5

1.5K 22 2
                                    

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

*IGIYAR ZATO.....💞*
(Eternal_love)

  *50*

*KADUNA*

Haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya a wannan gida, ina kokarin danne zuciyata wajen jinyar Mubeen da basa dukkan kulawa, hakan nama ahalinsa dadi sosai, Shi yasa suma suke bani dikkan kulawa.

Rashin kunyar Mubeen itace kawai ke batan rai, zuwa yanzu duk yanda zan canjama yaron nan fuska kona d'aure akan karya tab'ani baya jina sai yayi, musamman ma idan zan bashi abinci yafi min duk iya shegen daya gadama. Sai dai ina kokarin dannewa saboda rashin lafiyarsa, ga Doctors dinsa sun shinfidamin dokoki akan yanda zan bashi kulawa kodan dai-daitar komai.

Alhamdullahi yanda nake kokarin bin dokar tasu kuma ana dacewa, dan akwanaki goman nan dana dauka tare dashi jikinsa yayi kyau sosai, zuwa yanzu har dan fita yakanyi harabar gidan yasha iska.

Duk yanda naso sabawa da bakin al'amuransa nakasa hakan, sai dai nasihar Gwaggona tana dakatar da dukkan yunkurina akan komai.

Tunda na tashi a safiyar yau da tunanin maganar komawata makaranta na tashi, dan hutuna ya kare. Abin mamaki sai juya zancen nake a raina da tunanin yanda zan tinkari Mubeen dashi. Cikin kullawa da kwancewa na gama kimtsawa daga shirin da nakeyi, dan wanka na fito, ina cikin fesa turare ya shigo dakin da sallama.

Amsawa nai, sai dai ban juyaba dan ina kallonsa ta cikin mirror. Yanda na hango idanunsa na yawo a jikina duk sai naji na takura, nadan hade fuska dan banason raininsa, sai dai dana tuna kuma maganar komawata majaranta saina dan sake kadan...

Ajiyar zuciya na sauke a hankali jin ya rungumeni ta baya, tunanin dana tafi baisa naji sanda ya iso gareniba, ya dora kansa saman kafadata yana gogamin gashin sajensa a wajen. Take tsigar jikina ta hau tashi, nai kokarin ture hannunsa dake kan cikina amma na kasa hakan.

Ta cikin mirror muka hada ido, nadan hararesa shi kuma yay min murmushi mai cike da ma'anoni da yawa, cikin sanyaya murya yace,

"Tsaurin idonki yayi yawa Fateemah, bantaba ganin matar dake harar mijintaba sai ke".

Shiru nai ina maimaita sunan Fateemah daya kirani dashi, sai naji kamar ba sunanaba, dan tunda nake a duniya zan iya cewa babu wanda ya taba ambatar sunan da hakan..

Sake katsemin tunani yay da cewar,

"Kinason kiji labarina Mah!?".

Samun kaina nai da daga masa kai alamun amsawa. Yay murmushi tare da sumbatar wuyana, sannan yace,

"I love you".

Ban tanka masaba, danshi wannan kalmar ya maidata tamkar me a harshensa, a yini yakan fadamin ita sama da sau goma, duk da ni banajin son nasa amma inajin dadi, sai dai nakan kanne bana nuna masa naji dadin dan karya samu lagona.
      
Hannuna yaja zuwa bakin gadon, ya zauna sannan ya dorani saman cinyarsa. Da sauri na kalle shi inason sauka amma sai ya rikeni da kyau yana girgiza kansa.

"Dan Allah karkice zaki tashi kinji My Fikre".

Ban tankashiba, na dauke kaina ina mamakin solon fitina kala-kala na Mubeen.

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now