2

1.9K 34 1
                                    

*_IGIYAR ZATO_..........💕_*

   
    _*NA_*

_*NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO🧕🏼)_*

_®️ZAFAFA2020_*
    _(TAKU NA BIYU)_

_*SHAFI NA BIYU_*

*ASALIN MU*
(TAK'AITACCEN TARIHIN MU)

*GWANI IDRIS NAJIBULLAH*

Marigayi Gwani Idris Najibullah shine sunan mahaifin baban mu, Tare da matar sa Malama Halimatu Alkali, Ya kasance Malami a garin na kaduna, matar sa wato mahaifiyar su baban mu ita kadai ce mai dakin  sa, ALLAH ya albarkace su da ya'ya shida , Kawu Ishaq, Kawu Dawood, Gwaggo Aminatu, Kawu Khamis, Sai mahaifin mu Salis, Sai Kawu ilyas wanda ake kira da baba ila. Dukkanin yan dakin nasu a Zaria suke gidan mu d'aya, Banda Gwaggo Aminatu wadda ke aure a Kaduna. Gidan da muke ciki a Zaria gida ne na gado, wanda iyayen mu suka hada karfi da k'arfe suka siya. Dakuna tara ne acikin sa, kowanne guda d'aya d'aya ne ba ciki da parlor, Sai dakin baba ila dake 'kasa shine mai ciki da parlor. Dukkanin yan uwan mahaifin mu a gidan suke da zama da matan su. Gidah ne mai hawa biyu, mune a saman karshe dake dakuna uku ne: Muna cikin d'aya, sauran biyun kuma Bintalo da y'ay'an ta na d'aya. Sai Usaiba mahaifiyar su Larai da Talatuwa, Usaiba matar Kawu Ishaq ta farko, sai amaryar sa Rabi'atu ita takansace juya ce bata haihuwa, sannan a dakin k'asa take, Dakuna uku na 'kasan mu kuma, Kawu Dawood ne da matar sa Hafsatu sai yan biyun su Fareed da Fareedah. Sai Kawu Khamis da matar sa Innatuwa da Yayan su maza biyu 'kanana wato Yusha'u da Bala. Sai dakin karshen saman nasu wanda Rabi'atu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu. Sai Kawu ila wanda ke dakunan 'kasan karshe shi da matan sa Ummita da Hajara, dakin farko mai ciki da parlor Ummitan ce aciki wato matar sa tafarko Ita da tawagar yayanta su biyar dake yawan haihuwa take yi ne akub'i akubi. Sai d'aki dayan karshe na amaryar sa Hajara wadda ya aure ta bayan rasuwar mahaifin mu. Takasance tanada tsohon ciki wadda zata iya haife shi a kowanne lokaci saboda ya tsufa.

Marigayi Malam Salis Idris Najibullah shine mahaifin mu, Malama Kaltume Rabiu shine sunan mahaifiyar mu. Mahaifin mu kafin rasuwar sa ya kasance yanada mata biyu, Innar mu Kaltume sai Baba Zara'u wacce ake kira da Bintalo. Mahaifin mu dan asalin cikin garin Kaduna ne, almajiran ta takawo su shida yan uwan sa Zaria. Anan kuma ALLAH yayi zasuyi aure su hayayyafa. Mahaifin mu lokacin da suka fara sana'ar tashi zuwa garin katsina, anan Allah yayo zai gamu da mahaifiyar mu a kauyen Shema. Mahaifiya ta irin fulanin nanne na jaub'awa, Mahaifin mu kuwa bahaushe ne gaba da baya. Domin kakan su ma kafin Allah yayi mai rasuwa ance a garin kano yake. Baba Bintalo y'ar uwar mahaifin mu ce, da kakanta da mahaifin baban mu uwa suka hada uba kuma kowanne da nasa. Auren nasu ma auren had'i ne ko nace auren zumunci ne, mahaifiyar mu kuwa itace matar sa ta ladan noma. Mu bakwai ne awajen mahaifin mu, dakin mu mu uku ne, Yaya Najibulla wanda yaci sunan kakan baban mu ana kiran sa da Najib. Sai ni Fadimu Zahra'u, wadda ake kira na da Batoul. Naci sunan mahaifiyar maman mu wadda ALLAH yayiwa rasuwa tun ina yar 'kankanuwa. Sai autar mu Aminatu. Wadda taci sunan Yayar mahaifin mu dake garin Kaduna. Sai 'ya'yan Bintalo guda hud'u, Yaya Zabba'u wacce ke aure a kauyen kod'e dake lahadin makole a Kano. Sai Alawiyyah da Hindatu wacce muke kira da Hinde, Sai autar su Mariyah.

Nasan mai karatu zai yi mamakin yawan gidan mu da kuma ahalin dake cikin sa, Toh kamar yadda kuka gani a baya, 'Gidan Mata Tara' gida ne mai dakuna guda tara. Sannan gidah ne wanda mahaifin mu da yan uwan sa su hudu suka hadu suka siya tun kafin a haife mu.

Mahaifin mu marigayi Malam Salis ya rasu ne shekaru bakwai da suka wuce lokacin autar mu Aminatu na jaririya, ya rasu ne akan hanyar sa ta zuwa gidah sakamakon hatsarin mota daya rutsa dasu, wata jibgegiyar gingimari ce tabi takan mashin din da yake kai alokacin yayo cefanen sunan kanwar mu Aminatu. Tundaga lokacin rayuwar mu ta canza zuwa halin rashi da kuma 'kunci.

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now