29

6.5K 429 115
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_  

2️⃣9️⃣

A razane Naufal ya sanya hannunshi biyu ya tallafe fuskarta had'i da kiran sunanta,
cak Nauman ya d'auketa ya fita daga hall d'in yana cewa " ruwa!  ku bani ruwa jama'a ta suma,
jikin Daddy na rawa ya bud'e fridge ya d'auko robar ruwa ya b'alle ya zuba mata,
a fili ta sauke ajiyar zuciya had'i da fashewa da rikitaccen kuka batare data bud'e idonta ba,
jikin Mamy a sanyaye suka kalli juna ita da Daddy dan koda Neelah bata furta ba Mamy da Daddy sun fahimci komai,
Neehal na tsaye hannunshi sak'ale cikin na Najwah ya dake yadda kasan bai san abinda ke faruwa ba,
duk da kallo d'aya yayiwa Neelah ya gane ta, dan ko a gigin mutuwa ya ganta sayya gane ta,
deep down a matuk'ar tsorace yake, da mamakin daya cika mishi rai,  yana yiwa kanshi tambayoyi da dama,
" shin Neelah ce Pari d'in Nauman?

"Tayaya akayi ta shigo birni ta waye haka?

" Ya akayi ta zama Doctor dan Nauman yasha fad'a mishi likita ce,  tayaya duk hakan ta kasance?

Yayiwa kanshi tambayar yana gyara tsaiwarshi,  kallan Neelah dake kwance yayi yana mamakin kyau da had'uwarta,
" yanzu wannan poor villager girl d'in ce ta zama tamkar hurul'in?

"Lalle kyau na k'auye sai dai rashin gyara da wayewa, ya fad'a cikin ranshi,
  skin d'inta dake ta shek'i ya kalla ya tuna lokacin datake k'auye,  ya kalli gashin kanta zuwa fuskarta,
mahaukaciyar fad'uwa gabanshi yayi ya tuna lokacin da yake amfani da ita,  yadda take kuka yanzu sak a lokacin,
take komai ya dawo mishi ya rink'a ganin kamar a lokacin komai ke faruwa,
tsoro da fargabar da yake ciki suka tsananta, hankalinshi yayi masifar tashi, zuciyarshi ta shiga bugawa fat fat,
k'irjinshi ya soma yin sama da k'asa da tsananin sauri,  idan aka yanka jikin Neehal a lokacin baza'a samu jini ba,
saboda tsagwaran masifar dayake ciki,  amma dayake namijin duniya ne,  baka isa ka gane halin dayake ciki ba,
dan binta yake da kallo tamkar yau ya fara ganinta,  " wai meke faruwa ne?

Najwah ta fad'a tana kallan Neelah,  bakinshi ya tab'e had'i da d'age gira d'aya yace " oho!  ina zan sani,
" ka cuce ni!  ka zalunce ni!,  ashe dama kana raye amma baka tab'a waiwaya ta ba?

Tayi maganar cikin matsanancin kuka,  cikin rashin fahimta Nauman da Naufal da Umairah suka kalli juna,
muryar Naufal na rawa yace " meke faruwa ne Neelah?

" Wannan shine MIJI NA,  shine wanda Abpa na ya baku labari shine wanda aka AURA MIN 11yrs back,
tayi maganar tana nuna Neehal,  " what?

Nauman da Naufal suka fad'a a tare suna mik'ewa tsaye,  ido Najwah da Neehal suka had'a, bakin Najwah bud'e tace " me?

"Ke kina hauka ne?

"Kin san me kike fad'awa kuwa...?

Tayi maganar cike da izza,  Umairah kam kasa furta kasa koda kalma d'aya tayi,
Daddy da Mamy suka zubawa Neehal ido,  " wallahil shine mijina ko a gigin mutuwa na ganshi zan gane shi,
dan bazan tab'a manta fuskar bak'in kumurcin daya sare ni ba,  wanda har yanzu ina d'auke da dafinshi,
a haukace Najwah tayo kan Neelah tamkar zata yagi naman jikinta,  saurin rik'eta Neehal yayi,
ta shiga fizge-fisge tana k'ok'arin kwacewa, takawa Nauman yayi gaban Neehal had'i da nuna mishi yatsa yace,
" kayiwa wannan mahaukaciyar matar taka magana ta shiga hankalinta, wallahi muddin ta sake hannunta ya tab'a jikin Neelah sai nayi shari'a da duk uban daya d'aure mata gindi koda hakan yana nufin kawo k'arshen alak'ar dake tsakanina dakai,
yayi maganar yana kallan Neehal ido cikin ido,  Neehal bayyi magana ba yaja hannun Najwah suka bar wajen,
gaban Naufal da Umairah dake tsaye tamkar an dasa su Neelah taje,
cikin matsanancin kuka tace " wallahi Allah ba k'arya nake yi ba,  shine babansu Nail,  he's their biological father Allah ba k'arya nake ba,
tamkar mahaukaciya ta juya gasu Daddy tace " Daddy Mamy Allah shine mahaifinsu Nailah ban tab'a sanin wani d'a namiji ba sai shi,
ganin yadda ta firgice ta zama tamkar mahaukaciya yasa Mamy ta rungumo ta jikinta,
ta kwantar da kanta saman k'irjinta tana shafa kanta muryar Mamy na rawa tace,
" mun yarda dake Neelah,  wallahi tun ranar da kika haihu muka san yaran nan jininmu ne,  mu muka haifi Neehal munfi kowa saninshi,
duk da yayi k'ok'arin dakewa wallahi yana cikin tashin hankali,  bamu yi magana bane dan muna san muga me zayyi,
wacce k'aryar zayyi, da wanne salan rainin wayon zai zo,
cikin sanyin jiki Daddy ya d'ora hannunshi saman kanta yace " ni kunyarki ma nake ji Neelah,
wallahi kunyar had'a ido dake nayi,   kunyar yi miki magana nake yi,  na rasa ta inda zan fara, na rasa ta inda zan b'ullowa al'amarin,
Neehal yayi matuk'ar bani mamaki, amma bakomai gobe in sha Allah za'ayi ta tak'are,
Mamy ta kalli Umairah tace " zo ki kaita bedroom d'inta,  saurin amsarta Nauman yayi ya nufi bedroom d'in da ita,
Naufal da Umairah suka bisu,  cikin sanyin jiki ya zaunar da ita kan gado,  ya zauna a k'asa a gabanta,
hannunshi cikin nata,  Naufal da Umairah suka zauna saman gadon suka sanya ta tsakiya,
Naufal ya sanya hannunshi yana goge mata hawaye had'i da girgiza mata kanshi,
a hankali Umairah ta sauke ajiyar zuciya ta rafta tagumi hannu bibbiyu,  tace " amma fa abun da mamaki ace Neehal ne ya aikata irin wannan aikin,
Nauman yace " ni tun a bayan naso na fuskanci wani abu,  saboda lokacin daya dawo daga baukar k'asa yanayinshi yayi masifar canjawa,
sannan sau uku yana k'ok'arin fad'amin wata magana sayya share a lokacin har tambayarshi nayi yace min sirrin ciki sai hanji,
ashe abinda yake nufi kenan, haka lokacin daya dawo Nigeria daga Dubai,
danake bashi labarin Neelah bakiga tashin hankalin daya shiga ba, ya tsare ni yace sai na sanar dashi sunanta,
Naufal yace " Umairah kin tuna lokacin da muke cin abinci a dinning Daddy ya tambaye ki ina zaki wannan karon kika ce Taraba State k'aramar hukumar hard'o-koa'la?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now