7

5.8K 431 55
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

_Follow me on Instagram:- hauwa_a_usman_jiddarh_

7⃣

A kid'ime President ya mik'e tsaye had'i da zubawa Neesah ido,
batare daya iya furta ko da kalma d'aya ba,
cikin rashin fahimta Nana tace " what....!?

"Ban gane ba wai kina nufin aurenshi zaki yi....!?

" Yes Nana....!, ko da wata matsalar ne....!?

Muryar President a d'age yace " halan kin manta nan da next 10 days d'aurin aure ki ko....!?

Baki Neesah ta turo tana k'ok'arin yin kuka tace " I know! but I love him Dad...!,
a fusace President yace " baki da hankali Neesah, so kike ki mayar dani mutumin banza....!?

"Kin san harkar siyasa yanzu hakan yana iya jawo matsala,
ko ya haifarwa da jam'iyya matsala da fitina, tun farko inda kin san baki sanshi da baki bari an saka biki har ya zo gab da gab ba,
sai da aka gama buga kati aka raba invitation card sannan kice baki sanshi....!?

Kuka Neesah ta kuma sakawa had'i da diddira k'afa tace " wallahi ni dai Neehal nake so,
kuma shi zan aura babu wanda ya isa yayi min auren dole,
tana gama fad'ar haka ta shige bedroom d'inta had'i da banko k'ofa,
President zayyi magana Neesah ta fito tace " karka manta da batun kawo min mahifinta da ita kanta,
sannan ina san ganin Neehal dan zanyi singing a contract d'in nan,
dan haka ina san ganin su gaba d'aya gobe, sannan ka kira siriki na Alhaji Bilal Lagosa ka bashi hak'uri,
kace mishi karya damu babu komai,
President zayyi magana Neesah tace " no...! Dad just call him now,
tayi maganar da k'arfi tamkar tana magana da yaronta kamar yadda yaran turawa keyi,
bisa mamaki na sai naga President ya zaro wayarshi cikin Aljihu yayi dialing number Alhaji Bilal Lagosa,
instead of yayi mata fad'a koya nuna mata batayi dai-dai ba,
wayar Alhaji Bilal Lagosa ta soma ringing dai-dai lokacin yana tsaye gaban Neehal da Nauman yana zazzaga musu ruwan bala'i,
kasancewar shi mai matuk'ar zafi da fad'a dan baya wasa,
kamar bazai d'aga wayar ba, sai kuma yakai duba ga wayar dake aje gefe,
ganin sunan President yasa shi saurin mik'a hannu ya d'auka tare dayin picking ya kara a kunnenshi,
Neesah na tsaye a gefen President ta tsura mishi ido hannunta sark'e gaban k'irjinta,
bayan sun gama gaisawa ne President yace " I'm very sorry da maganar dana fad'a maka d'azu,
Neesah ta sanar dani ba laifinshi bane, so dan Allah karka d'aga hankalinka komai yana nan kamar yadda yake,
sannan gobe zan saka hannu a kwangilar, sai kazo ka amsa,
da sauri Neesah tace " no...! bashi ba ya turo Neehal d'in dai, I want see him,
idan kaga yadda Neesah ke bawa President oder yana bi saika rantse ita ce ta haife ba shi ya haife taba,
saboda tsakanin k'aunar da yake yi mata yasa yake yi mata biyayya wacce ita ce ya kamata tayi mishi,
da sauri Alhaji Bilal Lagosa yace " Alhamdulillah nagode sosai mai girma President,
goben in sha Allah zanzo da kai na,
" no...! ka aiko Neehal d'in gida sayya karb'a a hannun Neesah,
tunda su suka fara sai a barsu su k'ara abinsu gwara ma su fara koya tun yanzu tunda ba'asan me Allah zayyi gaba ba,
" haka me kam, Alhaji Bilal Lagosa ya fad'a yana murmushi irin na manya.

Bayan su Alhaji Bilal Lagosa sunyi sallama,
Neesah ta kalli President tace " call her useless father,
ba musu President yayi dialing number Alhaji Ubayyu,
bugu d'aya shima yayi picking cike da girmamawa ya gaida President,
ba wani dogon bayani President yace " gobe kazo villa house kai da 'yarka,
sai da ya d'an suruna tamkar yana gaban President yace " wacce daga cikin yaran nawa...!?

A dak'ile President yace " surukar Alhaji Bilal Lagosa, ya fad'a had'i da dropping wayar,
cike da tsantsar farin ciki Neesah ta rungume President had'i dayi mishi kiss,
tace " thank you...! thank you so much Dad, yana murmushi ya shafa kanta yace " kinyi farin ciki yanzu....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now