part 13

625 37 1
                                    

30/06/2018
🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*



Page *13*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*



Amina kuwa tin lokacin da tai ta kiran wayar Ahmad bata samu ba ta akashe ta ta ajiye.

Mama tayi tayi da ita suje asibiti amman taki.

Auwal ne da yazo duba su yaga halin da take ciki ya kira Dectorn da yake duba ta.

Ko da yazo ya dubata yagane damuwa ce a ranta.

Nan ya dinga kwantar mata da hankali duk da besan damuwar ta ba.

Wani magani ya bata wanda zata samu bacci dan sam bata iya bacci.

Yana komawa ya kira Ahmad ya fada masa komai.

Sosai hankalin Ahmad ya kuma tashi.

Haka ya dinga trying number ta amman a kashe.

Sai washe gari da ta tashi ta dan ji dama dama.

Wanka tayi ta taya Mama da wasu abubuwan.

Daki ta koma ta dauki wayar ta ta ga ashe a kashe take.

Kunnawa tayi ta zauna ta zuba tagumi ta rasa tunanin me take.

Can sai ga kiran Wayar ta nan. Firgita tayi dan bata cikin tunanin ta.

Daukar wayar tayi taga Yaa Ahmad akan ne. Da sauri ta dauka, ta kara a kunnen ta.

"Yaa Ahmad!"
Ta fada tana fashewa da kuka.

Rasa abinda zaiyi yayi, yai shiru kafin ya fara magana cikin sanyi muryar, muryar sa na rawa ya ce,
"Yi hakuri Meenal. Kiyi hakuri..."

Jin muryar sa ba dai dai ba yasa tai saurin katse shi ta ce,
"Yaa Ahmad lafiya kuwa."

Ajiyar Zuciya ya sauke ya ce,
"Yanzu dai ya kike? Jikina ya dade da bani baki da lafiya me yake damun ki."

Kuka ta saka ta ce,
"Nima ban sani ba. Ban san me yake damuna ba. Nasan dai rashin ka na daya daga cikin abinda ke damuna na. Ka manta dani na tsawon kwana ki."

"Ba haka bane!"
Ya fada a sanyaye dan ya kasa ma maganar.

"To menene?"
ta tambaye shi.

Nan ya bata labarin duk abinda ya faru. shiru tayi ta kasa magana ma.

Daga na ta kashe wayar tana tunanin wai kenan son Yaa Ahmad take.

Tab amman kuma ta yaya ta fara son sa.

Ta jima a kwance kafin ta kira number Yasmeen.

Yasmeen dake bacci ta dau wayar cikin sanyin jiki.

Ganin Amina yasa tai saurin daukar wayar tana cewa,
"Meenal ya dai ko jikin ne?"

Murmushi me sauti Meenal tayi ta ce,
"Aah jiki ai ya warware gobe ma zan shigo ckul."

"To shikenan Allah kara sauki."
"Ameen!"

Yasmeen ta ce,
"To menene? Naga kin kasa magana."

"Haka ne. Gobe dai ma hadu."
Ta bata amsa tare da cewa,
"Sai da safe."

Tana dire wayar kiran Ahmad ya sake shigowa.

Tana gani ta kasa dauka dan wani nauyin sa take ji.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now