20

4.7K 287 32
                                    

_*RABO AJALI...!*_

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''

LITTATTAFAINA MASU ZUWA
SAKI RESHE...!
WATA SHARI'AR...!
DUK NISAN DARE...!
NISAN KWANA...!
NADIYA...!
ABU A HUDU...!
DA KAMAR WUYA...!
SAKI NA DAFE...!

2⃣0⃣

Da sauri Umairah tace " eh sosai ma, karatu sai kin zab'i wanda zakiyi,
Neelah na haki tace " zani...! zan biki birni ki saka ni a makaranta,
dai-dai lokacin Abpa da Dada suka k'araso wajen, Neelah ta cigaba da cewa,
" ina san nayi karatu sosai, ina san na nunawa mutane masu k'amari da ji dakai,
had'i da shiga hurumin Ubangiji suna yiwa Allah shishshigi cewar babu wanda ya  san gaibu sai Allah,
haka babu wanda ya isa yasan me gobe zata haifar sai Allah, ina san na tabbatar masa zan amfani kai na da rayuwata in sha Allah,
tayi maganar cikin zafin rai da bushewar zuciya,
kai da ganin yadda take maganar da yadda ta kafe idonta akan Umairah bata ko k'iftawa zai tabbatarwa mutum zuciyarta ta zama k'ek'ashewa,
kallan jama'ar da suka taho tare Umairah tayi had'i da had'iyar yawo kut,
saboda yadda Neelah ke magana ya tabbatar mata tabbas akwai wani abu dake cin zuciyar yarinyar,
cikin mamaki da tsoro Abpa yace " me...!?

"Neelah kin san me kike fad'a kuwa....!?

Batare data kalleshi ba tace " eh Abpa'am nasan abinda nake fad'a cewa nayi ina san tafiya neman ilimi
ina san nima nayi alfahari dakai na, kuma kuyi alfaharin haihuwata da kuma kasancewata 'yarku,
jikin Dada na kerrrrma ta k'arasa inda Neelah ke tsaye ta rik'e hannunta tana k'ok'arin janta,
kafewa Neelah tayi tak'i motsi, cike da jin kunya Dada ta d'ago kanta ta kalli jama'ar k'auyansu,
da sukayi cincirundo suna kallansu, d'an murmushin yak'e Dada tayi tana rik'o Neelah,
muryarta k'asa-k'asa tace " mu tafi bukkar mu, a hankali Neelah ta zame jikinta daga na Dada ta nufi Abpanta,
wanda ke tsaya yana kallanta, idonta kanshi tana zubar da hawayen bak'in ciki,
tace " dan Allah Abpa'am karka ce a'a, dan Allah karka hana ni tafiya neman ilimi,
yasha fad'a min bazan tab'a morar rayuwa ta ba, yasha ce min bazan tab'a amfanar rayuwa ta ba,
yasha ce min haka zan k'are cikin wahala da tsantsar bak'in cikin rayuwa,
dan Allah Abpa'am karka bari maganarshi ta zama gaskiya,
ko kana so maganar shi ta zama gaskiya.....!?

"Kana san na rayuwa cikin k'unci da bak'in cikin rayuwa....!?

" Kana san na zama marar amfani ta yadda bazan iya amfana da morar rayuwa ta ba balle har wani ya amfana daga gare ni.....!?

" Abpa'am kana san na zama marar amfani da mamora na  k'are rayuwa ta cikin k'unci da takaicinshi.....!?

"Ko kana san maganganun shi su zama ajali na, bak'in shi ya zama sanadiyyar  mutuwata bayan ga dama ta samu Allah ya kawo hanya mafi sauk'i da zan mayar da maganganun shi tamkar almara ....!?

