73

4.5K 306 1
                                    

73

           Bai shiga 6angaren Momy ba, kai tsaye 6angarensu yawuce, yad'an watsa ruwa sannan yadawo falo yazauna, komai akashe yake, babu haske Afalon, yana zaune cikin duhune. Sai tunani yakeyi, yarasa yanda zai fassara abubuwan dake tunkaro rayuwarsa, kallon komai yakeyi abaibai, miyasa abubuwa suketa rikid'ar hawainiyane acikin gidansu?, muyasa baita6a kawo tunanin komaiba dangane da wasu abubuwa sai yanzu?.
   Guntun tsaki yaja, yazame ya kwanta a doguwar kujerar, hakai yayta tunane-tunane har kusan 10, ring d'in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yad'auki wayar yana kallon mai kiran, baffah ne, harta katse bai d'agaba, kamar bazai kiraba saikuma yay k'ok'arin dailing d'in number, gamo yayi da miss call d'in mimy har uku, ya furzar da huci, Dan kokad'an baiji kiranba, baikai karshen tunaninsaba kiran baffah yasake shigowa.
       'Dagawa yayi, cikin ladabi yagaida baffah tamkar yana gabansa.
    "Mu'azzama kana inane?".
     ''Ina gida baffah".
  " kazo to ina nemanka, amma yanaji muryarka haka?".
       "Babu komai baffah, barcine yad'an figeni, ganinan zuwa dai".

***********
      Baffah kad'ai ya tarar zaune afalo yana kallom labarai a NTA, harma sunkusa gabawa, zama yayi yagaidashi.
   Baffah ya amsa idonsa akansa, danya hango damuwa tartare da d'an nasa, baidai cemasa komaiba dangane da damuwar tasa, Dan yasan bazai wuce awajen aikibane.
         baffah yafara magana " dama nakirakane akan shawarar damuka yanke nidasu Ammah, saboda kafita tunda safe yau, akan maganar Ameenudden ne, da cikinsu tasleem zance yaza6a, amma sai Ammah takecemin Tasleem tana tareda k'anin Naufal ne, Maleeka kuma yaron Alhaji musa batsari, kuma duk takula mu'amullar tasu tayi k'arfi, wannan yasa na janye batun akansu, saida bazan bashi Hasnah ko husnah ba, saboda mahaifiyarku bazata barsu su zauna lafiyaba, akwai yarinyar Hameesu, k'anin Bilkeesu, Nafisa, tazo bikinnan, Tanama gidannan bata tafiba, kawai mun yanke shawarar maidama Ameenu ita a madadin mufeedah."
         Jin baffah yayi shiru, ya khaleel yagane yagama, zamansa yagyara shima.
    "Baffah shawararku tayi dai-dai, kuma ALLAH yasanya alkairi aciki".
    "To ameen, saikuma batun mufeeda, da nace takoma 6angaren Ammah, Dan asamu jinin ita momyn taku yasauka, tokuma saitace tafison tabi innah jigawa, idan tahaihu wai saita dawo".
         " karka yarda da wannan batun baffah, kasandai halin inna jummai, wlhy dakanta zata 6arar dacikin jikin mufeedar".
      Hakama Ammah tacemin d'azun.
      "Tokagani baffah, kawaima tatattara adarennan takoma 6angaren Ammah, barama dakaina zanje".
     " shikenan Mu'azzam, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, yajikin matar taka?".
      "Ameen baffah, jiki Alhmdllh".
     " ALLAH yak'ara afuwa to, tashi kawai kaje".
     Sallama ya khaleel yayma baffah yafice.
     6angaren Momy yanufa. Afalo ya iske su suna hira, inna jummai Na tsakkiyarsu, Duk suka gaidashi, sama-sama ya amsa yashige, innah jummai tarakashi da harara. dariya Anty Zuwairah tayi, tace, "nifa 'Yar tsamar innah da khaleel tana bani dariya, waimi kika masane haka innah?".
     Kunyace takama innah jummai, saita fara 'yan kame-kame, tarasa abinda zata fad'a domin Kate kanta.
 
