part 2

1.1K 79 0
                                    

21/06/2018
🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Labarin wata mata*

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *2*


*Bismillahir Rahmanir Rahim*



Zaune suke a babban Falo, wanda yake da manya manyan kujeru maroon kala. Sai ruwan madarar labulaye da kafet dake dakin.

Abba da Kannen sa biyu, sai Ahmad dake gefen su zaune a kasa.

Kanin shi, Basiru, ya ce
"Alhaji daman munzo mu taya ka murna da farin ciki game da irin namijin kokari da kayi akan danka Ahmad ya gama karatu ya dawo kasar mu."

Kai Abba ya jinjina, Basiru ya cigaba da magana.
"Ka cika jarumi,"

Abba ya ce,
"To nagode Allah saka da alheri."

iIliya, ya ce,
"Dole a jinjina masa, saboda irin tarbiyyar da ya bawa Ahmad  sai dai muyi fatan Allah sanya Alheri."

Abba, ya amsa da
"Ameen Ameen!"

Dai dai lokacin Mama ta zo kawo musu ruwa. Gaisawa tayi sannan ta mike ta bar wajen.

Labewa tayi, dan taji musuke cewa
Baba Basiru, ya kalli Ahmad ya ce,
"Ahmad muna maka murna da kammala karatun ka. Da dawowar ka kasar nan. Sannan kuma babban abin farin ciki da nayi da baka auro baturiya ka taho mana da ita a matsayin matar ka ba."

Dariya sukayi gaba dayan su.
Abba ya ce,
"Ahmad ai daban yake, domin irin tatbiyyaar da nai masa bazai taba auro baturiya wacce ba al'adar mu daya da ita ba, addinin mu da kuma dabi'un mu."

Baba Basir ya ce,
"Gaskiya ne, saboda mu a zuri'ar mu, har yanzu ba mu samu wanda ya fandare daga al'ada da dabi'u mu da iyayen mu suka dasa akai ba."

Baba Iliyasu, ya ce,
"Wallahi kuwa mun gode Allah."

Baba Basiru, ya kalle Abba ya ce,
"To Alhaji mu zamu koma, mungode da irin tarbar da akai mana."

Ahmad ne ya mike, ya ce,
"Ah kafin nan bari na kawo muku tarabar ku ta turai."

Ya fada yana murmushi, yayi cikin gidan
Baba Basiru, ya ce,
"Toh mungode fa. Allah yayi Albarka.."

Mama na jin ya tashi ta shige ciki da sauri dan kar Ahmad ya ganta.

Dakin sa ya shiga wanda dakin ma kan saabin kallo ne. Ba abinda babu a ciki.

Envelope ya dauko, sannan ya dauko jakar da ya dawo da ita yana lissafo kudin can.

Har zai xuba, Mama ta shigo dakin.

Kallon sa ta tsaya yi,  ta ce,
"Ahmad baka da hankali."

Dagowa yayi da sauri dan yaga abinda yayi,
"Menene?"

"Wannan kudin duk su zaka bawa."
Kai ya gyada mata. Ya ce,
"Wai dala dari biyar biyar ne nake son na basu."

Dukawa tayi ta kwashe envelope din tana fadin,
"To bani nan wajen sunyi yawa. Dala dari biyar din wa.  Dalah!"

Ta kwashe su dukka ta mika masa, tana fadin.
"sunyi yawa, ka dibi na Nigeria ka ba sa musu a ciki "

Ta mika masa envelope din. Kallon ta yayi,  ya ce,
"Kudin Nigeria kuma. Ni ban dasu."

"To bari kaga."
Ta fada tana kunto gefen zanin ta.

Wasu tsofaffin naira dari dari ne, guda biyu ta fito dasu daga zanin nata.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now