62

4.5K 308 0
                                    

62

        Babu dad'ewa Aysha tafito daga wankan, simple makeup tayi tasaka wandon jins blue dawata lemon green d'in riga wadda Tamata masifar k'yau, ta gyara kanta ta d'aure, bawai Aysha Nada wani uban gashi baneba, amma daidai gwargwado yanada tsayi.
        Kasancewar ba sallah zatayiba tafito falo, kwanciyarta tayi saman doguwar kujera tana sauraren karatun alkur'anin data saka, kokad'an tunaninta bai kawo ya khaleel yadawo gidanba.
           
     Shima a d'akinsa wanka yashiga, ya d'auro alwala yafito, jikinsa kawai ya goge da k'aramin towel ya zira jallabiya blue black ajikinsa, turare yafesa kad'an sannan yafito zuwa masallaci.
       Ganin Aysha a kwance idonta kuma alumshe saiyayi nufin tsokanarta, cikin sand'a yak'araso kusada inda take, k'afarta datad'an lek'o Yakama babban yatsanta yaja, da sauri yaduk'e bayan kujera.
          Kawai Aysha jitayi an matsa mata yatsan k'afa, aiko tamik'e a firgice tareda kwallah k'ara, sosai ta firgita, ta wawwayga kuma bataga komaiba, hakan yakuma tsoratata, sai tasaka kuka da kiran mama ta shiga uku, anturo abu zai kasheta.
        Yanda take dire-diren k'afafu da kuka tamkar taga dodo ido da idone abin yabama ya khaleel dariya, duk k'ok'arin rik'ewa dayakeyi Baisan dariyar ta kwace masaba.
     Aysha takuma tsorata, saida taji muryarsace sannan tagane shine.
     Yafito daga wajen 6uyarsa yana cigaba da dariya sosai.
    Tunda Aysha take bata ta6a ganin dariyar ya khaleel irin hakaba, saita samu kanta da shagala kallonsa.
     Shikam baimasan tanayiba, yaga mugunta dariya ta tik'eshi, ya zauna kan kujera yana dariya.
     Saida yayi mai isarsa sannan yad'ago yana kallon Aysha wadda ta cuno baki gaba saboda jin haushin dariyar dayake mata.
           "Wai dama haka kike da tsoro? Hhhhhhh, wlhy kinbani dariya, to dakika tashi ina zakije ne?".
        "Cikin shagwa6a Aysha tace, " yoni wlhy nama rikice, narasa INA zan dosa, d'aki ko waje, towai yaushe kadawo ban sanibane?".
          "Kina wankafa nashigo, harnayi wankama, masallaci zanje kawai naganki kwance ido arufe, shine naji sha'awar tsokanarki, kinzata miye to?".
      " yo aljani mana".
            "kinajin karatu wane aljani ya Isa zuwa kusadake, kedai shegen tsorone dake, saikuma tsiwar tsiya fal kanki".
         "Wlhy bazaka ganeba ya khaleel, natsorata wlhy, kaikuma kanatamin dariya, dama haka ka iya dariyar mugunta?".
           Bai bata amsaba yamik'e, ''kinga bara naje massalaci karna lalace anan ashiga sallah".
       Binsa kawai Aysha tayi da kallo tana murmushi dajin dad'in ganin dariyar mijin NATA murd'ad'd'e, dama yana dariya har haka? Oni shatun mama, su ya khaleel an iya mugunta.
               Saina rama aii Nima".
     Lallai yarinya zaki rame dai, naje madallaci".
     To adawo lfy.

Saida akayi sallar isha'i yadawo gidan aysha takawo masa ruwa ya kar6a yana fad'in "thanks", yana gama sha ya ajiye cup d'in yana satar kallon Aysha k'asa-k'asa, kwalliyar tata tamasa k'yau, amma dayake ya khaleel akwai iya shariya, bazaka ta6a zaton yama damu da itaba.
     Danne-danne kawai yakeyi a waya.
     Aysha tace aranta aljanun miskilancin sun motso kenan?......
     Maganarsace takatse tunaninta, tad'ago tana kallonsa, Dan bataji miyaceba sosai.
    "Kin tsareni da idanun kinnan, canayi ki dafamin shayi".
     Kad'an Aysha ta murgud'a Baki, azatonta baya kallonta, Dan haryanzu waya yake dannawa, tanufi kichin tana 'yan k'unk'uni.
     Yana kallom murgud'a bakin data masa, dakuma k'unk'uni datakeyi, saidai bayajin mitake fad'a, ransane ya6aci, "shin mi yarinyarnan ke nufi? Kodan taga Na sake mata ina wasa da ita?", kwafa yayi yacigaba da danna wayarsa.
     Kusan mintuna 10 Aysha takawo masa shayin, tasha jinin jikinta dan ganin fuskarsa cid'in-cid'in ad'aure, duk kuma saitaji babu dad'i, koba komai tana shiga farinciki idan taga ya khaleel Na walwala.
    Kofin tea d'in ta mik'a masa, batareda ya kalletaba ya kar6a, baisake bi ta kantaba, yacigaba da shan tea d'insa yana danna waya.
     Itama Aysha tayi shiru cikin kujera tana kallo, amma duk Rabin hankalinta Na Kansa, sai satar kallonsa takeyi.
      Ahaka hasnah tayi sallama tashigo ta samesu.
    Aysha ce kawai ta amsa mata, amma Oga ko ido baid'ago ya kallesuba.
     Hasna sai Harar Aysha takeyi, yitai tamkar batasan tanayiba, Dan bata gabanta, arantama sai ayyanawa takeyi, yarinriya da uwarki laura zanyi badakeba, danke kinmin kad'an a filin daga.
      Kusada ya khaleel hasnah ta k'arasa, ta rissina tana fad'in "'ya khaleel Momy tace kazo tana kiranka".
       Saida ya6ata mintuna biyu sannan yad'ago ido ya kalleta, "naji to, inazuwa, kinzo kinmin tsaye akai". 'Yak'are maganar da hararta'.
      Fita tayi tana tutura Baki wai ya dizgata gaban Aysha.
     Bai fitaba saida yagama shan shayinsa.
      Fita yayi batareda ya kalli ko inda Aysha takeba.
      Aysha ta ta6e baki cikin hanlin ko inkula, yana fita takira Rufaida da Sadiya a waya, tahad'asu waje d'aya suna hira, dayake shashashune kowacce k'uruciya Na d'ibarta, sai sukaita bama juna labarin first night d'insu.
   

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now