32

3.4K 293 2
                                    

3⃣2⃣

        Cikin sand'a take fitowa daga 6angaren nasu, kaikace sata zatajeyi, ahaka tafito babban falo, ananma shuru kowa yashige d'akinsa, ya Ramadan ne kawai zaune yanata danne-danne a lap-top, da alama wani akin yakeyi, kuma aikin yayi matuk'ar d'aukar hankalinsa.
          Ahankali tabi bayansa tashiga ta kicin, ta k'ofar baya tafice, tsakar gidan ko'ina k'wanyar yake da hasken lantarki, ta tsakanin motocin dake barbaje a harabar gidan tarink'abi, kasancewar yaran gidan kowa yana gida, ya khaleel ne kawai bama ya k'asar (amma suna saran dawowarsa a yau).
        Koda ta'isa k'ofar gate d'an gwari nakan benci sai zabga gyangyad'insa Na k'addara yakeyi, tazabga tsaki tareda shurin k'afarsa, firgigit yafarka yana niyyar saka ihu, da sauri tace, "ALLAH kamin ihu sainasa baffa yakoreka, kajimin wawan mutum.
      Tuni d'an gwari yanutsu danjin muryar mufeedah, amma jikinsa haryanzu k'yarma yakeyi, ta balla masa harara tana fad'in dallah bud'emin k'ofa.
      Kamar d'an gwari zai fasa kuka yace, " madam duk randa Alhaji yagane kina fitan dare zai punishing d'ina, ki tausayamin".
        Yama kasheka ina ruwana, munafiki idanhar bakaine zaka fad'aba waye yasan ina fita, wlhy duk randa hakan tafaru sainasa ankashemin kai, kai har uwarka saina saka ankashe, kadai San banida kirki, bud'emin k'ofa jio, shashasha mara lissafi, kadamu mutane da wannan banzan hausar naka Mara dad'in ji.
      Jikin d'an gwari narawa yabud'e mata k'aramin gate tafita.
     Tana fitowa tacire k'aton hijjabin jikinta, daga ita sai guntun siket iya cinya, tasaka riga maikama da best ko cibiyarta bata rufeba, shigar tata saikace 'Yar basketball.
      Kad'an tabar jikin gidan nasu ta tadda wata farar mota 'Yar k'arama, bud'ewa kawai tayi tashige abinta.
     Hi! babe. Tafad'a tana wani far da idanu.
        Woow!! zumata kinyi k'yau, yau wankannan Na musammanne, nima zanyi biya Na musamman kam.
     Still tayi far da idanunta, cikin salon tantiranci tace ka cancanci fiye da hakama, wlhy kodagani sai 👙kace nazo maka zanzo, kai ko tsirarane.
     Wata dariyar jin dad'i yayi, yace, ''kina cikin aikina wlhy, my Mufeey, zumata kenan".
     Ya akayi yau? Naga kinfito da wuri.
     Kabari kawai, aii boss ya khaleel baya nan, kuma bansan miya saka 'yan gidan barci da wuri hakaba, Momy kuma itace da baffah shiyyasa duk nasami fitowa akan lokaci.
     Dariya yaytayi tajin dad'i, tun'a mota suka fara masha'arsu.

(Nace, "ALLAH ka shiryemu, Momy gafa abinda kike gudun, dama masu iya magana kance, *Ciki da gaskiya* wuk'a bata hudashi🤷🏽‍♀).

_______________________________

            Har yanzu kan yana ciwo my Noor?.
     A'a ya daina ma tun d'azun wlhy, yanzukam saidai baya, shima kad'an-kad'an, zuwa anjima ma zakaji shima ya daina.
    To ALLAH yak'ara afuwa, babyna dai yana baki wahala.
    'Yar dariya meerah tayi tareda kallonsa, tace, "karka damu, ai zan ramane".
    Shima dariyar yamata, yana fad'in kokuma kirame ba, wlhy nifa da Dady zaima yarda dakawai muntafi ki haihu a Nigeria, naga lil sholy tak'agara ayi tafiyarnan, tunifa tagama had'a kayanta.
       Dolene taso zuwa gida, nikaina hak'uri kawai nakeyi, shekara 9 ba kwana tara baneba, amma nafison saina haihu, sai dai kawai naje musu da d'a ko 'ya.
      Cikin murmushi ya Naufal ya sumbaci goshinta, yana fad'in ALLAH ya saukeki lfy to, aii duk yanda kikeso haka za'ayi, kece mai mulkin Naufal zuciya da rayuwa.
     Meerah tayi murmushin jin dad'i, d'an box d'in zoben Aysha Na diamond tad'akko, tace nikam Ring d'innan zaiyi nawa a kud'in Nigeria dana nan k'asar?.
     Kar6ar box d'in Naufal yayi, itakuma meerah ta tsura masa idanu dansan fahimtar wani Abu.
     Bud'e box d'in yayi, yafiddo Ring d'in sai k'yalli yakeyi, d'an murmushi yayi, batareda yace komaiba yamaida Ring d'in a box d'in yarufe.
    Meerah tace, " ya haka kuma?".
     Kamar ya?.
Tanbayarkafa nayi kud'insa, amma babu amsa kamayar ka ajiye.
     Eh, namayarne saboda bansan kud'inba, ke inama kika samu zoben?.
      Meerah tad'anyi shiru, sai zuwa can tace, ''wanine yata6a banishi, shine kawai yau naganshi akaya na d'auko.
       Shiru yayi bai tankaba, saima kanta daya d'auke daga cinyarsa yamik'e abinsa, kinga bara naje wajen Dady muyi magana, Dan inason mufara tura kayanmu kafin lokacin tafiyar mu, inasaran zuwa next week k'ilan ki haihu insha ALLAH Dan EDD d'inki yakusa cika.
    bai jira cewartaba yafice abinsa.
    Binsa meerah tayi da kallon mamaki, kenan da gaske shine yabada Ring d'in wa Aysha?.
     Tayi murmushin takaici, tareda share guntun hawayenta, ALLAH ya tabbatar da alkairi tafad'a tana mik'ewa da k'yar, insha ALLAH bazata zama shashashar maceba wajen hana mijinta abinda yakeso, Dan batasan mi ALLAH ya shiryaba akan hakan.
     Tundaga ranar bata kuma yimasa maganar ba, tamaida ma Aysha zoben kuma, sati uku tsakani meerah tatashi da nak'uda.
      Tasha wahala kam hardai ALLAH yabata ikon haihuwar d'iyarta mace, mai matuk'ar kamada kakarta mom, meerah bak'a Naufal bak'i, amma ALLAH ya azurtasu da haihuwar baturiyar yarinya mai kamada mahaifiyar Naufal, shi bai d'akko kamannintaba d'iyarsa ta d'akko.
     Fad'amuku farin cikin da familie d'innan sukayi 6ata lokacine, kamarma Aysha taji labari, jitake tamkar yayarta uwa d'aya uba d'aya ta haihu.
     Yarinya taci suna  Zainab sunan mom, zasuna cemata (Raudah) to ALLAH ya raya Raudah, bawani taron suna akayiba, amma sund'anyi party acikin gida, dangin Momy kuma da abokan arzik'in ya Naufal duk sunzo, hakama gayyarsu Aysha da Maheer, hardasu iklas da Safwan.
         Watannin Raudat biyu a duniya suka fara shirin tahowa k'asarsu ta haihuwa Nigeria.
     Fad'a muku zumud'in da Aysha keyi a lokacinma 6ata lokacine, amma nabaku dama Ku k'iyastama zuciyarku.😄

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now