33

7.1K 405 82
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣3️⃣

Neehal baibi ta kan Najwah ba, ya rarrafa gaban Neelah bisa gwiwowinshi,
ya rik'e k'afarta yana gunjin kuka mai d'imauta ma'abocin sauraro, yayinda hannunshi ke dafe da k'irjinshi,
bakinshi ya bud'e da nufin yin magana amma ya kasa saboda hakkin dayaci k'arfinshi, kanshi ya sunkuyar k'asa yana cigaba da hakkin,
while jini baibar zuba ta hanci da bakinshi,  dakyar yayi k'arfin halin bud'e bakinshi,
yace " please  Neelah  ki so ni, karki bari na mutu, wallahi ina sanki, ina matuk'ar sanki,
fuska Neelah ta tsuke yadda kasan anyi mata sammacin mutuwa,
tace " SO!  ni kake son ko waccen!?

Ta fad'a tana nuna Najwah dake kwance bata motsi, bakinshi na rawa yace " ke!  wallahi ke nake so, ke kad'ai nake ji a zuciya ta, ke idanuwa na ke gani,
" oh!  yanzu ni kake so ba ita ba,  bayan da ita kake so ba ni ba, gaba idan ka kuma ganin wata kace ita ba ni ba,
ta yamutsa fuska had'i da mik'ewa tace " ban san namiji me zara da rawan ido, yau yace wacce gobe yace waccen,
idan yau ya gano wata gobe wata zai kuma hangowa, Allah ya amsa addu'a ta daya bani namiji d'aya tamkar da dubu,
ta fad'a tana k'ok'arin barin falon saurin rik'o k'afarta ya kuma yi yana zubewa k'asa rub da ciki,
idonshi na rufewa da bud'ewa yace " please!....!,  bata bari ya fad'i abinda yake da niyyar fad'a ba,
ta fusge k'afarta tayi shigewarta bedroom,  "Nauman zo ka duba Najwah please bata motsi, 
Mamy ta fad'a cikin tashin hankali,  Nabeelah tace " bata numfashi ma,
jikin Nauman na rawa ya nufi fridge ya d'auko mai sanyi,  ya b'alle murfin robar ya tsiyayewa Najwah gaba d'aya,
da k'arfi ta sauke ajiyar zuciya tana fitar da numfashi dakyar,
a hankali ta bud'e idonta tana bin mutanen dake parlor'n da kallo d'aya bayan d'aya,
kallan juna suka fara yi ganin irin kallan da Najwah ke yi musu,
cikin sanyin jiki ta mik'e ta zauna saman sofa while tana cigaba da kallan kowa batare data furta koda kalma d'aya ba,
kallan Nauman Daddy yayi cike da alamun tsoro yace " lafiyarta kuwa Nauman?

Bakin Nauman na rawa yace " DA KAMAR WUYA (MY UPCOMING NOVEL)  bari na duba, 
Nauman ya dad'e yana duba ta kafin ya sauke nannauyan ajiyar zuciya yace,
" her brain is in hook,  is like loosing memory, but bai kai looking memory had'ari da matsala ba,
kwakwalwarta ta tsaya cak ta daina aiki,  "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Taheerah mun shiga uku,
Mamy ta fad'a cikin matsananciyar damuwa, Daddy yace " meye abin yi yanzu?

Nauman yace " gaskiya babu wani abinyi sai dai addu'a dan babu maganin da zayyi mata aiki a halin data ke ciki,
" zai kai tsayin wanne lokaci kafin ta dawo dai-dai?

"Eh!  to babu tsayayyan lokaci but at anytime tana iya dawowa hayyacinta,  firgita, tsoro, razana, ko tashin hankali da kid'ima ke sanya mutum shiga irin halin data shiga yanzu,
dakyar Neehal ya dafa bango ya mik'e ya soma takawa dakyar yana had'a hanya,
da sauri Naufal ya rik'e shi ya zauna saman sofa, yace " please duba shi Nauman....,
" wallahi idan ya sake ya tab'a ni sai  nayi shari'a da shi,  ya fad'a yana cigaba da hakkin,
mik'ewa Neehal yayi yana tangad'i yabar parlor'n duk suka bi bayanshi da kallo, 
bayan Nabeelah ta koma gida ta sanarwa iyayenta abinda ya faru,  basu tausayawa Najwah ba,
sai ma dad'i da suka ji, Abbanta yace " Allah ne yayi maganinta da kanshi, ya kuma nuna mata kuskuranta akan shiga hurumin Ubangiji datake k'ok'arin yi,
duk gidan babu wanda ya kira ko a waya yaji ya take balle suje su dubota,
da Nabeelah ta nace kan tana san taje ta zauna da ita fad'a Ummansu tayi tai mata,
misalin k'arfe 11:00 na dare Neehal yana kwance saman sofa, hannunshi d'aya saman k'irjinshi,
while d'aya hannun yana dafe da kanshi abin duniya ya isheshi,  zambur ya mik'e yadda kasan an tsikare shi,
a hankali ya tura k'ofar bedroom d'inta ya shiga, ganin bata ciki yasa ya fara dube-dube yana nemanta,
motsi ya jiyo bathroom dan haka ya nufi bathroom d'in ya shiga kanshi tsaye,
jin an shigo yasa Neelah saurin kallan k'ofar bathroom d'in,  ganinshi tsaye yasata zaro ido tana kakkafe jikinta,
kasancewar wanka takeyi ya shigo, " dalla Malam meye haka?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now