36

8.2K 439 71
                                    

https://www.youtube.com/channel/UCT-hhCorDLc2vtszexn6klw

*PLEASE SUBSCRIBE TO MY CHANNEL ON YOUTUBE,  DAN GIRMAN ALLAH KUYI SUBSCRIBE D'IN TASHA TA (CHANNEL) A YOUTUBE DAN NUNA TSANTSAR SOYAYARKU GARE NI,  TA HAKA NE ZAN ZANE SOYAYYA, KULAWA, K'AUNA DA KUKE YI MIN*

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA

_*RABO AJALI...!*_
_*SAKI RESHE...!*_
_*WATA SHARI'AR...!*_
_*DUK NISAN DARE...!*_
_*NISAN KWANA...!*_
_*NADIYA...!*_
_*ABU A HUDU...!*_
_*DA KAMAR WUYA...!*_
_*SAKI NA DAFE...!*_

3️⃣6️⃣

Tsoki Nauman yaja had'i da dafe k'irjinshi yace " wallahi ka tsorata ni, nayi zaton Mamy ce ta kama ni,
" kam!  dan ubanka dama abinda kake yi kenan?

"Cikin dare kake lallab'owa kazo, wai uban ma me kake zuwa yi?

"Ubanka nake zuwa yi, shege kai zaman uban me kakayi da har yanzu kake zaune a parlour?

"Abinda kazo yi yanzu nima shi nake zaman jiran yi, cikin dariya Nauman yace " shege d'an iska munafuki,
to saina fad'awa Mamy tunda abinda kake yi kenan, "out of correction nake yi ko dai muke yi?

"Ni da kai Ali yaga Ali ne, ko kuma d'an juma da d'an jummai ba, Neehal ya fad'a yana dariya,
"Yo ba dole muyi satar layi ba tunda an hana mu matanmu, dan haka mu rufawa juna asiri, ka shige d'akinka iyalinka nima na shige d'akin iyali asubar fari mu d'au hanya,
dariya suka saka gaba d'aya had'i da tafawa, Nauman yayi saurin d'ora yatsa saman lips d'inshi tare da cewa " shhhhhhhh!  rufa mana asiri karka taso mana Mamy danna lura da ido d'aya take bacci,
" yo inda a tsaye take kwana ai wanda ya riga ka kwanciya dole ya riga ka tashi,
suka kuma saka dariya, Nauman yace ni dai nayi nan, kana cinye min lokaci, ya fad'a nufar k'ofar d'akin,
da sauri Neehal ya fisgo shi yace " gidan ubanka zaka dakayi nan hanyar?

"Ko bakaga hanyar d'akin iyali na bane!?

"Duba da kyau shege jaraba ta makantar dakai hanyar turakar iyali na bi,
inji ubanka Neehal ya fad'a yana kallan k'ofar d'akin, shiru yayi had'i da sosa kanshi yana murmushi yace " wallahi sai naga kamar d'akin Neelah ne,
ashe d'akin Suhaima ne, hararshi Nauman yayi batare dayayi magana ba ya nufi k'ofar d'akin,
" haka wanda ya riga ka zuwa duniya dole yafika sanin takan duniyar ba,
suka jiyo muryar Mamy na fad'a, idanuwa suka zaro waje cike da tsoro, Nauman ya kalli Neehal, shima ya kalli Nauman,
kai Neehal ya d'agawa Nauman alamar ina mafita, Nauman ya girgiza kanshi alamar babu,
" ku juyo mana d'an juma da d'an jummai, idonsu runtse suka juyo, Mamy ta kama kunnensu tana murmushi,
tace " dama abinda kuke yi kenan?

Da sauri suka girgiza kai, "Ok meya kawo ku?

"Bakomai suka ce kansu k'asa, "waya fara zuwa?

Da sauri Neehal ya nuna Nauman, shima ya nuna Neehal, " wato abinda kuke yi kenan ko?

