta?"

"Lapia lou Yayan mu. Bari naje nayo cefane."

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now