9

4.2K 316 0
                                    

9⃣

        Zuwa yaukam gidan yagama cika, kowa ya hallara, Anty Amatullah ma sun iso, hakama Anty shukurah.
     Aikam su Aysha suna cin uwar aiki, aduk lokacin data ke6e kanta gefe takanyi kuka Na tausayin kanta, haka kawai takoma boyi-boyi agidan wasu, dagatanta dakomai, ya ALLAH ka kawomin iyakar wannan bauta, takuma fashewa da dakuka, ada idan wani yace zata tsinci kanta awannan yanayin wlhy saita k'aryatashi, amma gashi silar maraici komai datama rayuwarta tanadi yagama wargajewa, k'addara ta guntule mata karatunta, maraici ya rabata da iyayenta da 'yan uwanta, duk wani gatanta ya ku6ce mata.....
    Aysha! Aysha!! Waimikike tunanine? 'Yar karamarki dake harkin fara saka rayuwarki a garari?, haba Aysha, ki k'ar6i k'addararki da hannu biyu mana, akwai yara irinki dasuka fad'a fiye da halin dakike ciki, kodan ni har yanzu bakisan nawa tarihin baneba?. yanzu kitashi kije Maman yara nakiranki.
      Share hawayenta tayi, jiki a sanyaye tamik'e tafita.

Gwaggo bintu nazaune bakin katifarta tana k'idaya kud'i masu uban yawa, shigowar Aysha baisata dainawaba, saidai ta nunama ayshar gefen katifa alamar tazauna.
     Saida tagama tsaf sannan tadubi Ayshar tana washe baki, shatun gwaggo kenan, yanaga fuskar taki haka? Kuka kikayine?.
        A'a gwaggo, abune yafad'amin a idona, amma bishirah taciremin.
   To madallah.
Yanzudai Albishirinki.. 
     Cikin mamaki Aysha tace, "goro", Dan yau itace rana tafarko da gwaggo bintu tasakar mata fuska tunda tazo gidan.
      Yauwa shatuna, dama wani alkairine yazo miki, burinki yacika yau, hajia babbace ke tambayata kinyi karatu? Shine nace eh, amma iyakarki aji uku ko?.
    gyad'a mata kai Aysha tayi kawai.
   Yauwa, to shine tacemin akwai d'iyar k'anwarta kaltume a k'asar waje, tanada ciki, kuma cikin nabata wahala, shine akeso ajedake kizauna da ita harta haihu, daga nan kuma saikici gaba da karatunki a can k'asar wajen, tak'are maganar da washe baki.
         Dukda Aysha k'aramar yarinyace batakai girman hangen nesaba, amma saitaji maganar bata kwanta mata araiba.
     Amma gwaggo kekuma kin yarda damaganar tasune?.
      Eh mana nayarda Aysha, ni aii karatun nake miki kwad'ayi, yanzu hakama nakira Yaya bilya nasanar MASA komai, kuma sunyi magana da hajia babba, mamankima ansanar mata, kuma duksun amince, yanzu zakuje anjima ayimiki hoto Dan nanda sati d'aya zaku bar k'asarma.
        Gwaggo! Sati d'ayafa kikace?.
     Eh sati d'aya nace, kenifa banason iyayi, inama laifi data za6eki, baga bishirah nanba amma tace ketakeso saboda kinada hankali da ilimi, amma shine zaki kawomin shirme.
        Kwallar data cikama Aysha ido tasamu damar zirarowa akumatunta, batadamu da sharewaba, muryarta narawa tace, "to gwaggo Na amince, amma yaushe zanje Kano? namusu sallama, gakuma bikinsu Yaya Fadeela ma yakusa, koza'a bari sai bayan bikin?.
          A'a Yaya yace basaikinzoba, tunda zakuzo Idan Zata haihu, bikinsu Fadeela kuma aibadole saikina nan za'ayiba. Amma zantanbayi hajia babba idan lokacin yayi saisu sakoki a jirgi kizo kiyi kwana hud'u ko?.
     Shiru Aysha tayi saboda k'unar da zuciyarta kemata, kokad'an zuciyarta bata amshi wannan zancenba, amma tamik'a lamarin ga ubangijin talikai.
  
Su Aysha anje anyo hoto, hajia kaltume Ce tazo sukaje, daganan sukaje har airport nanma sund'an dad'e sannan aka dawo da'ita gida.
      'Yan gidan basusan hidimar da'akeyiba, Dan gwaggo bintu tagargad'i Aysha akan kada tasanarma ko bishirah.
   Sosai Aysha tarame, saita k'ara tsawo da fari, tak'ara zama silent sosai, kuka kam hartayi ya isheta, taduk'ufa tana sanarma ALLAH kukanta, Dan kokad'an tafiyar bata kwanta mata Araiba, haka kawai takeji akwai lauje cikin nad'i akan tafiyar, saidai batada madafar dafawa barema tasami hangar ku6uta daga tarkonsu hajia babba, gawani abinda kebata mamaki, ayanzu sosai gwaggo bintu kebata kulawa, gawasu magunguna datake bata Wanda tarasa namiye?, ita kanta hajia babba yanzu tarage mata kallon wulak'anci, takuma hana yaranta hantararta, yanzu ko aikin gidanma gwaggo bintu bata barinta tayishi, lamarin nadamunta gaskya.

______________________
     Wajen k'arfe biyar Na yamma su Aysha suna harabar gidan zaune itada bishirah, hira sukeyi, amma bishirace k'arfin firar tayau, Dan kokad'an yanzu Aysha batason yawan magana, yanzu hakama batawani fahimtar firar da bishiran kemusu, takasa hankalinta waje ukune, firartasu, dakuma tunanin gida, saikuma ya khaleel dayafito daga k'ofar babban falon gidan, sanye yake cikin jajayen kaya masu ratsin bak'i, ko ina ajikinsa arufe yake, kayan suna kama Dana training, yarik'e hular kamar tamashin ahannunsa, taku yake cikeda isa irinta zaratan maza k'arfafa masuji da tashen samartaka, yayinda yagittasu sai k'amshinsa yagauraye hancinansu, Aysha Na mamakin yanda kulum dakalar k'amshin dazakaji ataredashi, baka isa cewa ga ainahin turaren dayake sakawaba, kullum da kalar kamshin dazakaji ataredashi.
       Gani sukai yak'arasa wajen wani k'aton mashin mai masifar k'yau, shima jane da ratsin bak'i, dakayan da mashin d'in iri d'ayane, bawani mashin baneba illah (Power bike🏍).
         Hular kwanon yad'ora ahannun mashin d'in sannan yaymasu Aysha nuni da hannu alamar suzo.
     Suduka saida gabansu yafad'i, Aysha uwar tsoro tace bishirah munshiga uku, kodai yagane muna kallonsane?.nifa harga ALLAH tsoron bawan ALLAHn nan nakeyi?.
    Aysha muje kada musake laifi.
    Atsorace suka k'araso wajen, yajingina da mashin d'in k'afafunsa sark'e da juna, hannunsa d'aya acikin aljihun wandonsa, d'ayan kuma yana wayane.
     Cikin dadd'an sauti muryarsa ke fita, yana maganane acikin harshen turanci, turanci kuma maik'yau Wanda kosu masu yaren bazasu nuna masa iyawaba, no sir karka damu, insha ALLAH zan kamasa, yanzu haka akwai plan dana had'a domin cafkesa.
    ''Ok thanks you sir!"
       Bayan ya yanke wayar baikulasu Aysha ba, yakuma kiran wani.
   Babu dad'ewa aka d'aga, yanzukam da Hausa yake maganar. Adams inafata Kun shirya? OK kakira Emanuel & Taheer, ga Joseph nan shida Youseef taredani.
   Ok, nabaku nanda 5minutes, kasan banason jira.
   Baijira cewarsaba ya yakashe wayar.
 
Dagacan Adams yace kai *j!* ko matsala.

Dubansa yamaida Kansu Aysha dake durk'ushe, cikinku waye yamin gyaran d'aki ranar?.
    Bishirah tace Aysha ce Ya khaleel.
   Key ya jefamusu yana hawa bashin d'in, gashinan aje amin gyara yanzu, idan kingama ki ajiye key d'in ahannunki idan nadawo zan kar6a, idan kuma aunty Mamie tadawo kafin nadawo kibata kawai.
        Kafi su Aysha subashi amsama harya saka hular  yaja mashin d'in yafita.

Bishirah Dan ALLAH tunda baya nan yau muje kitayani, kinga saimu gama dawuri kafin 'yan gidan sudawo, wlhy inagudun matsala, bakiga Harar da Anty Hameeda taminba ranar, nasanma daba a gabansa bane saita dakeni.
      Tabama bishirah tausayi danhaka tace mujeto.
     Aikam dandanan suka gyara ko ina yad'auki k'amshi mai dad'i, cikin minti 30 suka kammala komai, d'akin suka kulle masa suka dawo tsakar gidan suka zauna, dagashi har 'yan gidan babu Wanda yadawo har gab da magriba, sannan ya Zunnurain yadawo daga aiki, saikuma ga Muslim shida hafez amashin, da'alama su daga makaranta suke.
     Su Aysha Na niyyar tashi, d'an gwari yabud'e gate, mashinan ajere harasu 6 suka shigo gidan, ya khaleel ne agaba, bayan yakashe nasa mashin d'in yasauka tareda zare hular kansa yajuya yana kallon sauran.
      Kutabbatar kunshirya mana komai atsare gobe idan ALLAH yakaimu, kundaiga miya faru yau, so kowa yasan irin shirin dazayi.
    OK sir suka fad'a atareda Saluting nashi.
    Shima yamayar musu da murtani sannan yabasu izinin tafiya.
     Hafiz ne yak'ar6i hular yana fad'in wellcom Yaya.
     Thanks you hafez.
    Da sauri Aysha tak'arso kafin yashige, tacemasa sannu sannan tamik'a masa key d'in.
         Kar6a yayi batareda ya amsa mataba yayciki abinsa.............🖊.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now