63

4.3K 310 1
                                    

63

         Ya khaleel yana fita suka had'u da Adams, Adams yabud'e masa baya da sauri, dakatar dashi yayi. Yabud'e gaban motar yazauna, Adams yadawo mazaunin driver yaja motar sukabar anguwar, suna tafiya sunad'an tattaunawa akan aikin dazasuje, har suka iso wani katafaren club
         Tun a k'ofar club d'in suka fara gamo da 'yan mata da samari, duk cikin shigar rashin mutunci, saika rantse a turai suke ba 9ja ba, kuma harda cikakkun 'ya'yan hausawa awajen😢.
        Duk da aikin ya khaleel yasha kaishi irin wad'annan wajajen, harma da inda yafishi fitsararru, Hakan bai hanashi jan tagwayen tsakiba, da Neman kariya wajen ubangiji gudun fad'awa tarkon shaid'an, babu abinda zai hana sha'awa bijiro maka a irin wad'annan wajajen inhar Kannada lafiya, dakuma raunin imani.
      Shikansa Adams tsigar jikinsa sai tashi takeyi, addu'a kawai yakeyi ALLAH yasa sugama abinda yakawosu  dawuri subar wajen kafin shaid'an yayi tasiri akansa.
         Jikin beer parlor suka k'arasa, irin kantarnan da ake zuba kayan shaye-shaye aciki, sai a gewaye inda mutane kan tsaya su jingina.
        Ya khaleel ya zauna a kujerar nan maid'an tsayi tajikin table d'in. Shima Adams zaman yayi.
        Wata budurwa dake tsaye jingine da table d'in sai hambud'ar giya takeyi da'aka zuba cikin irin k'ananun glass cups d'innan, ta shanye Na hannunta idonta akan ya khaleel. Wanda shima satar kallonta yakeyi da takaici.
       "Hii", 'tafad'a tana d'aga masa hannu🙋🏻‍♀'.
        d'an murmushin yak'e😁 yayi shima yace mata, "hii".
        Saves ta kallah tamasa sigina da ido, da nuna yatsun hannunta uku.
     Kansa ya jinjina mata, sannan yajuya ya d'akko kwalaben guilder guda uku acikin Kantar glass d'in wajen, ya goge kofuna biyu yazuba k'ank'ara yakawo gabansu ya khaleel dake kallon Shiga da fitar mutane cikin kwarewar aiki.
      Ajiye kofunan dayayi yasaka ya khaleel juyowa ya kalleshi, Save's yanuna masa budurwarnan data saka aka kawo musu, ta kannema ya khaleel ido d'aya tareda lashe la66anta da harshe.
     Guntun murmushi yasaki tareda kauda kansa, matsowa tayi kusadashi ta d'ora hannayenta saman cinyarsa, a'uziyya yayi azuciyarsa cikin dabara yaxame jikinsa, rankwafowa yayi saitin kunnrnta yace, " kozamu zaunane?".
         Jajayen idanunta tad'ago ta kalleshi, cikin salon barikanci ta kanne masa ido d'aya tana mayaudarin murmushi.
     Awasukujeru sukaje suka zauna.
     Giyan datayi Order aka biyosu da ita wajen, har saves yajuya zai koma yamasa sigina, siiii!! Jimana my man.
       Saves yadawo yana sauraren ya khaleel.
     "Kawo mana sorpt drinks".
      "O, my friend!, why?  bazakasha wannanba danasaka akawo?".
        Guntun murmushi yayi, yasaka yatsansa yana Sosa girarsa, cikin basarwa yace, ''no, banashan giya".
        " why?".
Tasake tambayarsa.
        Bakinsa yad'an ta6e tareda d'age kafad'a yace, "haka kawai".🤷🏻‍♂
       " woow, amma ka birgeni, rayuwarka abin sha'awa, handsome irinka baya shaye-shaye, akwai k'ayatarwa a tsarinka".
     Adams yay guntun dariya, yana fad'in ''kad'anma kenan daga abubuwan dake tattare dashi".
        Jinjina tama  khaleel dukda bata fahimci maganar Adams d'inba sosai, saboda ba bahaushiya baceba, tamik'ama ya khaleel hannu alamun su gaisa "am blessing".
         Amma saiya basar bai bataba, saiya wayance dafad'in, "Nice name, Ibraheem Abdallah, ko kice j!".
       " woow komai naka daban Dana kowa".
      Murmushi yasake yi, amma Baice komaiba.
        Tayima saves alamun yazo, da Sauri saigashi, giya takuma buk'ata kwalba biyu, amma sai ya khaleel ya dakatar da saves d'in akan karya kawo, ya kalleta cikin nuna kulawa yace, "please ki huta mana".
         Batace komaiba sai guntuwar dariya Datayi.
            Suduka kowa ya maida hankalinsa wajen waige-waige, da Alama kowannensu da abinda yake nema, shiru nawani lokaci sannan ya khaleel ya jefeta da tambayar data sakata maido hankalinta Kansa. Ahankali hira tacigaba da gudana atsakaninsu, yayinda Rabin hankalin ya khaleel yake wajen nazarin jama'ar club d'in, shikam Adams gaba d'aya yamaida hankalinsa ga mutane.
     Itama ya khaleel yalura baduk hankalinta ke kansaba, kamar kuwa an tsikareta saiyaga tamik'e,
    da Sauri yace, " lafiya kuwa".
     Cikin rabuwar hankalinta biyu tace, "please 2minutes".
    Tana d'aga k'afa zata bar wajen wani cart yafad'o daga aljihun wandonta.
    Kiranta ya khaleel yashigayi danta d'auka, amma INA bata jishiba ma, ganin harta fice ya sunkuya ya d'auka, bin bayanta yayi da Sauri domin kaimata batareda ya dubaba.
       Waige-waige yafara a waje amma bai gantaba,
     🤦🏻‍♂Omg saikace aljana, haryayi shirin juyawa ciki saiya  duba cart d'in, yazaro ido waje dan ganin kowacece ita ajikin ID cart d'in.
     A hanzarce yafara bincikenta cikin mutanen dake tsaye a wajen, cikin dabara yake dubata, cikin sa'a kuwa yasamota tsakanin wasu motoci tana kici-kicin kama wani guy, daka ganta kasan tasamu kyakykyawan training, saidai giyar datasha ta haddasama k'arfinta rauni, duk da shima guy d'in abuge yake, amma bai kaita shawuwaba, hasalima shi kusan normal yake, giyan bata fara tasiri ajikinsaba.
       K'arasowa yayi wajen da Sauri, da taimakonsa suka kamashi, cikin motarta suka sakashi suka kulle.
     Sai a sannan ta kalli ya khaleel, yatsun hannunta biyu ta d'aga masa tace, "thanks".             "amma miyasa ka taimakeni? Bayan kuma bakasan alak'ata da guy d'inba, kasani ko zan cutar dashine?".
        Hannunsa duk biyu yatura cikin aljihun wandonsa, tareda gyara tsayuwa yasaki guntun murmushi, ID cart d'inta yaciro daga aljihunsa ya mik'a mata.
