3

1.6K 35 0
                                    

'''~_**_IGIYAR ZATO_..........💕_*
*_~'''
   
    _*NA_*

_*NANA HAFSAT_*
   _*(MISS XOXO🧕🏼)_*

_®️ZAFAFA2020_*
    _(TAKU NA BIYU)_

_*SHAFI NA UKU_*

                        •••

"Zo nan dan uban ki."

Wani abu ya tokare min a wuya na, na rasa mai yasa ala dole sai sun zagi Abban mu aduk lokacin da zasu mana fad'a. Jiki ba 'karfi na 'karasa kusa dashi na tsugunna tamkar mai neman gafara.

"Gani Kawu."

Da alama bai masan meyasa ya kira ni ba, domin sai cixan lebe yake alamun tunani. Babu abinda nayi masa wallahi, Kawai dai neman yadda zai dake ni yake yi ko tozarta Innar mu.

"Ruwan tuk'a tuk'a zaki ebo mani, kwarankwatsa idan kika da'de baki kawo ba sai na lahira yafi ki jin dadi."

N kara kasa da kai na ina kukan zuci, duk ga yara nan ciki harda almajiran gidan amman babu wanda zai ebo masa ruwan sai ni? Ga yunwa dake addabar ciki na sai kukan agaji yake. Rankwashi ya sakar min a kai na nai saurin dafe wajen,

"Toh Kawo a me zan ebo maka?"

"Tambaya ta kike? Lalle figegiyar mahaifiyar ku ta kara lalata ku."

Mik'ewa yayi daga kan bokitin da yake zaune ya shiga zundumawa Innar mu kira ba 'kakkautawa,

"Ke Kaltume, Kaltume, kina ina ne? Zaki fito ko sai na raunata shegiyar yar nan taki?"

Innar mu dake sallar nafila tai hanzarin sallamewa, cikin sauri tafi to tana dafe kirji,

"Kawun su, ya akai? Lefi ta maka? Dan Allah kayi mata hak'uri."

A dai dai lokacin Usaiba tai kukan kura ta cakumi Bintalo tana yage dankwalin kanta,

"Shegiya mai kan 'kwakwido."

Cewar Usaiba ta fadawa Bintalo tana tsurtar da yawu a gefan Bintalo, Bintalo ta kece da daria tana nuna Usaiba da hannu,

"Shegiya wada, tamkar a kife ki da kwando, da ido aciki munafuka."

Baba ila yaja tsaki yana nuna su da hannu, ku fitar min a hanya, ko nai sanadin barin mutum anan gidan. Innar mu dake saukowa daga bene tafara girgiza kanta tana mai cewa da baba ila,

"Kayi musu hak'uri sharrin shed'an ne."

Kawu ila ya kece da daria, hade da tafa hannaye kamar mace, Cikin kasakantaccem kallo ya dubi Innar mu,

"Toh munafuka algunguma, Sa'idinawa ana ruwa kuna irgawa masu bacci da ido d'aya."

Innar mu tayi shiru kanta a 'kasa, Bintalo ta buga zanin ta tana sakin gud'a,

"Kuji min annamimiya, Ke har kina da bakin magana? Dangin mayu uwar shegiya, acike nake da ke wallahi kika kuskura wata kalma tafito daga bakin ki sai na daka shegiyar yar ki."

Innar mu tayi shiru kanta a 'kasa, na goge hawayen da ya fara tsere a fuskar ta. Wai shin yaushe zamu dandani farin ciki ne? Wannan wacce irin musibace ace yan uwan mahaifin ka na jini su dinga kyamatar ka suna la'antar ka.

"Ya ALLAH ka nuna min ranar da zan mai dawa su Kawu ila martani, domin nagaji da rashin 'kauna da tozarcin da suke mana shekara da shekaru. Ameen ya hayyu ya qayyum."

Na fa'da a zuciata ina mikewa tsaye.

Bokitin da ya mike akan sa na duaka na fice cikin sauri, Usaiba dake gefe ta ja tsaki tai hayewar ta sama tana mai jifan su da munanan kalamai. Har naje tuk'a tuk'a na dawo ina jiyo muryar kawu ila yana zuba magana da alama da Innar mu yake domin ina jiyo ta tana bashi hak'uri, a soro na tsaya ina mai baje kunnuwana don jiyo zancen su,

IGIYAR ZATO....💕 || PAID NOVEL (COMPLETED✅)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz