16

3.8K 285 1
                                    

16

      Dolene Aysha takira wannan tafiya datazo acikin k'addarar maraicinta, sanadin maraicine yasata zuwa Abuja har hajia babba taganta, awannan ranar da'ana kuka hawaye suk'are dana Aysha sunk'are tas, tayi kuka hartaji babu dad'i.
    Amma Abu mafi cin zuciya da ruhi shine rashin ko inkula da gwaggo bintu tanuna agareta, aganinta kobabu komai tasamu sassauci ga gwaggo bintun koda kuwa Na lallashine.
   Amma Sam bahaka baneba ga gwaggo bintun.
    Har lokacin da Suka rakosu airport gwaggo bintu batace da Aysha ko yi hak'uriba, wannan ne yak'ara rura wutar bak'inciki da tsananin kishinkai ga ayshar.
   Tak'udiri aniyar inhar yakasance da gaske karatun aka turata tofa zata tsaida hankalinta waje d'aya tayishi kodan takar6ama kanta 'yanci alokacinda hakan zaizama nadamarsu gwaggo bintun.

                Tafiyace data kasance harsu kimanin bakwai, akwai hajia kaltume, sai wata matashiyar budurwa Dabaza ta wuce shekaru 28 ba, mai suna kubra, saikuma 'yanmata hud'u wad'anda dukkansu zasukai shekaru 18-19-20, Aysha ce kawai mai shekaru 14.
    Tun'a airport tafiyar tasu tarabu, hajia kaltume tad'auki 'yammata uku ita cikon ta hud'u, mukuma matashiyar budurwannance tad'aukemu nida budurwa d'aya mai amsa suna Besi, suma sauran 'yan matan nakula duk yarene.
         Gefe hajia kaltume taja Anty kubra suna magana, ak'allah sunkai 18minute's suna tare, saida aka fara kiran masu tafiya, da sauri sukayi sallama tace mutaso jirginmu zaitashi.
       Wasu hawayene masu zafi suke zarya akumatun Aysha, wai yaune zatabar k'asarta akan zalincin wad'ansu mutane, tunda take bata ta6a zuwa kudancin 9ja bama bare tabar k'asar, ko a arewacinma bako ina tasaniba, tafiya takeyi tamkar wadda kwai yafashema acikin ciki, jitake wata k'aunar k'asarta Na ratsata, tanason k'asarta amma za'a fiddata tak'arfin tsiya akaita bauta wata k'asa dabatasan kowaba.
       Anya kuwa hukumomin k'asarta suna aikinsu da k'yau?, shikenan yanda talaka bashida 'yanci cikin k'asarmu hakama bazai ta6a samun 'yanciba awata k'asar, talauci abune mai ciwo, tasanadin talauci ake hajijiya da al'ummar k'asarta Nijeria.
   Shin sai yaushene talaka zai samu 'yancine a Africa ma baki d'aya?........
      Rankwashin daya sauka tsakkiyar kan Ayshane yafarkar da ita daga nannauyan tunanin data tafi.
          K! Dallah kidawo cikin hankalinki, wlhy kikayi abinda yakawo mana Matsala saimun k'arar dadukkan danginku, kajimin wawuyar yarinya, 'Yar k'arama dake sai tsaurin ido.
       Aysha Na share hawaye tace kiyi hak'uri Anty bazan sakeba.
    Kima sake kiga abinda zai biyo baya mana.
   
