100🤣😜

3K 127 11
                                    

100

MIYE MANUFAR BILYN ABDUL A LABARIN CIKI DA GASKIYA?

_Tambaya mai muhimmanci, wadda kafin kowa yamin, niyakamata nayima kaina._

_ba burina idan kun karanta labarin *CIKI DA GASKIYA* kubarsa ananba, a'a, burina kud'auki muhimman abubuwan ciki Ku amfana dasu, labarin *ciki da gaskiya* dunk'ulallen labarine, amma mai tafiya da harshen damo. labarine dayazo muku da abubuwa da dama._

      Bara nafara da jarumin matashi Ibrahim Abdallah, Wanda yataka rawar gani ajigon labarin.

_Ibraheem Abdallah matashin saurayine dakowane matashi yakamata yayi koyi da tsarinsa dagashi har abokansa, Taheer, Joseph, youseef, harma da Adams._
      _bashida tsoro ko kad'an, sannan da zuciya d'aya yake aiki, ko sigari wannan bayasha, baya neman mata, akullum kuma yak'i yake da k'arya, gashi da zuciyar taimakon nak'asa dashi, yana kuma girmama nasama dashi, a fannin familie nasa da iyayensa kowa yabonsa yakeyi saboda k'yawawan halayensa._
     
Shin abin tambaya anan, duk mi yakawo wannan?.

_kai tsaye zan iya nuna muku yarik'e martabarsa ta matashine, wadda ayanzu hakan yayi k'aranci ga matasanmu, kullum idonsu nakan 'yammata, burin yin kud'i kota halin k'ak'a, d'aukar shaye-shaye amatsayin wayewa, raina nagaba dasu saboda sunaji da tashen balagar samartaka, rashin yin biyayya ga iyaye saboda jahiltar wayewar zamani, dakaga kakai tsawo shikenan iyayenka sunzama abokan wasanka, fifita ilimin boko fiyeda Na addini._
      _Dan ALLAH tayaya za'a samu nasarori arayuwa? Tayaya zaku iya zama Ibrahim Abdallah j?, k'alilannefa acikinku masu irin wannan k'yak'yk'yawan tunanin, k'arancinsu yasaka kowa ganin tamkarma babusu._
     _Dan Allah Matasanmu Ku gyara please, kune ginshik'in kowacce al'umma, daku duniya take alfahari, kudaina shaye-shaye, domin kullum ruguzaku yakeyi, yaruguza k'ashenmu da al'ummarmu, kudaina zina, kullum durk'usar daku takeyi tana k'ask'antar daku, kudaina barandar siyasa, inbahakaba kullum a 'yan Turin mota zaku k'are, Ku turasu sukoma kan mulki suna zaginku dafad'a muku kune lalatattun matasa, dole kuma kuringa amsawa, Dan bakuda za6in daya wuce hakan, rayuwar j abin birgewa daban sha'awa, amma miyasa yazama haka?, saida yakasance mai yawan hak'uri da gaskiya, yature Duk wani abun jin dad'i da samarin yanzun suke d'aukarsa amatsayin ado wa rayuwarsu, sannan yazama mai yawan nasara. Dan Girman ALLAH kufarka daga nannauyan barcin daya d'aukeku, Ku daidaita rayuwarku, kunutsu kuyi karatu, kudaina karatu domin burin aiki, karatu wata katangace agareku, idan kun mammala kobabu aiki Ku kama Sana'a, kubar girmankai, k'ila wannan sa'ar itace mafi alkairi arayuwarku, amma kullum idonku nakan k'aton offices, why?._
      _Dan ALLAH kucanja kodan kuma Ku amfana, kuzama jarumai irin Ibrahim Abdallah, bafa wai jaruman littafi sunfuku wani abubane, suma mutanene tamkarku,  muna kafa musaline dasu domin kuma kuyi koyi da halayensu, hartakai mun rubutaku duniya takarantai labarinku._

   ALLAH yasa mudace.

_Lamarin Aysha abin birgewa da k'ayatarwa ga kowacce mace, matashiya kokuma babbar mace. anrabata da iyayenta tana 'Yar k'aramarta, ankaita wata k'asa mai nisa, batada kowa awajen sai ALLAH daya halicceta, abin birgewa dukda k'ank'antarta bata mance dafad'ama ALLAH kukantaba, haka tadage dare da rana wajen kai lamarinta ga ALLAH, Wanda shikad'aine zai iya kawoma rayuwarta mafita, duk kuma Wanda yarok'i ubangiji zai amsa masa, Aysha tarok'a kuma ya amsa mata, datasamu damar k'aratu batayi wasa da damarba tanutsu tayi, cikin wad'anda ba k'abilarsu d'ayabama, amma bataji shayi ko burin kasancewar gazawarta ba agaba-gaba ba wajen nuna kwazonta da jajircewa_.
       _sannan kuma taginu akan wani k'yak'k'yawan buri nason ku6tar damata dayawa dasuka tsinci Kansu cikin irin rayuwar datake, walau dasaninsu, koda tirsasawar wasunsu, ahakan hartasamu ceto rayuwar meerah, wadda tafidda rai dagama shiriya baki d'aya, alokacin kuma data samu damar k'arfafa mijinta saitazama mai k'arfafashin, da nuna fushinta wajen son yataimaki matan wannan al'ummar damuka kasance cikin gararin rayuwa, bayan addininmu yamana gata, amma wasu tsiraru acikinmu suke nuna  zalinci da k'arfa-k'arfa akan hakan._
    _yakamata 'yan uwana mata muyi koyi da Aysha, muzama masu kishin junanmu dasanin darajar juna, muzama masu k'arfafa zukatanmu wajan fallasa asirin wasu 'yan jari hujja dake wargaza rayuwarmu komin kusancinmu dasu kuwa, da wannan jarumtar Aysha tasamu damar fallasa asirin su momy har aka d'auki hukunci akansu, datayi shiru tsoro yahanata haka rayuwar zatayita tafiya da walagigi da sauran mata. Kuma wlhy abinda su momyn nan suke aikatawa agaske yana faruwane yanzun, saidai shugabanninmu sunyi burus da lamarin😭._
     Mata muzama Aysha, koda k'ar6ama rayuwarku 'yancinta🤷🏽‍♀.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now