Abpa'am muddin na cigaba da zama anan maganganunshi zasu zama gaskiya,
zayyi galaba akaina, dan nasan wallahi Allah bak'in ciki ne zayyi ajali na,
shiru Abpa yayi idonshi kanta, yana sauraran maganganunta
" sau d'aya tak a rayuwata Abpa ta na rok'e ka alfarmar yadda zanyi da rayuwata,
sau d'aya tak ina rok'okanka dan girma Allah Abpa ka barni nabi zab'in zuciya da rai na,
ka bari na bar wannan k'auyan da kowa ke kyamata kowa yake raba 'ya'yanshi dani suke hana su wasa dani, har suke neman camfani,
na zama tamkar mujiya, ku kanku sanadi na kun sha yin kukan bak'in ciki,
saboda ni kuka daina shiga taro, Abpa'am saboda da ni har sallah a masallaci dai na fita kayi,
k'asa-k'asa 'yan k'auyan suka fara maganganu suna cewa " oh! ji rashin kunya k'iri-k'iri wajen yarinyar nan dan Allah....!,
Saude tace " yo yarinyar data san dad'in namiji dama meye bazata yi ba,
wani yace " hummm ai kad'an ya gani ma, badai san abin duniya ne yasa ubanta ya bada aurenta ga wanda bai sani ba, ai idonta ya riga ya gama bud'ewa tarr bata da wata sauran kunya yanzu,
ido Abpa ya runtse da k'arfi yana jin zafin maganganun mutanen,
" dan Allah Abpa'am karka bari maganganunsu suyi tasiri a kanka da zuciyarka,
karka bari maganarsu ta rinjayi ranka, dan Allah kada ka kula da abinda zasu ce ko abinda suke fad'a,
babu abinda basu riga da sun fad'a ba, babu wata magana mai zafi ko bak'ar magana wacce ta rage basu jefe mu da ita ba,
babu wani abu da zasuyi ko su fad'a yanzu wanda zayyi mana zafi, balle har mu kula dashi,
sosai zuciyar Umairah da jama'ar da suka zo tare ta karye, cikin matsanancin tausayawa,
Umaira ta bud'e baki da niyyar yin magana, Abpa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu,
fuskarshi a had'e murtuk yadda kasan bai tab'a yin dariya ba,
ganin haka yasa Neelah durk'ushewa k'asa had'i da fasa matsanancin kuka,
ta zube a gabanshi tare da kifa kanta saman k'afafunshi,
ta rik'e shi gam da duka hannayenta tana rusgar kuka da iya k'arfinta,
tana cewa " shikenan yayi nasara akaina, ya ci galaba akaina, tabbas muganganunshi gaskiya ne,
dayace bazan tab'a amfanar rayuwa ta ba, balle na amfani wani,
yayi gaskiya dayace a haka zan k'are cikin wahala da tsantsar bak'in ciki tare da k'unci,
yayi gaskiya dayace bazan tab'a ci gaba a rayuwa ta ba, yayi gaskiya daya ce rayuwa ta bata da amfani,
yayi gaskiya dayace....! kukan datake yi ne ya sark'eta ta kasa k'arasa maganar ta,
sosai ta cigaba da kuka tana cewa " mutuwa zanyi, wallahi Abpa'am Dada'am mutuwa zanyi,
rayuwa ta bamai tsayi bace, haka Allah ya tsara bazanyi tsayin rai ba,
ajali na a kusa yake, ta k'arasa maganar tana zamewa gefe,
Abpa ya kafeta da ido kwalla na gangarowa daga idonshi, dan sosai maganganun Neelah suka karya mishi zuciya,
while Dada na tsaye gefe batace komai ba, cikin karaya Neelah ta cigaba da cewa,
" dan Allah Abpa'am karka karya min kwarin gwiwa ta, karka bari gaba d'aya buri da mafarkaina su tafi a banza,
dan Allah Abpa'am ka cika min buri na, sau d'aya tak a iya tsayin rayuwa ta na tab'a rok'arka abu, dan Allah karka k'i yi min Abpa,
sau d'aya na tab'a nuna maka abinda raina ke so da zab'in rai na, a baya zab'inka  nakasance ina bi, kuma zan kasance mai bin zab'inka har izuwa k'arshen rayuwata,
nayi maka alk'awarin duk abinda kace nayi shi zanyi, duk abinda kace na bari zan bari,
duk abinda ka zab'arwa rayuwa ta shi zanyi, dan nasan bazaka tab'a cutar dani ba,
a hankali  Abpa ya sauke ajiyar zuciya, gami da sanya hannu ya goge hawayen dake gangarowa saman kuncinshi,
kana ya d'ago Neelah suka fuskanci juna yace " kin tabbatar duk abinda nace kiyi shi zakiyi....!?

RABO AJALI...!Where stories live. Discover now