     Cikin mamaki ta kar6a, saikuma tafara laluben aljihun wandonta itama, tabbas ID cart d'intane, yaushe yafad'i bata saniba, tad'ago danufin tambayarsa saiya nuna mata nasa ID cart d'in, d'an zabura tayi taja baya, saikuma tak'ame tareda salute d'insa.
    Kansa ya jinjina mata.
   Tamatso kusadashi tace, " thanks you so much sir, amma kana neman wanine? Dan bakayi kama damasu zuwa club ba".
     Saida yad'an wawwaiga yaga babu mai kallonsu, kowa harkar gabansa yakeyi sannan yace mukoma ciki, amma yaza'ayi da sannan Na mortar?".
        "OK INA zuwa, tayi maganar tana zaro k'aramar wayarta acikin bra d'inta, baidamuba Dan yasan dun cikin salon aikine,, su jami'an tsaro sunada salo iri-iri saboda tsaro, kira tayi, babu dad'ewa saiga mutane hud'u, tamusu bayani akan ya khaleel.
    Nan take suka fara salute nashi Dan d'ammararsa tafi tasu.
    Key d'in motarta ta mik'a musu, tace suje dashi, amma d'aya ya jirata, zata koma ciki ta k'arasa wani aiki, duk suka amsa mata da girmamawa tareda salute nata, suka cika umarni.
     Itada ya khaleel kuma suka koma cikin club d'in, kujerar dasuka tashi suka koma, zaune suka tadda Adams wata budurwa a cinyarsa, sai shafashi takeyi, shikuma yana lumshe idanu tareda maida murtani, da d'an k'arfi ya khaleel ya buga table d'in cikin Jan tsaki.
     Da sauri Adams yadawo hayyacinsa, yature yarinyar daga jikinsa yana soshe-soshen jin kunya.
     Itakam blessing dariya tayi kawai.
      Ya khaleel baisake cewa komaiba yacigaba da dube-dubensa, can kuwa idonsa yafad'a kan Moxies dake zaune kan wata kushin, haggu da damarsa 'yanmata biyune suna rungume ajikinsa, kowacce cikin shigar rashin mutunci, gabansu kwalaben giyane birjit. Sai garadan samari majiya k'arfi dake tsaitsaye alamun yaransane, Duk saida ya khaleel yagama nazarinsu kaf.
    Sannan ya waigo da kallonsa wajensu Adams, da har yanzun kunya bata sakeshiba.
     Murya k'asa-k'asa yace, "ga Moxies can".
    daga Adams har blessing kallonsa sukayi, har Adams zai tashi blessing ta dakatar dashi, ta kalli ya khaleel dashima ita yake kallo, ''sir! Bara Na gwada sa'ata.
     Jinjina mata kai ya khaleel yayi.
      Tana barin wajen yamaida kallonsa ga Adams, ka sanarma su Samuel su taho, naga alamun Moxies bazai kamu cikin sauk'iba, dolene saimun d'an tada jini".
        " OK sir!".
Can ya khaleel ya hango blessing kan cinyar Moxies suna kissing d'in juna, (sosai ya khaleel ya jinjina hatsabibancin blessing)  kusan mintuna 10 yaga Moxies ya d'auki blessing zuwa wani d'aki, juyowa tayi ta kalli ya khaleel tamasa sigina da idanu, jinjina mata kai yayi cikin lumshe ido, daidai da isowar su Samuel wajen.
       Ya khaleel yamik'e, "Adams kuji da yaransa, INA zuwa.
     Adams ya amsa da OK sir.
         Saidai su ya khaleel basusan suna shuka bane a idon makwarwa, Duk abinda ke faruwa idon yaran Moxies biyu yana Kansu, duk wani motsinsu ya khaleel akan idonsune, yana tashi sukabi bayansa, bayan sun sanarma sauran 'yan uwansu abinda ke faruwa.
       Yakusa d'akinda Moxies yashiga da blessing yajiyo k'arar harbi, yaran Moxies sun kaima su Adams hari, dandanan club d'in ya hargitse, aka fara gudun tsira, yayinda sukuma suke musayar wuta, kowa takansa yakeyi.
      Ya khaleel zai Shiga d'akin  wad'anda suka biyo bayanshi suma suka fara harbinsa, kaucewa yakeyi cikin kwarewar samun cikakken training, d'akin ya k'arasa da hanzari bayan ya harbi d'aya kafad'a, jin k'arar harbi da bud'e k'ofa moxies yatsaya da romancyn d'in blessing.
       Da sauri yad'aga hannunsa sama saboda nunasan da ya khaleel yayi da gun, juyawa yayi yana kallon blessing dake dariya, gira ta d'aga masa tareda kama hannayensa tamaida baya tasaka hand cop, sorry dear you are onder arrest🤨 ".
       Bak'in ciki tamkar zai kashe Moxies, wai anyi amfani da mace ankamashi, tsawon shekaru yana harkokinsa, ya gagari mazanma, amma yau da mace aka masa tarko.
         Suna fitowa da harbi suka fara cin karo, ya khaleel yay saurin komawa baya, yala6e jikin bango, saida yad'an lek'a sannan yay harbi, Yakuma komawa baya da Sauri yana rimtse ido, wancanma harbin yayo Yakoma ya la6e, haka sukaita Harbin juna har bullet d'in wancan yak'are. Amma babu Wanda aka sama.
     Ya khaleel ya fito, Ashe wancan Yakuma samun gun, yana fitowa yaron Moxies yafara ruwan harbi, wata sufa ya khaleel yayi akwance harya k'arasa Inda wancan yake ya tad'eshi da k'afa ya fad'i.
      Yay saurin harbinsa a cinya, shikuma yasaki k'ara.
        Blessing  tayi masa wani duka ya durk'ushe k'asa.
      Cikin club d'in suka fito, ko INA a harmutse, kwalaben   da kofuna duksun fashe, kowane table da kujera akwai Inda sukayi, babu kowa sai wad'anda suka samu raunikane kawai kwance, suma Duk yaran Moxies ne, sai kad'an da tsautsayi ya afkamawa.
     Kwashesu aketayi ana kaiwa mota.
    Ya khaleel yabi club d'in da kallo yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa.
     Ahankali saves dake 6oye yad'an lek'o da Kansa, yana ganin su ya khaleel Yakoma ya durk'ushe, dariya abin yabama khaleel amma baiyiba, yak'arasa Inda yake yasaka hannu ya jawosa, jikinsa sai 6ari yakeyi, ya had'e hannayensa alamar rok'o.
     Sakinsa khaleel yayi tareda jinjina masa👍🏻, yace, ''kayi k'ok'ari, thanks daka bamu had'inkai".
       Sai yanzu saves yad'anji sanyi, ya jinjinama khaleel kai, haryanzu dai a d'arare yake, dukda ya amince babu abinda zasu masa, Dan shine yabada dukkan bayanai akan Moxies,  kwana uku kenan dasuka wuce ya khaleel yazo club d'in yay bincike.

