part 8

642 42 0
                                    

25/06/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Labarin wata mata*

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐
🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *8*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Yanzu fa sai kunyi hakuri. Ba lokaci saboda makaranta.*
*Nagode*

Yau tinda  Amina ta dawo daga isilamiyya da yamma ta dawo da zazzabi wanda har washe gari da shi ta farka.

Wanda hakan ya hana ta zuwa makaranta.

Tana kwance a daki rufe cikin bargo bayan Mama tabata panedol ta sha.

Mama na waje tana gyaran gidan bayan ta share gidan.

Kayan Wanke wanke ta hada, ta dauko ruwa zata wanke.

Dai dai shigowar Ahmad sanye yake da bakin wando da hakar riga sai tabarau dake idon sa.

Kafar sa sanye da sau ciki da safa hannun sa daure da agogon azurfa. Tsintsiyar hannun sa gashi kwance kasancewar rigar me gajeren hannu ce. Farar fatar sa ta fito tai kyau da sheki.

Mama na ganin sa ta mike tana masa murmushi, ta ce,
"A'ah Ahmadu kai ne!"

Murmushi yayi ya durkusa, ya ce,
"Ina kwana Mama?"

"Lafiya lou!"
Ta amsa masa.

Tana tambayar sa ya gida dasu Maman sa da Alhaji.

Duk suna lafiya ya bata amsa da. Wajen kayan wanke wanken ya karasa yana cewa,
"Mama wanke wanken za ayi ne?"

"Eh Ahmad dan Allah ka bari kar ka bata jikin ka."

"Haba dai Mama mene dan na bata jiki na."
Ya zauna yana wanke mata kayan wanke wanken yana yi suna hira abinsu.

Sai da ya gama tsab sannan ya koma kan tabarma ya zauna kusa da Mama.

Kallon Mama yayi ya ce
"Mama yau ba dumame ne?"

Murmushi Mama tayi, ta ce,
"Bari na dauko maka a daki na ajiye maka. Na manta kuma."

Ta mike ta kawo masa. Ya zauna yana ci sai da ya gama ya kora da ruwan sanyi.

Hira suke tabawa yana bata labarin karatun da zai tafi. Mama tai shiru dan ba karamin kewar sa ta tabbata zatayi ba.

Suna zaune Amina ta fito da sauri daga daki bakin rariyar gidan ta matsa tana kwara mai.

Da sauri Ahmad ya mike yayi gun ta yana mata sannu tana gamawa ya mika mata ruwa a buta ta wanke wajen.

A hanakali ta mike tayo kan tambarma ba tare da ta lura da wanda ya bata ruwan ba.

Jikin Mama taje ta kwanta, jikin ta zafi radau. Wajen ya wanke sannan ya koma kan tabarmar.

A gefen su ya zauna ya kalli Mama ya ce,
"Mama bata da lafiya ne?"

Kai Mama ta daga masa ta ce,
"Wallahi tin jiya da ya dawo daga makaranta."

"Kuma ba kuje asibiti ba?"
Ya tambaya.

Mama ta ce
"Ai tasha penedol.zazzabi ke damun ta."

Jikin ta ya taba yaji zafi radau kamar wuta. Ido ya zaro ya janye hannun sa da sauri.

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Where stories live. Discover now