35

6.5K 387 48
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣5️⃣


Tunda Neelah ta isa Sunkhanni Dada da Abpa suka sanya ta gaba suna tambayarta abinda ke faruwa, ganin yadda take kuka,
" Malam ni fa al'amarin yarinyar nan ya fara bani tsoro, tunda ta zo tak'i magana sai kuka kawai take yi,
ido Abpa ya zuba mata na tsayin lokaci kafin ya fitar da numfashi yana kallan Dada yace,
" bari naje wajen Mani me waya na kira can birnin naji lafiya, da sauri Neelah tace " a'a dan Allah karka kira su bana san susan ina nan,
cikin mamaki Abpa da Dada suka kalleta, Abpa yace " kamar yaya kar'a kira su?

"Eh!  dan Allah Abpa!, "ke lafiyarki lau kuwa?

Cewar Abpa yana gyara tsayuwarshi, cikin  matsanancin kuka tace " idan ka sanar dasu inanan shima biyoni zayyi,
" wa!?

Dada da Abpa suka fad'a a tare, " Neehal,  ta basu amsa tana k'ara sautin kukanta,
" waye haka?

"Babansu Nail, a razane Abpa da Dada suka ce " wa!?

"Dama kuna tare dashi acan birnin?

Kanta ta girgiza alamar a'a, cikin rashin fahimta Abpa yace " kiyi mana bayani yadda zamu gane mana Bingel, 
muryarta na shak'ewa ta sanar dasu komai tun daga farko har k'arshe tas,
shiru Abpa da Dada sukayi suka kasa furta komai, d'an nisawa Abpa yayi had'i da cewa "  yanzu Bingel kina nufin yaron nan d'an Alhaji Bilal ne?

"Eh!, tace tana share hawayenta,
" iko sai Allah, Ubangiji me yin yadda yaso,
ya gudu ya barki yana tunanin ya rabu dake har abada sai gashi Allah ya nufa iyayenshi sun rik'e ki,
haka suma batare da sun san alak'ar dake tsakaninki dasu da yaranki ba suka rik'e ku hannu bibbiyu,
amma abin da mamaki......!  ihuuuun Neehal da suka jiyo yana kwalawa Neelah kira ne ya katse Abpa,
da sauri Abpa dasu Nailah da Dada suka nufi inda suke jiyo ihuun Neehal,  ganinshi suka yi ya nufo bukkarsu,
yana tangad'i da had'a hanya tamkar wanda yake cikin mayen mutuwa, a tub'e daga shi sai wondo iya gwiwa,
babu ko takalmi, k'afarshi na zubar da jini saboda k'ayoyin daya taka,
amma bai kula dasu ba, ya cigaba da taka su, while yana hakki tamkar ranshi zai fita,
ya jik'e sharkaf da gumi, yana tafe jini na d'iga daga hancinshi, duk ya b'ata mishi jiki,
gaba d'aya jama'ar k'auyen yara da manya suna biye dashi, har da me gari,  ganin yadda Neehal ya koma ya sanya su Neelam fashewa da kuka,
sautin kukansu ne yaja hankalin Neehal zuwa gare su, duk da baya gani sosai, dishi-dishi yake gani,
hakan bai hana shi gane Neelah ba, sauri ya k'ara yana jan k'afarshi dakyar ya isa gare ta,
yayinda tsananin mamaki ya yana Malam Liman motsawa,
sauran jama'ar garin kuwa suka fara k'us-k'us a tsakaninsu suna magana k'asa-k'asa,
zubewa yayi gabanta yana rusgar kuka wiwi tamkar wanda ake zarar ranshi,
batare daya iya furta koda kalma d'aya ba, yana daga durk'ushe yaja ciki gaban Malam Liman da Dada,
ya had'e hannuwanshi biyu alamar bada hak'uri yana cigaba da kuka wiwi batare dayayi magana ba,
dakyar ya isa tsaida kukanshi yace " bani da bakin da zanyi amfani dashi wajen baku hak'uri,
bani da kalmar da zata goge muke tabon danayi muku, bani da maganin zai warkar da ciwon dake zuciyarku,
bani da abinda zai kawar da d'aci, rad'ad'i gami da k'uncin dana dasa muku a rayuwarku,
amma dan Allah dan girma fiyayyan halitta kuyi hak'uri ku yafe min,
na gane kuskure na, Allah ya jarrabe akan abinda nafi rainawa da kyama a rayuwata, abinda nayi zaton bashi da wani amfani a rayuwata,
dan Allah Abpa kuyi hak'uri ku yafe min laifin dana yi muku, nasan hak'k'inku ne ke wahalar dani,
abinda nayi muku shine yake addabar rayuwata, ya hana ni kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi, ya hana duniyata sakat,
kunyi min alkhairi na saka muku da sharri, kunyi min halacci nayi muku butulci,
kun bani dukkan farin cikin duniya, kun kub'utar da rayuwa amma nayi muku muguwar sakayya,
dan girma Allah Abpa ba danni ba ku yafe min, ya k'arashe maganar yana fashewa da kuka.....!,
hawaye Abpa ya goge yana murmushi ya d'ago Neehal daga durk'ushen dayake ya rungume shi,
" baka yi min komai ba, imma kayi min na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba d'aya,
karka damu da abinda ya faru a baya, dan hakan muk'addari ne daga mahaliccin mu, akwai kuma dalilinsa nayin hakan,
muyi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, Abpa na gama rufe bakinshi motocin su Daddy nayin parking,
cikin hanzari suka bud'e motocin suka fito gaba d'ayansu,
bak'aramin dad'i Daddy yaji ba ganin Neehal rungume a jikin Abpa, hakan ya tabbatar mishi da Abpa dattijon arziki ne.

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now