SANADIN SHI 31-40

44 2 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*EDITING ❌*

*31-40*

Itama Wasila tashi tayi tana cewa."Allah ya bada hakuri,Mama zan wuce gida." Kallonta Mama tayi tana cewa."Amin,Amman Wasila kunyi ganganci ai ba'a kin fadin wanann babbar matsalar,fadi ake da wuri dan ayi ma tukar hanci ba sai komai ya runceb'eba." Kallona Wasi tayi tana cewa."wallahi Mama bansan bata gaya maku ba,dan nasan bata boye maku komai nasa tuni Kun sani ai da nasan baku sani ba da ni da kaina zanzo na gaya maki dan ayi maganin matsalar."

Kwafah Mama tayi tana wurga man harara tace."Kulu ashe daman baki da wayau ban sani ba,ashe wayaunki na banza ne har da wofi?ina kika Kai hankalinki da tunaninki Kulu,to daga yau karda na sake ji balle gani karda ki sake boyeman komai naki,nice mahaifiyarki nice ya dace ki daya ma damuwarki,karda ki sake ko da wai ace kin boye man abunda ya shafeki dan nice nayi silar kawoki duniya."

Dan shuru tayi tana mai kallon Wasila tace."yi tafiyarki Wasila,Allah yayi maki albarka ya kareki a duk inda kike."Dan dukar da kai Wasi tayi tana cewa ."Amin ya Allah Mama na barku lafiya." Tafiya tayi bayan ta tafi Mama ta cigaba da cewa."duk duniya baki da kamata daga ni sai yan uwanki,ban hanaki.gayama Wasila damuwarki ba tunda itama tana gaya maki ta ta damuwar,amman kisan mai zaki ringa gaya mata,bai yuyuwa ace yanda tasan asirinki ni uwar da na mahaifeki ban sani ba,gaskiya ban yarda da wannan tsarin ba."

"Inason nida ku mu zama tsintsiya inason gidanmu mu zama abun kwatainci a wajen yan'uwa saboda hadin kanku, inason yarana su mana abun nunawa a wajen kowa saboda nastuwarku,dan haka karda ki sake rufemana damuwarki dan damuwarki tamu ce mu dukanmu,haka ma farincikinki namune mu dukanmu,mu hadu muyi murna tare idan a abun farinciki ya samu d'aya a cikinmu,sannan mu hadu muyi kuka tare idan wani abu ya samu wani a cikin shine ake kira da uwa daya uba daya."

Nidai bance komai ba,inajin yanda suke man fad'a dan sosai Mama tayi man fad'a kamar ba Mama ba mai saukin kai da raha maiwasa da yaranta,sai da suka gama na basu hakuri sannan na tashi na shiga room dinmu,wanka nike son nayi ga kuma kaina na ciwo saboda hayaniyar da nayi Ahmad ga kuma maganar su Mama, wani irin ciwon kai Nike sosai wanka na shiga dan na dade a toilet Ina watsa ma kaina ruwa Ina sauke ajiyar zuciya,sai da naji natsuwata ta dawo normal sanann na fito,doguwar rigar material na saka sanann nayi sallah na kwanta sai bacci duk da banyi isha'i ba, na gaji Ina bukatar hutu sosai.

★★★

Koda su Baba suka fita ba inda suka zarce sai gidan su Ahmad sallama Baba yayi ma mai gadin gidan yana ce mashi. Malan sannu da aiki."

"Yauwa sannu Alhaji,lafiya dai ko."?

Lafiya lau Alhamdullahi,nace Alhaji Bala mato yana ciki kuwa."? Dan shuru maigadi yayi yana kallon Baba sai kuma yace."yana ciki,amman baiyi dani yana da bak'i ba gaskiya." Murmushi Baba yayi yana cewa."eh gaskiya kam baisan da zuwana ba,amman dan Allah kayi man alfarma kayi man sallama dashi dan magana nike son nayi dashi mai mahinmamci."

A gaskiya Alhaji kayi hakuri dan baisan ana shiga ana kiranshi idan baiyi da kowa zasu hadu ba,dan shi Alhaji Bala ba mutumin da ake zuwa ana ma hawan kawaraba." Murmushi Baba yayi yana cewa."amman ai ban maka kama da mabaraci ba dai ko?tun daga kayan jikina zaka kalla har da motar da nazo da ita banyi kama da matsiyaci ba."

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now