     Bayan sun gama kwashesu suka fice, lokacin har garin yafara haske, harma an idar da sallar asuba.
    Kai tsaye setesion d'insu suka wuce dasu, duk aka zubasu inda yadace.
    Ma'aikatan daba nan suke kwanaba harsun fara isowa.
    Ya khaleel ya kalli agogonsa yana fad'in bara naje gida nayi wanka nai sallah asuba, bazan iya sallah da kayan nanba.
   Adams ya yunk'uro zaibi su rakashi kamar yanda suka saba, ya dakatar dashi.
    kai Adams idan akace kabini saika bini?, koka manta da nauyin dake kanmu wanda yafi komai muhimmanci, kaje tunda akwai mota hannunka, nima dagani sai ema zamu tafi, daya ajiyeni zaitafi gida. Idan nagama kwaje ku d'akkoni.
   Baijira cewar  adams d'inba yashiga mota da ema ya bud'e masa.
    Yayinda adams ke binsa da kallo, wata k'aunar ogan nasa dakuma ganin kimarsa na k'aruwa a idonsa, tunda yake dashi baita6a ganinsa yana aikata wani abun asha ba arayuwarsa, mutumne mai tsananin rik'o da addininsa, baya wasa da dokar ALLAH, inhar kaga sallah takwacema ya khaleel to tabbas dolene, babu yanda zaiyine, kodai jikinsa babu tsarkin gabatar da sallar, kokuma bai yarda da tsarkin wajen daya tsinci kansaba.
   Ya ALLAH kabani ikon yin koyi da k'yawawan halin bawan ALLAHn nan, ALLAH ka kare manashi dadukkan wani sharri.

