part 29

570 31 0
                                    

16/08/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *29*

*Godiya gare ku masoya na. Allah ya bar kauna*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*



Washe gari Yaa Ahmad tin karfe Bakwai ya fita dan basu gama da bakin Dady ba.

Gidan ya rage daga ita sai Ibrahim da Mami.

Kitchen ta shiga ta hada break sannan ta koma dan taso Ibrahim ya kawo wa Mami abinci.

Mami ta gani zaune a falo ta hakimce. Amina na jin tsoro haka ta karasa gefen Mami ta Durkusa.

"Ina kwana?"
Amina ta fada.

Mami ta ce,
"Da ban kwana ba zaki gannin ki kawon abinci kin tsaya sai kace naki ne."

Mikewa Amina tayi a hankali ta tafi kitchen ta kawo mata ta ajiye.

Dakin ta ta shige tai wanka ta saka bakar doguwar riga ta haye gado.

Ibrahim ne ya fito cikin shirin makaranta ya saka bakin wando da farar riga.

Durkusawa yayi ya ce,
"Mami ina kwana?"

"Lafiya lou."
ta amsa tana ya mutsa fuska.

"Mami zan tafi makaranta ne?"

Mami ta ce,
"Uhmm kai saboda sakarci da rashin hankali ka zo ka zauna a cikin gidan nan wannan yarinyar da take shahsasha ballagaza ta zauna sai saka aika ce aikace take. Kuma fa ka girme ta fa."

"Haba Mama ke dai ba'a raba ki da abin fada. Ni dai bari naje sai na dawo. Kina hakuri damu da duniyar ma gaba daya."

Ya mike.
Ta ce,
"Allah kiyaye Allah bada sa'a a dawo lafiya."

"Ameen!"
Ya amsa ya fice.

Baki ta rike a ranta ta ce,
"Wallahi bazan taba barin Ahmad da Amina ba. Ai ba kalar sa bace yafi karfin ta 'yar matsiya ta. Tab Sai na raba ku wallahi. Yarinya duk ta asirce min ya'ya da miji da yan uwa. To wallahi ni na fi karfin ki. Ta Allah ba taki ba."

Ta daura kafa daya kan daya tana jijigawa.

"Amina Amina!!"
Ta kwada mata kira.

Da sauri Amina ta karaso tana amsawa da
"Na'am!"

Mami ta ce,
"Naci amman ban koshi ba. Kije ki min sakwara miyar agushi ki kawon yanzun nan."

Kai ta sunkuyar ta ce,
"To Hajiya!"

Ta nufi kitchen. Doya ta feraye ta daura aaka wuta ta dibi kayan miya ta gyara ta blanding sannan ta gyara nama ta daura miyar.

Nan da nan tayi ta gama abinka da gas ga kayan amfanin zamani da akayi

A fulas ta kawo mata shi. Kallon ta ta yi ta ce,
"Allah yasa baki barbada min wani abu a ciki ba."

Shiru Amina tayi ta bar wajen. Daki ta koma ta dauro alwala ta hau kan sallaya tana rokan Allah ya yaye wa uwar mijin ta wannan tsanar da tai mata.

Ta jima tana kai kukan ta gun Allah kafin ta tashi ta koma kan gado.

Yasmeen ce tai mata waya suka sha hira wannan ne ya rage mata wata damuwar a ranta.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now