72

4.2K 313 2
                                    

72

       Su ya khaleel Na isa office aiki kawai yafarayi, yakwana biyu baizo office ba, saboda tafiyar dayayi, dukda dai akan aikine shima, amma baihana yatadda jibgin aikiba dake jiransa a office.
     Zamansa dakusan mintuna 40 kiran Taaheer yashigo wayarsa, harta kusan tsinkewa yad'aga.
     Bayan sun gaisa taheer ya tabbatar masa da wadda zasu kama tafito.
      "A'a mikuke jira, Ku kamata mana, damani banaso akamata cikin gidanmune kawai ne".
     "OK sir".

   Duk suka yanke wayar suduka.

     Aiki ya khaleel yakeyi amma zuciyarsa tarabu gida biyu, rabi akan Aysha rabi wajen matar dasu taheer zasu kama.
      Yana tsaka da tunaninnan akayi knocking d'in k'ofar office d'in, umarnin shigowa yabada, youseef yashigo hannunsa d'aukeda takardu,  saida yayi salute nashi, ya khaleel yanuna masa kujerar zama sannan yazauna, hannu yabashi sukayi musabaha.
    Yauseef yace, "sir, gashi munsami mutum kusan 16 masu tambarin kunamarnan".
         Da sauri ya khaleel yakar6i takardun yashigo dubawa.
     Saida yagama tsaf sannan youseef yacigaba da maganarsa.
       " tabbas barau modibbo yana ciki, sannan akwai yaron Alhaji bishasha Lazarus shima yanada ita, akwai yara da'aka kama agidanka suma duk sunada ita.
    Cikin mamaki ya khaleel yake kallonsa, kallo irin Na tabbatarwa.
    Youseef ya jinjina masa kai alamar gaskiyane.
     Huci mai zafi ya khaleel yafurzo daga bakinsa, gaskiya wannan lamarin yafara d'aure kansa, shin miyasa hakan kuma?, kenan da gaske akwai mai alak'a da wannan k'ungiyar acikin gidansu?, (zuciyarsa tana karkata ga zargin Aysha ne, musamman idan yatuna da lokacin da'aka sanarma barau modibbo zuwansu, ya tabbatar Aysha ce kawai taji hakan, amma to mizai sakata tiromusu 'yan Daba kuma? Bayan harda ita zasu cutar?, tokuma ya'akayi tasan talatuwa mai aikin Hajia khaltum ce?, kenan tanada alak'a dasu?, musamman idan Yakuma tattara bayanan matashiyar budurwa sakeena.
     Kai, bai yarda da zuciyarsaba, yabibiyi Aysha amma haryanzun bai kamata dawani Abu dayashafi wannan k'ungiyarba, yakamata gakuma sato masa Sakina, zaimata wasu tambayoyi.......
     Youseef ne yad'an buga table yace, "sir!, lfy kuwa?."
       Da Sauri ya khaleel yakawo numfashi, kuma furzar da hucin yayi sannan yace, "babu komaiba youseef, cigaba ina saurarenka".
     Ajiyar zuciya youseef ya sauke shima, yacigaba dafad'in sannan akwai wasu 'yammata biyu damuka kama kusan 3years kenan da cocaine a airport d'in Lagos, suma sunada wannan tambarin kunamar."
     Cikin jinjina kai ya khaleel yace, ''kunyi k'ok'ari youseef, kuma kucigaba da aikinku cikin kulawa, ina alfahari daku sosai".
      Murmishin jin dad'in yabon da ogansu yayimusu youseef yayi, yace, "duk wani kwazonmu yanadaga cikin tarbiyarka Sir".
       Murmushi kawai ya khaleel yayi, yace, "babu damuwa kaje, zuwa anjima zan nemeku kaidasu Joseph".
     "Ok, thanks sir".
Ya khaleel ya jinjina Kansa yacigaba da aikinsa.

__________________________

     Cikin nasarar aiki su Taheer suka sami damar cafke kubrah, a babban filin jirgin sauka da tashi Na Abuja, ankamatane tana k'ok'arin tafiya Lagos. mamaki yayi matuk'ar kama Taheer, Dan yasan kubrah sosai, tadad'e tana kamun k'afa dashi akan yashawo mata kan khaleel yasota. Yamzu har yarinyarnan zata iya ta'addanci haka?. Kai yanzukam ya gama yadda ba'a shedar mutum.
     Kallon-kallo kubrah da Taheer sukayi, sai gumi takeyi da rawar jiki.  pretending tafara musu, akan mitayi daza'a kamata?, tanayin hakanne kuma saboda taga Taheer, atunaninta zata samu sassauci daga gareshi. Amma abin mamaki saiya nuna halin ko inkula da ita, saima ka rantse baisantaba.
      Cikin yaran taheer wani yadaka mata tsawa da zabga mata lafiyayyen maruka, tuni tadafe kunci tana hawaye, bakinta kuma yayi gum, danta gane rijiya bawajen wasan makaho baneba. kad'an daga aikin masu bak'ar fuskarnan su suburbud'a mata alburushi atsakkiya kwalwarta yanzunan.
     Hankalinta baigama tashiba gaba d'aya, ta tabbata inhar ya khaleel nawajen zai kubtar da ita, tunda baita6a kamata dawata 6arnaba, koma hajia babba tasaka ya fiddota aii.

CIKI DA GASKIYA......!!Where stories live. Discover now