86

4.7K 310 2
                                    

86

Dole likitoci suka rufu kan hajia babba, dukda ba'a bama wani criminal kulawa kamar haka, saidai inhar suna buk'atar wasu bayanai awajensa, amma darajar khaleel Taheer yace abama hajia babba kulawa, Dan lamarin yawuce k'aramin Abu, Amman jini taketa zazzagawa. Innah jummai sai kuka takeyi. Kusan awanni biyu likitoci natareda momy, bayan wasu 'yan mintuna saigasu sun fito, kowa yana yarce gumi.
     Sai hura hanci sukeyi.
   Taheerne ya tambayesu abinda ke faruwa?.
    Dr Abraham yace sir, akwai matsala, zuciyar matarnan ce tabuga gaskiya, shine dalilin aman jinin datakeyi, saidai munsami nasarar ceto rayuwarta, yanzu hakama tana barci, maganar gaskiya kuma, bamuda tabbacin tashinta normal.
   
    "Miyafaru da itane?".
         " uhm, inagafa tasamu paralysis, 6arinta Na dama munga duk jijiyoyin sun saki".
    " Ya salam!". 'Taheer yafad'a yana shafa kansa da huro iska abakinsa".
       Gaba Dr Abraham yayi abinsa.

Nidai bilynku nace magana ta girma😱.

_________________________________

        Tunda khaleel yashiga office saiya kulle kansa, inda kujeru suke agefen office d'in yaje ya kwanta, Dan anhad'a wajenne tamkar falo.
      Idonsa alumshe suke, amma hawaye Na zurara.

   Yabani tausayi ainun, domin bansan mike k'ona zuciyarsa hakaba harta kaisa ga yawan kuka.😢

     Haka yayta zama cikin office d'in, saidai yatashi daga nan Yakoma nan, saikuma sallan data zame masa tilas, komin knocking d'in da akamasa k'in bud'ewa yakeyi, su Taheer basusan yana nanaba, duk zatonsu yatafi gida.
        
___________________

       Hankalin Aysha yafara tashi, ganin har 10 Na dare babu koda alamun ya khaleel, takira wayarsa yafi sau ashirin yak'i d'agawa, daga k'arshema idan takira saitaji switch up, duk motsinta nakan idon Anty Mamie ne, Dan tunda suka dawo ayshan bata koma 6angarensu ba, tana nan cikin gida, lokacin dazatayi barcine tadawo d'ankin Anty Mamie ta kwanta, ganin kuma bai dawoba tayi zamanta tana jiransa.
         Anty Mamie ta ajiye bowl d'in hannunta a saman dirowar gefen gadon, ta kalli Aysha dake kwance a gadon rik'eda waya tana hawaye, girgiza kanta tayi, sannan tace, "Aysha miyake faruwane?".
        Kokad'an Aysha batasan Anty Mamie tashigo d'akinba, da sauri tad'ago ido tana kallonta, saikuma tatashi zaune, komawa tayi jikin Anty Mamie takuma fashewa da kuka, cikin kukan tace " Mamie ya khaleel haryanzu bai dawoba, nakira wayarsa yafi sau ashirin yak'i ya d'auka, daga k'arshema wayan switch up".
         Ajiyar zuciya Anty Mamie ta sauke, ita kanta dukkan hankalinta Na kansa tun d'azun, daurewa kawai takeyi, lallashin Aysha tashigayi, da kwantar mata da hankali, saida taga Ayshan ta tsagaita da kukan sannan tad'akko bowl d'in data ajiye tamik'ama Aysha, fruit ne datace zatasha d'azun, saikuma tayi barci.
    Kar6a ayshan tayi Tanama Anty mamaie godiya.
        Shiru sukayi suduka, Aysha nashan fruit amma hankalinta nakan khaleel, kad'an-kad'an saita kalli agogo, saikuma gwada number sa takeyi.
     Anty Mamie dai tayi shiru, tausayin Aysha da k'aunarta nakuma ratsa zuciyarta da ruhinta. ganin har 11:30pm Anty Mamie tad'auka waya takira Sultan.
          Shi harma ya kwanta yaji kiran wayar, matarsa tamik'o masa wayan yakar6a yana fad'in waye a wannan lokacin?....
     Ganin Anty Mamie yasakashi mik'ewa zaune da Sauri, bai d'aga wayarba ya d'auki jallabiya yasaka yafito da sauri.
            Aysha data gama shan fruit tamik'e tashiga toilet.
     Anty Mamie tabita da kallo, har ranta tana k'aunar yarinyar, tun a ranarda tafara ganinta da gwaggo bintu tazo da'ita, Ashe Aysha alkairice acikin rayuwarta, shiyyasa tana kallonta gabanta yafad'i.......
     Shigowar ya sultan a hanzarce ya katsema Anty Mamie tunaninta, tad'ago ido tana kallon yanda yashigo d'akin a birkice.
     Shima turus yayi yana kallon Anty Mamie, soyake yagamike damuntane?.
     Fahimtar hakan da Anty Mamie tayi yasakata fad'in "kwantar da hankalinka, yayankune bai dawo gidaba har yanzun, kuma anata kiran wayarsa yak'i d'auka, daga bayama saiya kashe wayar, to munata tunanin ko lafiya? Gashi matarsa dukta tayar da hankalinta, nikaina hankalina a tashe yake wlhy".
            " Kina nufin bai dawoba har yanzun Anty Mamie? to kodai aikine yamasa yawa a office?".
          .....bana tunanin haka, sultan, kasan zuciyar babana, kuma hankalinsa atashe yake yanzun, nafi tunanin badai lafiyaba gaskiya".
         ''Bara muga nakira Adams naji".
       Wayar Adams sultan yakira, ko gaisawa basuyiba yace, ''Adams ya khaleel fa?".
           Cikin muryar barci Adams yace, "bayana gidaba ya sultan? nazata tare kuka tafi d'azu da safe aii?".
        " A'a, kasan yama rigamu barin hall d'in".
     Babu shiri Adams ya janye Amal dake jikinsa tana barci yatashi zaune."
      "Ya sultan kana nufin baya gida?, barato naje office na duba, amma idan har Oga ba aikine dashiba bayakai wannan time d'in a office gaskiya."
       "OK nima ganinan zanzo, muhad'u a can, dukda nasan bazasu barni na shigaba".
      " A'a kajirani amota idan kaje, idankuma narigaka zuwa shikenan".
     "OK".
   Bayan ya Yanke wayar ya kalli Anty Mamie da Aysha dake tsaye tafito daga toilet, taji dukkan abinda yafaru, wannan yasakata cigaba da zubar da kwallah, tana addu'ar ALLAH ya tsare mata mijinta aduk inda yake.
       "Anty Mamie bara naje office Na duba, zamu had'uda Adams a can, Dan bazasu barni nashigaba idan nikad'aine".
        " hakan yayi, amma kira mujahedeen kuje tare, Dan dare yayi, har 12 takusa".
         "Anty Mamie da'an barsa, k'ilama yayi barci yanzu, zan iya tafiya nikad'ai babu damuwa".
         "Shikenan, amma dai daka duba ko Muslim ne kuntafi tare".
      "to bara Na duba idan baiyi barciba, saimun dawo".
        Addu'a Anty Mamie tamasa yafita yana amsawa, ta maido kallonta ga Aysha da har yanzu take a tsaye.
         " k'araso kiyi sallan kinji Aysha, insha ALLAH yana nan lfy, ki kwantar da hankalinki".
     Jin jina kai Aysha tayi, tak'araso tad'auki hijjab ta kabbara sallar isha'i dabatayiba tana barci.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now