SANADIN SHI 01-10 BEGINNING OF FATE

182 6 6
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

'''ALHMDULLIHI ALLAH abun godiya da ya bani ikon cigaba da posting din labarin DA'IMAN ABADAN BOOK TWO (SANADIN SHI),fatan zaku bani hadin Kai kamar yanda kuka bani a baya...yanzun aka fara wasan fa🥰'''

*Daga tafiya hutun sati biyu ya zama complain oooni Jameey🤔 daga groups har DM maganar kenan yayi yawa yayi yawa to mun dawo ko satin d'aya ma ba ku bari munyi ba🤧,sai a cigaba da gashi sai dai Babu posting Saturday and Sunday Thank myluv's💋🥰*

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba,ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*1-10*

Abincin aka kawo masu na saukar amarya.masace da sinasir sai miyar ganye da taji kafar sa.sai kuma wata miyar kabewa ta aka wadatata da zallar hanta.wata kular kuma soyaiyen naman kaza ne a cikin sai kuma dayar ragadadar kan ragone.sai catoon din ruwa da kuma na lemuna kala kala.haka aka kawosu aka ajiye gabansu.
Sai sannu da zuwa Meelat take masu ta rasa Ina zata ajiye su dan dadi Meelat kanwar Najeeb ce uwarsu d'aya ubansu d'aya anan cikin abuja itama take aure.sai kuma Sema ita kuma kanwar Moha ce.kamar yanda Moha da Najeeb suka taso Kai daya haka ma Meelat da Seemarh haka suka taso.tare ake masu komai har hatta course d'aya suka karanta a turkey B.S.C.NURSING,kuma rana d'aya aka yi masu aure.
Meelat da kanta ta zuba masu abinci sai da ta fara kai ma Zubaida sanann ta zuba ma Zulaihat ta kai masu sai sannu take masu.yanda tayi masu kuwa sunji dadi dan har nuna sukayi.ita dai Zubaida ta samu ta dan ci kadan dan yanda take jin yunwa ba zataji zata iya kyale abincin ba gashi kuma kamshi sai tashi yake

Ita kuwa Zulaihat yanda aka ajiye mata abincin haka ta zuba mashi ido tasa sa hannunta a ciki ba dan bata jin yunwa ba,tana jin yunwa abunda ke yunwa sai dai bata jin zata iya cin wani abu a halin da take ciki.
Ta kasan ido take kallon movement din kowa tana ankare da komai.tana ankare da yanda yan'uwanshi suke cikin walwala da farinciki tana mamakin yanda ya fita zakka a cikin yanuwanshi.duk fuskar da ta kalla sai taga annnuri a samanta kamar dai fuskar Dr Moha,amman shi ne kadai ya banbanta da halin yan uwanshi bashi da annurin fuska ko kadan.

Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin yanda zatayi rayuwa da shi da irin wanann halin mai wuyar sha'ani.gani take bata iyawa dan ba zata iya dauka ba.ji take kamar tabi yan kawo amarya su koma tare dan ita bata iyawa.komai ya kwance mata tama rasa ta ina zata fara da wanann mutumin marar mutunci da tausayi.
Furzar iskan bakinta tayi tana cewa a cikin zuciyarta.."zan iya yes zan iya zan koya maka hankali zan baka mamaki Najeeb zan nuna maka Da da yanzun akawai banbanci na shirya zama da kai da ko wani irin hali kazo dashi kuwa."

Dangin su Najeeb basu bar shashen da aka sauke amare ba sai da goma tayi sanann suka yi masu sallama suka tafi.dan kuwa Shuraima makale kafad'a tayi tace ita a wajen Zulaihat zata kwana ba yanda ba'ayi da ita ba amman taki yarda har da kukanta ganin tana kuka yasa Zulaihat saka baki akan a bar mata ita.
Daman bata son tafiyar yarinyar duk da ba wata magana take mata maitsawo ba amman tana dan yaye mata wani pain din,ajiyar zuciya Yaya Seemarh tayi tana barin Shuraima dan ba yanda zatayi,amman taso ta biyota suma su Zubaida sun samu su dan sake suyi fira da yan uwansu tun dai gobe zasu tafi.flight din rana zasu bi
Bayan tafiyarsu Zubaida ta fara tashi dan shiga wanka dan daman a takure take. Tana fitowa Zulaihat na shiga wankan bayan ta fito sauran yan rakiya suka shiga kowa yayi shirin bacci,dan kafin su gama shiryawa har Shuraima tayi nisa a bacci.gyara mata kwanciya Zulaihat tayi tana kureta da kallo.tana bala'in kama da Najeeb dan dai kawai Najeeb ya dan fita haske da kadan.ita tana da duhu sabanin shi da yake da haske shine kawai banbanci, Addu'a ta tofa mata sannan itama ta kwanta tana yin Addu'ar baccin itama.

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now