4

1.4K 38 1
                                    

*_IGIYAR ZATO_..........💕_*

   
    _*NA_*

_*NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO🧕🏼)_*

_®️ZAFAFA2020_*
    _(TAKU NA BIYU)_

_*SHAFI NA HUDU_*

                         •••

"Ya ishe ki Bintalo, Banason tashin hankali shiya sa bana biyewa ayi dani idan hayaniya ta kaure a tsakani. Saboda haka kada ki 'kara sheganta min yara, 'ya'yana yan halak ne. Allah ya isar mana idan har kika kara aibata su. Banda bina da 'yayana da sharri ba abinda kika iya, Allah ya tsare mu da da miyagun halayen ki..."

Tunda Innar mu tafara magana har ta gama gaba d'aya kowanne acikin yan gidan mu mamaki ne dankare a zukatan mu, idanuwa muka zuba mata ni kam harda 'kyak'kyaftawa ko mafarki nake, domin tunda nake bantaba ganin Innar mu ta maida wa wani martani ba fyace yau. Da alamun an kaita mukura, dadi ne ya mamaye ni ganin tafara samawa kanta 'yanci. Na dubi Bintalo yadda ta daskare a wajen tana kikkifta idanuwa, da alamun  maganganun da Innar mu tayi sun shammace ta. Cikin tunanin dana tafi na sake jiyo Innar mu tana yiwa Yayan mu magana,

"Wannan yaron (Saboda 'dan fari ne) Inaso ka gayawa kowa yadda ku kai da yarinyar nan data bika da sharri."

"Innar mu wallahi kawai ina kwance a cikin net na jiyo ana kiran sunana, Sai kawai na mike tsaye ina kallon gabana ganin mai kiran nawa, Ashe ita ce. Tasa hannu kenan zata bude min net din na mike tsaye gaba d'aya na tattare tabar tawa da net din zan koma langalangar almajirai, Toh a lokacin ma na hango Batoul ta dawo daka kasa da alamun bandaki taje. Bayan shigar Batoul daki ke da wuya kawai naji ta rik'o min hannu, nai nai ta sake ni ta'ki, Nasa d'ayan hannu na kenan zan fincike sai Bintalo tafito daga dakin ta tana kurma ihun gardi, Wallahil azim hakan akayi. Daman tasha tara ta a koina ne tana gayamin kalaman so. Gata nan a tsaye idan 'karya nai mata."

Bintalo tayi kukan kura tana girgiza jiki agaban kowa,

"Sittin ta Ubangiji karya kake yi, Sau nawa kake lalata 'ya.."

"Karya kike yi Bintalo, wallahi tallahi wannan yaron baya kula wata ya mace ma ballanta na har yakai ga lalata. Allah ya isa wallahi. Kin kai ni karshe Bintalo.."

Innar mu ta karasa fada tana sharce hawayen bakin ciki. Kawu ila dake jingine da kafar bene ya ja tsaki yana komawa dakin sa. Kawu Dawood ne yai kokarin cewar,

"Toh ita yarinyar tafada da bakin ta abunda ya faru. Sai musan hukuncin da zamu dauka ko kuwa?"

Su Kawu Khamis suka daga kai alamun 'Eh hakan yayi'. Kawu Dawood ya sake maida kansa ga Islaha da kanta ke a 'kasa tana lankwasa yan yatsun ta yace,

"Ke gaya mana gaskiyar lamari, shin abunda yace shine gaskiya ko kuwa karyane shi ya kira ki?"

Bintalo tasa kafa ta take ta Islaha alamun tace Eh shine ya kirata. A hankali Islaha ta goge hawayen dake kwarara a idanun ta, cikin rawar baki tace,

"Eh Kawu! Hak'ik'a Yaya Najib shine ya kira ni, Tun ba yau ba yakeson yai la.l..lalata da ni."

Bintalo ta saki wata uwar guda, kai kace amarya aka kawo. Cikin buga zanin ta hade da tafa hannuwa tace,

"Alhamdulillah yanzu naji zance. Daman na gaya muku shine ya neme ta."

Yayan mu ya saki wani marayan kuka mai kuna zucia, wanda kowa ya saurara sai ya tausaya masa. Cike da rawar baki ya tsugunna a gaban Islaha yana duban idanun ta, Wadda tai saurin kauda kai gefe.

"Is..Isl.Islaha ki dubi girman Allah ki sanar da su gaskiyar lamari, zamu mutu zamu koma ga Allah. Allah yana kallon ki, shin ni na kira ki ko kuwa kece kika neme ni?"

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)Where stories live. Discover now