    Ankira sunayen su Aysha, bayan kammala dukkan wani bincike da ainan-ainan suka samu Shiga jirgi.
        Addu'oi Aysha taitayi azuciyarta, Ashe duk yanda muke hasashe da tunanin jirgi a sararin Saminiya yawuce gaban haka, lallai dukkan wani bawa mai imani yashiga jirgi dolene ya tsarkake sunan ALLAH da k'ara yalwatar imani acikin ruhinsa, yo inba hikimar ALLAH ba, yama za'ayi duk girman jirgi yatashi sama, haryayi gudu batareda ya fad'o cikin k'asaba, lallai akwai ni'imomin ubaginji ga bayinsa akan jirgi.
          Hakadai taita tunaninta har aka kammala Kiran sunan masu tafiyar.
     Alokacin da jirgi zai tashi Aysha ta rintse idanu kam, tareda rirrik'e hannun besi dake kusada ita dukda kuwa tana d'aure da belt ne.
         Koda akazo tambayarsu mizasuci acikin jirgi Aysha KASA magana tayi, saboda batajin turanci, (kowadai yasan lalacewar makarantunmu Na arewa, inhar kanaso yaronka yaji turanci tofa saidai kasakashi private school, amma gaskiyar magana Government schools namu sunada k'arancin kulada ilimin 'ya'yan talakawa, shiyyasa kullum mune ak'asa😎).
      Da taimakon besi aka kawoma Aysha abincin, kad'an ta tsakura Dan baimata wani dad'ibama.
    Tafiyar awoyi 8 takaisu wata k'asa da Aysha batasan sunantaba, sunyi hutun awoyi 2 sannan suka samu canjin jirgi.
   Ayanzuma tafiyar awani 11 takaisu wata k'asar, anankam sun isa da daddare, Dan haka suka nemi masauki, Aysha Na mamakin k'yawun k'asashen azuciyarta, komai Nasu acikin tsari da tsafta yake tafiya bakamar k'asashenmu Na Africa ba, wanda son mulki Dana dukiya yagama kashewa, mukuma talakawan zuciyarmu tagama mutuwa saboda jiran abamu, (da wannan damar 'yan siyasar k'asarmu sukeyin amfani suna hajijiya da mu).
        Ba'a hotel suka saukaba, kubra ce takira wani yazo har airport yad'aukesu.
       Tundaga yanayin guy d'in Aysha tasha jinin jikinta, kokad'an bashida k'yakyk'yawar alak'ar dazai amsa suna mutumin kirki, tunda yakafama Aysha ido yakasa d'aukewa, tun abin nabama Aysha mamaki harya fara bata haushi tashiga Neman tsarin ALLAH daga sharrinsa.
   K'yakyk'yawan gida sukaje Wanda Aysha talura dukan gidajen sassan masu k'yaune kamarsa, (to dama turai ai ba'a cika banbance talaka damai arzik'iba, sabodasu sun tsare martabar k'asashensu).
   Komai agidan atsare yake, babu tarkacen hauka ko kad'an, saidai akwai abinda bai birge Ayshaba agidan, sune manyan hotunan 'yammata Na turawa tsirara, Aysha takauda kanta tana Jan tsaki azuciyarta.
     Bayan sunyi wanka aka kawo musu wani kalar abinci, kokad'an Aysha da besi sunkasa cinsa, gwarama besi tadaure tad'an tsakura, amma Aysha lemo taita  bankama cikinta Dan bazata iyacin wannan jagwalgwalonba.
    Amma kubra hankalinta kwance takeci, wannan yatabbatarma su Aysha ita ba bak'uwar cin irin abincin baceba, suna gamawa su Aysha suka koma d'akin da aka basu itada besi.
       Aysha tayi addu'ointa nabarci ta kwanta cikeda kewar k'asarta da iyayenta, besi nashirin rage musu hasken d'akin akashigo burum, mai gidanne yashigo, yayinda kubra tabiyoshi abaya da sauri tana masa magana cikin harshen France, dagashi sai gajeren wando, gashi atsaye babu wata k'ibar arzik'i ko k'irar cikakkun maza, daka gansa  cocaine tagama ragad'eshi.....
    Tunanin Aysha yatsaya lokacin da kubra ke fad'in please mana my man........sauran maganganun su Aysha basaji, Dan itama besi batajin France d'in, daga turanci sai yarenta saikuma Hausa d'ai-d'ai, to aysharma dai daga Hausa babu dad'i babu k'ari, aturancin dai takan tsinci k'ananun kalmomi.
               Da k'yar kubra tasakashi yafita, sannan tacema su Aysha su sakama d'akin key.
     Aysha takalli besi ido tab da hawaye, anty misuke nufi?.
    Shiru besi tayi Dan bata fahimci maganar ayshaba.
   Saidai Aysha tad'an jagula turancinta, shima awajensu Ummunoor take d'an tsinta.
   Sannan besi tagane, (indai mutum najin turanci, ko ayaya aka jagula masa zai d'an fahimta).
      Cikin gur6a tacciyar hausar besi tace sholy baki gane ba?, aii tunda muka sauka a airport yake fad'ama Anty kubra waimu kayanashine Dan kinmasa, yanason young irinki.
   Shine tace masa a'a banshiba.
   Todaganan suka koma magana da France, nikum banajin language d'in France.
    Shiru Aysha tayi tana had'a maganganun besi amizani, amma kokad'an takasa musu fashin bak'i saboda k'arancin shekarunta, dakuma kokad'an tunaninta baita6a karkata ga hakanba dukda kasancewarta yarinya mai basira da k'yakyk'yawan tunani.
    Haka sukai barci badan Aysha tanajin dad'in barcinba, sai juye-juye takeyi da tunani kala-kala.
   Amma bahaka baneba ga besi, hankalinta kwance take barcinta, tayi wani rashe-rashe agadon, dagani kasan batasaba samun irinsaba ko kwatankwancinsa.
    Tashi Aysha tayi tashiga toilet d'in dake cikin d'akin, ta d'auro alwala tazo tacire hijjabi a handbag d'inta, tasaka d'ankwalinta ta kabbara sallah batareda tasan inane gabasba, acewarta ko ina aii ALLAH yana nan kuma yana kallon bayinsa. Dama d'azun ahaka tayi sallalolin da ake binta.
        Saida dare yay nisa Aysha tasamu barci awajen datayi sallahr, zuwa sannan kam tasamu sauk'in damuwarta.
   