     Daga Momy har ya khaleel da Anty shukurah suna jiyosu daga d'aki, saidai hankalin Momy nakan khaleel, sosai taga damuwa afuskarsa.
      "Ibraheem mike damunkane?".
      " murmushin yak'e yayi, babu komai Momy, ciwonkune mana keda A'eesha, waini momya bammaji kinmin maganar A'eesha ba, kobakisan batada lfy ba?, kinsamu jika Momy, amma banga kin nunamin farincikiba ko sau d'aya".
      Cikin daburcewa Momy tace, "ba....bahaka baneba Ibrahim, in...I..ina farin ciki mana sosai, Kasan tashin hankalin mufeedar nanne yadanne komai azuciyata. Amma yanzu ya jikin nata?".
       " Alhmdllh, saidai tana shan wahala".
      Baki hajia babba tad'an ta6e, amma khaleel bai ganiba, afili kuma tace, "ayya Allah Yakawo afuwa, dama ciki saida hak'uri, barema cikin fari".
         "Hakane Momy".
     " naga kema aii jikin naki Alhmdllh".
    "Uhm da sauk'i kam sosai, saidai abinda ba'a rasaba, kaji wai mi baffanku suke son k'ullawa?".
       " naji, Indai akan Auren Nafisa da Ameenu ne".
       "To mikace musu?".
         " mizance Momy, Addu'ar fatan alkairi namusu mana, ai hakan shine dai-dai kodan halaccin da Ameenu sukamana shida iyayrnsa".
    Fuska Momy tahad'e, "wai Ibraheem nikam mikakeson maida kankane?, Kaine babba acikin yara mazan gidannan, amma kokad'an bakada wata jarumtar kwato mana 'yancinmu nida 'yan uwanka, katunafa kaikad'ai ALLAH yabani namiji".
     ''Hakane Momy. Amma inason kiringa fahimta abinda yazo akan turbar gaskiya. Kasan cewata wakilinku agidan nan, bashine zaisa nayita danne gaskiyaba saboda farincikin Ku, itafa gaskiya D'ayace, daga k'inta sai 6ata, shin bakiji masu iya magana nacewa *_CIKI DA GASKIYA WUK'A BATA HUDASHI BA_*, wannanfa zancen gaskiyane wlhy, idan zaka kasance mai gaskiya abuga-abuga, dole abarka momy, Idan Abu yazo a turbar gaskiya yakamata kudinga kar6arsafa".
       " naji shashasha, tashi ka6acemin anan, sallamamme kawai, basaikaje kaita goyon bayansunba".
       Khaleel baice komaiba yatashi yafice, afalo yace INA mufeedah?.
      Hasnah tace, "tana d'akinta ya khaleel".
   Baice komaiba yashiga d'akin muferdah, tararwa yayi tana 6alle magunguna zatasha, jikinta sai rawa yakeyi bataso kowa ya ganta, shiyyasa taketa waige-waige.
    Shigowarsa yasaka jikimta k'ara k'arfin rawa, tasaki magungunan hannunta a k'asa yanayinta kawai ya tabbatar masa batada gaskiya, cikin takunsa Na jarumta yak'arasa gareta, tsugunawa yayi yad'ibi kwalayen maganin yana dubawa.
    Fuskarsa amatuk'ar d'aure yad'ago manyan idanunsa da suka koma jajaye gabad'aya yinin yau yad'orasu akanta, (humm todama Yaya lafiyar giwa) idon ya khaleel Na a daidaima ya'aka k'are ballantana yau dayake cikin 6acin rai, fitsari kawai mufeeda tasaki atsaye, jikake tsululululu!!😂.
       Lafiyayyun Marika hud'u yasakar mata, cikin daka tsawa mai firgitarwa yace, " ubanwa yabaki maganin zubar da ciki?!!! Nace ubanwaye yabakishi agidannan?!! Wlhy koki fad'amin koma 6a66allaki, dagake har cikin kutafi barzahun 'Yar iska maikama da dabba. Wlhy bak'aramin asarar kud'in Tara akayiba wajen biya miki kud'in makaranta, mai kwakwalwar kifi kawai, bazaki fad'amin Wanda yabakibane saina miki dukan mutuwa?".
        "Wlhy ya khaleel innah Ce, narantse bani nasiyaba..."
    Bata rude bakiba innah jummai tafad'o d'akin, saiwani cika da batsewa takeyi, Dan duk abinda ke faruwa sunaji afalo.
        Cikin masifa tace, "kai wallhi kafita idona in rufe, kafara shigarmin hancifa, yanzunnan saina fyatoka".
       kallon samada k'asa yamata, kamar ba kakarsaba, Dan Ransa amatuk'ar 6ace yake, idonsa yarufe baima tantance wadda yake agabansa, yace.
     "Dan ALLAH karki fasa fyatonin, ya da girmanki da shekarunki zaki d'auki abinda zai cutar da yarinya kibata?, anya  kuwa ked'in kakarmuce? Nifa INA kokwanto wlhy, dan tuni nakula da rashin k'auna dakike nunamin tun INA k'aramina, yanzu kuma shine zakibama yarinya magani wai danta Barar da ciki?, shiyyasa kika nemi abaki ita kutafi Jigawa?, shin idan ita batada hankali kema bakida shine?, wlhy tuni dama nakula ked'in tsohuwar......
            Bai k'arasheba yaji saukar mari akumatunsa, shiru yayi yaduk'ar da kansa, Dan yaga k'afafun Momy, karo Na farko data mareshi dawayonsa, bama itaba, zai iya rantsuwa da hankalinsa wani baita6a marinsaba sai yau.
       "Ibraheem bakada hankaline?, uwar tawa katasa gaba kakema fitsara? Shin INA hankalinka yatafine?, koka fara shan giyane wai?".
      Shiru yayi bai tankaba.
    Cikin daka tsawa Momy tace, "ibraheem kobaka jinane!!!!?".
        Nanma shiru yamata, har yanzu kuma hannunsa Na dafe da kuncinsa, idanunnan sunkuma rinewa jajur.
    " yaza'ayi yabaki amsa, dukdai kece kika jamana bala'innan, tunda kece kika dage wajen.......
      "Haba innah mikikeson fad'ane haka?"......
    Adai-dai nan baffah da Ammah suka shigo.
    Anty Zuwairah Na kuka tasanar musu abinda ke faruwa, Dan yau tausayin d'an uwan nata yashigeta, tadad'e da fahimtar tsangwama da k'yara da innah jummai ke nunama  khaleel, ita kanta tana mamakin hakan, amma bata ta6a kawo komai arantaba, Dan innah nacewa saboda miskilancin sane da taurin zuciya, itakuma batason mai wannan halayyar, dukda dai wannan bai Isa abin gamsarwa ba haka Anty zuwairah tashare bata maida hankaliba.....
       Baffah baice komaiba, sai Jan khaleel yayi ajikinsa, yana buga bayansa ahankali, wannan ne ya karya zuciyar ya khaleel, dama ga damuwar dake cunkushe da zuciyarsa tunda safe, saikawai hawaye suka fara zirara a kumatunsa.
     Karo Na farko danaga ya khaleel yana kuka😳.
  
