68

4.3K 312 3
                                    

68

        "Sakina kinsan miyasa aka d'akkoki aka ajiye anan harna tsawon kwanaki hud'u?".
        "a'a yalla6ai".
    "Inason wasu bayanai awajenkine, miye alak'arki da gidan Alhaji mustapha Adamawa?".
       "ni mai aikice agidan yalla6ai".
      "Aikinmi kikeyi?".
  " sharan d'akunan masu gidan, saikuma falo dadai sauransu".
       "Uhm, atunanina Wanda ka yarda dashi kake sakarwa shiga lungu da sak'o Na gidanka, danya gudanar da irin aikinki, da alama kema masu gidan sun amince dake kenan?".
        Cikin in ina tace, "ha...hakane yalla6ai, amma nima duk sanda zanyi wannan aikin, musamman Na bedrooms nasu saiwani d'an gidan yatsaya akaina harna gama, sannan mu fito tare".
      Shiru ya khaleel yayi yana kallonta, yakoma jikin kujera yana lilawa ahankali, hannunsa rik'eda bindiga yana sosata akan kwantaccen sajensa zuwa baki.
        Sakina dai atsorace take sosai, tunda take bata ta6a ganin bindiga ido da ido hakaba, saidai ta 'yan sanda, itama daga nesane.
    Kusan mintuna biyu baisake cewa komaiba, sai zuwa can yajeho mata tambayar data gama rikita dukkan illahirin halittar jikinta.
        "Hakan yana nufin basu yarda dakeba kenan kema? Dukda tsawon shekaru Biyar dakika d'auka kina aiki agidan? Shin wacecema talatuwa agidan?".
    Tsoro, razana, kad'awar ciki data zuciya duk suka riski sakina lokaci d'aya, takasa cewa komai, sai zufa dake keto mata takowacce ga6ar jikinta.
          Cikin daka tsawa yace, "nace wacece talatuwa agidan dakike aiki?!!".
           "yalla6ai fad'ata tamkar salwantar rayuwatane narantse maka, sannan bansan miyasa basu yarda dani d'inba".
      Wani murmushin k'asaita yayi, tareda fad'in ''dak'yau yarinya, anzo wajen".
        "Ki fad'amin, kokuma kafin ki koma wajensu su kasheki, ni zansaka alburushin bindigata acikin kanki, saidai akai musu gawarki su tambayeta".
          Hawaye masu zafi suka fara zarya akumatun sakina, tace, " yalla6ai zan fad'a maka, amma Dan ALLAH karufamin asiri karkace nina fad'a".
      Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanu, amma baice komaiba.
    Tace, "shekaruna kusan biyar ina aiki agidan, lokacin da'aka kawoni banwuci 14 ba, kuma talatuwace ta d'akkoni daga k'auyenmu Na boza a fika Local Government, jihar yobe, mahaifina da hannunsa yabadani wajenta, bayan tabashi mak'udan kud'ad'e, ina kuka mahaifiyata Na kuka aka taho dani. Koda aka kawoni Abuja wani gida aka kaini, agidan akwai 'yan mata dayawa, k'anana da manya, kuma kowanne irin yare dake Nigerian zaka samu, hardama 'yan Niger dawasu k'asashe makwaftan Nigeria, banfahimci abinda yatara wad'annan mata agidanba aka d'akkoni aka dawo dani gidan Alhaji mustapha, nikaina bansan dalilin yin hakanba, amma daga nanne nacigaba da aiki agidan, Alhaji mustapha ba mazauni baneba, shiyyasa gidansa yazama k'ark'ashin mulkin matarsa, dukda dai nakanji masu gidan sukan tattauna akan hajia khaltum tanada kishiya, kuma alhaji mustapha yafi zama a can, yalla6ai satar amsa 1 zan baka, nasan kaid'in kwararrene Dan nakanji firarka awajen yaran gidan, suna yawan yabama kwazonka saboda soyayyar da baby take maka".
     Da Sauri ya khaleel yataso daga jikin kujerar, ''kinga fad'amin wace satar amsace?, bar batun wancan shirmen".
        Sakina ta jinjina kanta tace, " yalla6ai mafi yawancin masu zuwa gidan wajen hajia khaltum, namiji ko mace zaka samesu dawani tambarin hoton tarttu na 🦂kunama a damtsen hannunsu Na haggu, tabbas wannan shine tambarinsu, wannan kawai Na iya fahimta tartare dasu yalla6ai, wlhy iya gaskiyata nafad'a maka, Dan ALLAH karka kasheni, kuma karkace Nina fad'a".

          Kwantar da hankalinki, zansa a maidaki yanda bazasu fahimci komaiba, da sauri yad'auki ☎waya yayi kiran office d'in Mahfouz da Basheer.
    Babu dad'ewa saigasu sunzo kusan atare, saida suka k'ame, tareda salute nashi, sannan ya khaleel yace, "Mahfouz! Amaida yarinyarnan, amma yanda za'a iya fahimtar saceta akayi".
    "OK sir"
"Kibishi kuje, inhar ina buk'atar k'arin bayani zansa akuma d'akkomin ke".
     ''To yalla6ai ngd, tayi maganar tana hawaye, Dan bata fatan akuma kawota wannan wajen".
      Saida aka d'aure idonta kamar yanda aka kawota sannan aka fita da ita.
    Ya khaleel yamaida hankalinsa akan Basheer dake zaune, ''Basheer ina buk'atar hotunan gawar David".
      " OK sir!, bara na kawo, amma akwai Na binciken k'arshe da akayi suna hannun Oga Joseph ".
    Jin jina kai khaleel yayi, yakira Joseph akan yakawo masa file d'in binciken mutuwar David.
      Babu dad'ewa saiga Joseph ya iso, kar6a khaleel yayi yafara bincike, zuwa can yad'auki wani hoto da David ke shinfid'e a table doctors nata aikinsu akan gawar, damtsen 💪🏻hannunsa ya khaleel ya kalla, cikin zare ido yace, "Joseph hoton miye wannan?".
      Kar6ar picture d'in yayi yana kallo, sir! Inhar hasashena yayi dai-dai wannan kunama ce🦂, dukada ba'a gani dak'yau".
       Da sauri ya khaleel yamik'e yana fad'in Joseph inason ganin gawar David yanzunnan.
       " OK sir!, idan ka shirya saimuje".

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now