part 10

696 42 1
                                    

27/06/2018

🌵🌵🌵🌵
*Koma kan mashekiya*
*(kaikayi)*
🌵🌵🌵🌵

*Back to sender*

*Labarin wata mata*

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*
*MANS*



Page *10*

*Bismillahir Rahamir Rahim.*

*Gaisiwa ta gare ki Anty Rashida A kardam.*
*Ubangiji Allah ya saka miki da gidan Aljanna. Allah kara daukaka da zakin hannu.*

*Mahaifan ki Allah ubangiji ya kara musu lafiya da nisan kwana. Allah ya barki da masoyan ki na gaskiya.*

*Allah kawo miji na gari musha biki.*


To yanzu ma da taji bayanin Ahmad nason fasa tafiya tai tsalle ta Dire kan dole sai ya tafi.

Ahmad da yake yaro me hankali da bin maganar iyaye, wannan yasa ya dauki kaddarar Allah ya fara shirin tafiya.

Lokacin da Amina taji labarin tafiyar ba karamin tashin hankali ta shiga ba.

Ta damu matuka kamar yadda Ahmad ma ya damu duk suna halakan ta haka da sabo da junan da sukai.

Lokacin da tafiyar sa ta tashi kuwa kuka ta dinga yi.

Ahmad da Mama ne ke lallashin ta. Dan shima karfin hali kawai yake yi.

Amina kuwa, kuka sosai duk ta tada hankalin ta.

A haka Ahmad ya tafi ya bar Mama da Amina cikin wani hali.

Duk da ya damka amanar Su a wajen Dady.

Ahmad ya je lafiya inda ya bar wa su Mama wayar da zasu na gaisawa.

Wannan shi ya dan ragewa Amina kadaicin da take ciki.

Dady be bar komai daga kulawar da Ahmad yake musu ba.

Har dadi yake musu duk da bashi yake kai musu ba sai dai ya aika.

Shakuwar su Amina da Ahmad kuwa ta kara yawa.

Inda kullum sai sun sha waya kamar ba gobe. Da safe da rana da yamma duk suna makale da juna.

Ko tana makaranta Allah, Allah take ta dawo su hadu.

Haka nan duk lokacin da Amina ta samu lokaci sai taje gaida Dady.

Dady na matukar jin dadi banda Mami da take jin haushin ta dan tin da taga tana shige musu take tunanin akwai wani abu tsakanin su da Ahmad.

Duk da daga Ahmad har Dady ba wanda  ya fada mata wani abu. Amman ita tasan tabbas akwai wani abu aboye.

Duk lokacin da Amina taje gidan in Dady baya nan sai Mami ta bata mata rai. Hakan be taba sa tasa abin a ranta ba.

Duk saboda abinda Dady da Ya Ahmad sukai mata yafi karfin ta wulakanta ta. Wannan yasa take ganin girman Mami ita ma.

Na'ima kanwar Ahmad ma duk abinda taga Mami nayi shi take dauka tayi. Duk da shekarun su kusan daya ne.

Yau tin asuba ta tashi da wani irin ciwon ciki wanda bata taba yin kamar sa ba.

Mama ta firgita da ciwon cikin da take. Dan ita Amina ta ce cikin tane ke ciwo.

Suna zaune bayan mama ta bata kanwa Amina na kwance tana ta juyi Ahmad ya kira a waya.

Bayan Mama ta gaisa da Ahmad ne, yake tambayar ta Amina.

Kallon Amina ta yi kafin ta ce,
"Gata nan ba lafiya."

Koma kan mashekiyya (Back to sender) 2018 (Complete ✔)Onde histórias criam vida. Descubra agora