" imma hakan suke yi ai laifinki ne tunda kin rik'e musu matansu,
Daddy ya fad'a yana saukowa daga steps, nufar Daddy sukayi gaba d'ayansu,
cikin marairace fuska Nauman yace " yauwa Daddy shigar mana, " ku kwantar da hankalinku daga yau ba sai kunyi satar hanya kun hauro ta katanga ba,
gobe in sha Allah matanku zaku tare ko mutum ya yarda ko bai yarda ba, ni da kaina zan kawo muku matanye har gida,
" wa!?

"Tab! ai Allah yadda ake kai kowacce amarya haka za'a kai min 'ya'ya gidan miji,
" to na baku nan da kwana biyu ku gama shirinku akaisu, adaina barmin yara suna haurowa,
" Allah Daddy ba haurowa muke yi ba, Neehal ya fad'a cikin shagwab'a, Daddy yayi dariya, kana yace " tom naji ba haurowa kuke yi ba,
kuje ku kwanta,  da sauri Neehal ya nufi d'akin Neelah, Mamy tayi saurin jan rigarshi ta baya had'i da nuna mishi k'ofar fita,
tace " ba nan ne hanyar ba ga hanyar nan, suka fita suna dariya, washe gari Mamy ta tada shirin tarewar amaren, da kanta takaisu saloon aka gyara musu kansu,
aka wanke musu k'afa had'i da zana musu lalle me black & red wanda ake kira da Arabian Henna,
kasancewar gaba d'ayansu farare ne lallan yayi masifar yi musu kyau, Mamy taso 'yan kai amarya su kai su,
amma Daddy ya hana yace sunnah zai raya shi da kanshi zai kai 'ya'yanshi gidan miji,
dole tasa Mamy ta hak'ura, bayan an idar da sallar ishaa Daddy ya tara amaren da angwayen harda Umairah da Naufal,
babu kiran da ba'ayiwa Najwah ba amma tak'i zuwa,  sosai Daddy yayi musiha, ya basu misalai da ayoyin Alkur'ani da Hadisai,
musamman Neehal me mata biyu, ya nuna k'arara yafi son Neelah, Daddy yayi mishi fad'a kan yayi adalci a tsakaninsu,
sunso Daddy ya basu matansu su tafi amma yaki,  Suhaima aka fara kaiwa, kana aka kai Suhaira da Suhaila,
Neelah ce k'arshe,  Daddy ya k'ara yi musu nasiha me ratsa jiki, sannan ya kalli Nauman yace " kira min Najwah,
ba musu Neehal ya mik'a ya shiga part d'inta,
bisa mamakinshi bata gidan, ya duba ko'ina bai ganta ba,  sosai yayi mamakin rashin ganin Najwah a gidan,
ya juya zuwa parlour inda yabar Daddy yana tambayar kanshi inda Najwah ta tafi,
cikin girmamawa ya durk'usa gaban Daddy yace " tayi bacci, " ok to ba damuwa Allah ya baku zaman lafiya, ya had'e kan zuri'arku,
suka amsa da amin, Daddy ya mok'e ya fita, Neehal na ganin Daddy ya fita, ya motso kusa da Neelah,
a shagwab'e tace " please kaje ka raka shi, k'ara matse ta yayi yana shinshinar wuyanta yace " aiya tafi,
" a'a nidai please kaje ka raka shi, ta fad'a kamar zatayi kuka, ya mik'e yana dariya yace " bari naje,
sai da raka Daddy har bakin mota kana ya dawo, bai same ta inda ya barta ba, ya nufi bedroom, a tsakiyar bed ya iske ta tayi zaune tana rufe da mayafi,
a hankali ya cire babbar rigarshi ya aje kana yahau saman gadon, ya d'ora kanshi saman cinyarta,
yana k'ok'arin d'age mayafin tayi saurin kawar da kanta, murmushi yayi mai sauti, yace " yau kuma rowar fuskar ake yi min?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now