         " Jummai iro yanada hujjar fad'a miki duk kalamin dayazo bakinsa, shin amatsayinki Na babba yadace kifita kinema maganin zubar da ciki kibama mufeedah?, shiyyasa kai tsaye nace banyarda kitafi Jigawa da itaba, saboda nasan halinki, nasan mizaki iyayi, wato hanawata tasakaki canja salo?, kika bata maganin dantasha yazube ayanzu? Wlhy jummai kinji kunya, tunda ke bazaki ta6a zama mai hankaliba, da ALLAH bai kawoshi d'akinba dashikenan
........
       Haba yaya, wai yazaki tasani gaba kina gayamin maganganu agaban yara? Naga yanda kikeda iko da mufeeda nima inada iko da ita aii.
     Tabbas kinada iko da ita jummai,  amma ikon bashi zaisa abarki ki cutar da itaba.....
     "Ammah kiyi shirunki kawai, kidaina 6ata ranki, aiiduk abinda kashuka saika girbeshi watarana".
        Hannu Innah jummai tad'aga zata mari ya khaleel dake magana, da sauri yarik'e hannun, ido cikin ido suka kalli juna, (wani irin tsoron  khaleel ne yashigi inna jummai, mugun kwarjininsa da baiwar rikita Mara gaskiya da ALLAH yayma kwayar idonsa yasaka dukkan sassan jikin inna jummai fidda zufa) yace, "daga yau banida kaka ta 6angaren uwa, nashafeki acikin tarihina, danhaka jummai, wlhy kikayi kuskuren marina saikinyi nadamar haiguwata dakika bari akayi, Dan saikinji inama Momy kika bama maganinnan tasha lokacin tanada cikina, Na radaddage aciki kuka watsani a gotta......"
   Baffah ne yazo ya janyeshi yana masa fad'a, Momy kuwa da innah jummai kuka suka Sanya, itakam Ammah ko'a kwalar rigarta, dantaji dad'in abinda ironta yayma k'anwar tata, taja hannun khaleel da mufeedah tafice.
    Baffah ma bayanta yabi.
     Anty zuwairah madai yau bataji dad'in lamarinnanba, kuma zuciyarta tafi karkata ga khaleel,  Dan ganin gaba d'aya yanda aka tozartashi, tamkar ba jinin momyba, tomi khaleel ya tsarema innah haka? Miyay mata dazafi haka? Kowa yasan tun suna yara batajan khaleel ajikinta, "why?".
       

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now