Tunda safe suka koma airport, ayanzukam taxi suka hau yakaisu, Dan Wanda yad'akkosu jiya yanajin haushin anhanashi hutawa shiyyasa basu samu rakkiyaba agareshi. 
    
Ayanzu kam tafiya awanni 6 ce takaisu inda Aysha take addu'ar ALLAH yasa sunzo kenan, Dan itakama tagaji matuk'a da hawan jirginnan, saboda rashin sabo jikinta sai masifar ciwo yake mata, ga ciwonkai Wanda take k'yautata zaton yunwce, Dan tunda suka baro 9ja bata sake cin wani muhimmin abuba, kai tunma randa sukaje Kano da gwaggo bintu...

__________________________
     *_Nigeria_*

Koda yashiga Office saiyayi k'ok'arin bin umarnin aunty Mamie, lunch box d'in data had'oshi da ita yabud'e, shiryayyen breakfast ne aciki mai nagarta da d'and'ano, koba'a fad'aba yansan wannan girkin aunty mamien sane, yana k'aunar matarnan, Dan komai nata daban yake Dana matan gidan, subasuda damuwa saina aikin gwamnatinsu, basu kula da 'ya'yansuba barema mijinsu, wannan halayyar tasu momy yasakashi sha'awar auren k'aramar yarinya wadda batada zurfi da ak'idar yin aikin gwamnati, halayen Anty Mamie nak'ara masa k'aimi wajen sha'awar hakan.
   Dukda azagayensa Na k'asashen duniya yaga mata dayawa dasuke aikin gwamnati kuma suna bama 'ya'yansu da mazajensu kulawa, to amma masu iya magana kance ruwan daya dakeka shine shine ruwa......
     Kai mutumina duk dad'in abincinne?.
    Firgigit yadawo hayyacinsa, k'aramin tsaki yaja tareda danna laumar dankalinsa abaki, amma idonsa nakan mai maganar.
      Taheer yazauna yana dariya, J! wai dad'in abincine haka?.
    Saida ya had'iye nabakinsa sannan yabashi amsa da kaid'inne d'an iska aii, yanzu zaka katsemin jin dad'ina, kuma ma aii aikawa nayi akiraminkai amatsayin oganka ba abokiba.
    Wata dariya Taheer ya tuntsure da ita, yace to sorry sir, bara mugama cin abincin saika koma serious, Dan yanzun kana komawa amatsayin Oga abincinnan da k'amshinsa yacikan hanci haramiyata, dama nafito gida ban karyaba.
    Harararsa Ya khaleel yayi tareda fad'in tuzurum banza kawai, ALLAH yakamata Ummi Tanaka aure kodan iskancin daka koya.
     Oh nawa tuzurancinne ya to she maka idanu kawai? kai baka duba yawan shekarunka? ALLAH ka k'ara wasu shekaru anan gaba matarka tsoho zata aura, taheer yay maganar yana danna laumar dankali abakinsa.
       Duka ya khaleel yakai masa, amma saiya kauce. Yace, "kai mara mutunci barmin office".
     Hhhh ALLAH babu inda zanje sai tumbina yacika Malam.
    Kwafa ya khaleel yayi, yad'auki cup d'in tea yana sha da Harar taheer.
    Oho kayita hararata har abusa k'aho Dan ALLAH, abincinedai babu fashi sainacishi, tunda ba matarka ta girkaba momyce.
    Dariya ya khaleel yayi yace aiba momyn baceba yaro.
   To waye?.
   Aunty Mamie ce.
Kai ammafa ta iya girki, wannan weekend d'in dolene nashigo gidannan gaisuwa.
      Shege gaisuwar kwad'ayiba.
   Dariya kawai taheer yayi yana fad'in komadai tamiye lada zan samu aii.

Bayan yakammala cin abincin yagyara wajen, daga nan ya khaleel yaci serious, fuska a tamke Yakoma yima taheer magana.
    Shima taheer d'in ya zama seriously saboda afagen aiki suke yanzu, ya khaleel amatsayin Oga yake ba abokiba a halin yanzun.
    Bayan sungama tattaunawa suka mik'e domin zuwa Inda aka rufe Oga David..............🖊

CIKI DA GASKIYA......!!Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin