part 24

577 34 0
                                    

14/07/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *24*


*Bismillahir Rahamanir Rahim*



"Allah sarki. Yaya dazu Na'ima ta kira tana min ya jiki? Wai me yake damuna ne?"

Murmushi yayi ya ce,
"Eh ban fada miki bafa ko Na'ima ai tana gida."

Ido ta zaro ta ce,
"Lafiya dai ko?"

"Ina fa lafiya. Wai Kanwar mijin ce da Maman sa suka mata sharri."

"Allah sarki kuma shine yace ta taho gida."
"Eh kinsan ba kowa ke zama yai tunani ba."

"Allah ya dai dai ta toh."
"Ameen!"

"Yaya baka fadan me yake damuna ba."
"Tashi muje muyi break tukkunna."
Mikewa tayi suka nufi daining sai da suka gama taga ya tashi ya fita.

Can bakin titi yaje neman garwashi sanna ya dawo. Tana dakin ta dan haka can ya nufa.

Turaren da mallam.ya bashi ya saka sannan ya dauko man ya murza a hannun sa ya shafa mata a jikin ta.

Kallon sa ta tsaya yi duk da kamshin abubuwan ba dadi to amman takasa fada masa bare ta tambaye shi.

Sai da ya gama ya dauke kaskon ya dawo sannan ta ce,
"Yaya wannan kuma na mene?"

Murmushi yayi ya zauna agefen ta ya bata labarin duk abinda ya faru.

Kuka ta fashe dashi ta fada jikin Ahmad. Lallai Ahmad me son tane da wani ne da gidan su zai maida ita ai mata magani.

Amman jibi yadda Dady da Ahmad suka tsaya akan ta wanda ko mahaifiyar ta ma bata sani ba.

"Menene na kukan kuma?"
Ahmad ya tambaye ta.

"Dole nayi kuka Yaa Ahmad da Allah bai bani kai ba da ba kowa ne zai dauki lalura ta ba. Maza nawa ne daga matan su sun fara rashin lafiya suke kai su gida amman jibi ni ku kuka tsaya a kai na har na samu sauki. Yaa Ahmad bansan da me zan saka maka kai da Dady ba. Lallai kai da Dady kun zame min uwa da uba ban da bakin godiya a gareku sai dai Allah yai muku fiye da abinda kukai min."

Ta kuma fashewa da kuka. Dagota yayi yana goge mata ido yana mata murmushi wanda ke kara kwantar mata da hankali.

Ita murmushi tayi duk da hawaye na zubowa a idon ta.

Dariya yayi ya cee,
"Ina da albishir gareki amman ki daina wannan kukan na fada miki."

Murmushi tayi ta goge idon ta. Ta ce,
"Ina ji?"

Ya ce,
"To albishirin ki."

Murmushi tayi ta ce,
"Goro!"

Ido yayi waje dasu yace,
"Tab kaji wayoo. Ni Allah vana son goro."

Dariya tayi ta ce,
"To ka zabi abinda kake so."

"Yan biyu nake son ki haifar min."
Ido tayi waje da su ta ce,
"Ta yaya zan samo maka yan biyu."

Dariya yayi ya ce,
"Kawo kunnen ki kiji."

Matsawa tai yai mata rada. Da sauri ta mike zata bar wajen.

Kamo ta yayi ya ce,
"Ina kuma zaki bayan ban fada miki abinda zan fada mikin ba."

Fuskar ta a rufe da tafin hannu ta ce,
"Wallahi na gode ni kam bari na je na daura girki."

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt