34

3.3K 294 1
                                    

3⃣4⃣
   
        To masu iya magana nacewa d'a da mahaifa sai ALLAH, hakance tafaru da meerah, dukkan wani 6acin ranta da tsanar mahaifiyar tata datayi, hakan bai hanata kwace hannuntaba dagana ya Naufal tanufi mama da gudu tana kuka, kanta tafad'a tana rubzar kuka mai matuk'ar tada hankalin mai saurarenta.
           Ya Naufal dasu Aysha duk sunyi tsaye suna kallonsu, wasunsuma kuka sukeyi suma.
         Kusan mintuna 4 meerah da mama nata kuka, kuma suna'a rik'e da junansu.
    Ganin kukan zaiyi yawane yasaka mom matsawa ta janye meerah daga jikin mamar saboda ganin halin ciwo da mama take aciki.

Rasa inda mama zata ajiye wad'annan 'yan gayu tayi, sukam su mom babu ruwansu, tabarmar dake a falon suka zazzauna, Raudat cedai keta kuka saboda zafi bata sababa, gashi dama yaud'in da akwai rana.
      Maheer daketa faman jijjigata akan tayi shiru yace waimike damun Raudat ne? Dukta rud'e wlhy.
    Mom tamik'a hannu ta kar6eta, cikin hausarta dabatama iyaba sosai tace maybi zafine, tafara k'ok'arin cirema yarinyar Riga, mafici mama tamik'o Dan ama Raudat fifita.
    Dad yakar6a yana fifita Raudat data fara rage kukan tana sauke ajiyar zuciya ajikin mom, kai kace wata babbace.
    Saida ta tsagaita da kukan sannan mom tamik'ama ya Naufal dake kusada ita, Naufal mik'ama Meerah tabata abincinta.
       Kar6arta yayi tareda sumbatar goshinta, my dear mah-mah sorry kinji, zafine kawai yamiki yawa nasani, yamik'ata wajen Meerah da gaba d'aya hankalinta na'akan mamanta.
    Saidama ya zungureta sannan tajuyo tana kallonsu shida d'iyar tasa, da ido yamata nuni yunwa.
    Batace komaiba takar6eta tad'ora a cinya, mama dai tana kallon ikon ALLAH, da al'ajabin abinda ke shirin faruwa, wai Meerah da d'iya.
    Bata k'ara gaskatawaba saida taga tafara shayar da yarinyar sannan.

Dad datun d'azun yake kallon mama a sace, yadai daure yace nikam baiwar ALLAH Na tambayeki mana?.
      Mama tace ina saurarenka Alhaji.
     Dad yagyara zamansa, yayinda duk idon yaran ke'a kansa Dan mamakin furucinsa ga maman meerah.
             Yanisa sannan yace, kama kikemin dawata a sokoto mai suna Zainabu 'yar Dije.
      Mama da idonta yacika da hawaye, tace tabbas itace, kuma tunda kashigo nake maka kallon Sani, saidai banida tabbas akan ko yahaya ne k'anin malam Abdul'majedu?.
    'Yar zabura dad yayi, bakinsa har rawa yakeyi yace tabbas shine, Abu kina nufin da gske kece?, ina d'an uwana Abu? Kardai kice Ameerah jini nace? Karki cemin haryanzu baki canjaba Zainabu?.
     Inna lillahiwa'inna ilairraji'un, dad yashiga ambata yana hawaye.
     Tofa falo yayi tsit ana kallon ikon ALLAH, mama da dad duk kuka sukeyi, Wanda babu Wanda yasan ma'anarsa cikinsu ya Naufal..

____________________________
       Tunda suka zo gidan gwaggo bintu batada lfy, wannan yasaka matan gidan babu Wanda yasan da zuwanta gidan.
   Sun sandai zuwairah tazo, itakam dama babu matar datake gaidawa agidan, saima tazo tagama zamanta baifi tahad'u dasu Anty Mamie sau uku ba, shima sai idan tata ta fiddota daga 6angarensu, amma bada nufin gaida matan gidanba, to yanzuma girma yak'aru ga daraja, saboda dawowar mama tayi alk'awarin tadaina shiga 6angaren ko waccensu.

Iya hama ce takaima mama gulmar dawowar Gwaggo bintu gidan, harda halin datake ciki.
    Anty Mamie akwai tausayi. Wannan yasaka hankalinta tashi tanufi gefin masu aikin taduba gwaggo bintu, ganin halin datake ciki yasakata kiran Hafiz yayi driving nasu zuwa asibiti itama tana nan tahowa zata gama wani aiki.
        
Hafiz yad'auki iya hama da gwaggo bintu dake kashir6an cikin halin rashin lfy yatafi.
          Komai shiyayita k'ok'ari aka mata, har aka basu gado, sai a sannan Anty Mamie ta k'araso itada ya Zunnurain daya kawota.
      Da taimakonsu aka kammala komai, gwaggo bintu tafara samun kulawa.

___________________________

Saida sukayi kuka mai isarsu sannan falon yay tsit, dad yace Abu miya dawo daku Kaduna? Nidai nasan harna bar k'asarnan kuna sokoto?.
        Hawaye mama tashare, cikin nadamar abinda ta aikata tace yahaya ka gafarceni, tabbas ni azzalumace, kuma na cutar dakai kaida d'an uwanka.
     Tabi su ya Naufal da kallo tana hawaye, tace bara nabaku labarin wacece zainabu 'Yar dije.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now