Nace, "amin Adams".
   

**********

     Aysha Na tsaka da gyaran gidan, zeenatu Na tayata ya khaleel yashigo da sallama, har k'asa zeenatu ta tsugunna ta gaisheshi, ya amsa yana nufar d'akinsa, Aysha ma sannu da zuwa tamasa tana ajiye moper d'in hannunta tabi bayansa, zeenatu kuma tacigaba da aikin.

        Ad'aki ta iskeshi yana 6alle ma6allin rigarsa, warin giya da Aysha taji yanayi bak'aramin tada hankalinta yayiba, cikin kare hancinta da hannunta tace, " sadauki warin giyafa kakeyi? Dama kana shan giya?, atsorace take maganar, dan muryarta har rawa takeyi".
       Amatuk'ar d'aurewar fuska yajuyo yana kallonta, yazame rigar daga jikinsa yana fad'in bakisan inashan giyaba? Barama Na tabbatar miki!!", cikin tsawa yayi maganar.
    Har saida Aysha ta zabura baya.
    Shikuma yatako inda take, ya matseta ajikin bango, da hannu d'aya ya damk'o ha6arta yamatse da k'arfin tsiya, d'ayan hannun kuma yadafe bango.
      Saboda matsotan dayayi saitaji warin giyar Na hawa kanta, kamar zatayi amai, ga jikinta sai rawa yakeyi saboda yanda yazo gabanta a fusace, bakinsa yad'ora kan nata ya had'e da k'arfi saboda mugunta😏..............✍








💓💓💓💓💓😍😍😍😍😍😍😍😍❤❤❤❤❤❤❤❤❤

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now