SANADIN SHI 101-110

34 1 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Editing❌*

*101-110*

Yau da wuri na tashi da yake Ina da lecture ten,lokacin da na gama hada mana breakfast takwai ta wuce wanka na shiga na sa kaya sanann na fito na zauna na fara breakfast Ina cikin yin breakfast Meenat ta fito itama cikin shiri kallonta nayi Ina cewa.
"Daman kina da lecture yau."?
Zama tayi tana hada tea, murmushi tayi tana cewa.."Ina kwana Yaya Jidda." Hadiye abincin bakina nayi Ina ansa gaisuwarta time ta kalla tana cewa.
"Wallahi fixing din lecture din akayi mana daga dawowa har an fara had'a mana zafi."
Murmushi nayi Ina cewa.."ai daman ku manya ne barrister ce fa nan da kanta."
"Amman kafin na zama Barrister din ansha wuya ko Yaya Jidda? daga wannan sai wanann har na gaji da karatun nan wallahi Wanda bai karewa."
Dariya nayi Ina tashi nace.."Daman aiki idan yazo gaban goshi ai yafi zafi duka duka baifi yan shekaru ki gama ba."

Itama tashi tayi tana daukar back bag dinta tace..."amman kafin yan shekarun suzo ansha wuya sosai Yaya Jidda." Har na nufi kofa na waigo Ina kallonta dan waro idona nayi ina cewa.."ya da tsayuwa kuma?ko ba ten kike da ita ba."? Kallon time tayi tana cewa ."ten gareni mana,wai Baba ya fito ya bamu kudin transport ko."?

"Okay taho mu tafi akwai kudi a wajena."

Tahowa tayi muka tafi muna fitowa muka tadda Wasi tsaye tana waya sai murmushi take ga dukan alamu da Yaya Auwal take waya dan daganin wanann wayar ta masoya ce murmushi nayi Ina cewa.

"Morning yanmata."

Waigowa tayi tana cewa.."ai yanzun nike shirin shiga na fito dake." Turo baki nayi Ina cewa.."duka duka yazun 9:30 tayi har na makara kuma."

"Kwarai kuma kina da tabbata cin zamu samu naped kan lokaci."? gaba nayi ina cewa.."ai yanzun gashi nan zaki sa muyi lating din mai hujja ba." Bayana tabi tana cewa.."Meenat wanann semester kenan kina da lecture din safe kema." Murmushi tayi tana cewa.."aikuwa rabin lecture din wanann na safe ne amman bamu da lecture yau ma kawai dai fixing akayi mana."

"iKon Allah har an fara fixing kenan daga dawowa hutu to Allah dai ya bamu sa'a baki d'aya."

Da Amin muka ansa muna ta famar tsada naped amman shuru bamu samu ba,cikin ikon Allah sai ga Yaya Auwal ya tsaya yana cewa.

"sannunku iyayen yan makara ."

Tare mukayi dariya Ina cewa.."Laaa Yaya Auwal wallahi Wasi ce ta jamana wanann makarar." Kallon Wasi yayi yana murmushi langwabar mashi da Kai tayi tana turo baki tace.."amman Babe ai kasan komai tunda kana jinmu a waya ko."

Gira d'aya ta dage mata yana cewa.."amman ai waya kika tsaya da tsigumi ko Sweetheart."

Turo baki kawai tayi tana harfe hannu,fakaitar idon Yaya Auwal nayi Ina mata gwalo,kukan banza ta barke dashi tana cewa.."Babe ka ganta ko."?

Dariya nayi Ina bude baya na shiga nida Meenat,itama ta shiga gaba sai zabga mashi shagwabe yake shi kuma yana ta lailashi yana maida laifin a wajena.

Bayan ya saukemu ya wuce wajen aiki,da yake ba wata lecture bace mai tsawo zamuyi one hour ce ,ana gamawa muka je wajen project supervisor dinmu muka anso gyaran chapters din akayi mana sannan muka fito bamu tsaya bata lokaci ba muka dawo gida.

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now