SANADIN SHI 121-130

45 4 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*121-130*

Zaune suke a cikin parlo sunyi jigum ba mai ma wani magana ba sautin da ake tashi a parlon sai sautin kukan Haidar tun ana bashi hakuri har an daina an saka mashi Ido,kuka yake kamar karamin yaro tunda Muhd ya kirashi waya ya gaya mashi halin da ake ciki ya nemi ticket ya duro a gusau yake kuka..kowa ka kalla fuskarshi a parlon ba annuri a cikinta sai tarin damuwa...damuwar d'aya ce har yanzun basu kira waya ba wanda suka dauketa takaimaimai ba'a ma asan shin waye suka dauketa tunda ba a gida bane balle ace kidnappes ne.

Mutanen unguwa da mutanen gari sai zuwa suke jaje,sallamar da akayi ce ta tada su Yaya daga parlon suka koma bangarensu har lokacin kuka Yaya Haidar yake dafa shi Yaya Muhd yayi yana cewa.

"Haba Broth kukan nan ya isa haka karda ka jawo ma kanka ciwon kai addu'a zamu cigaba da yi mata Allah ya tsare ta a duk inda take shine yanzun fatanmu ba wanann kukan ba, banjin dadi idan Ina kallonka kana wanann kukan da wane zani ji dan Allah."

Cikin kuka Yaya Haidar yace.."Broth kenan duk yanda zan gaya maka yanda zuciyata take man akan wanann b'atan na Jidda ba zaka fahimceni ba,yanzun ace mace tana hannun wasu gardawan banza tun jiya gashi yau din ma dare yayi Ina hankalina zai kwanta ba zai tab'a kwanciya ba wallahi inason Jiddah kuma Kai kasan yanda nike da kishi akan abunda nike so nike kauna ba zan iya yafe masu ba hannunta da kuka kama da shigar da ita a cikin motar balle kuma yanzun da take a wajensu sai kalleta suke taya zuciya zatayi dadi."

Dafashi Yaya yayi yana cewa.."naji na kuma fahimceka na gane abunda kake nufi amman dan Allah kayi hakuri ka daina wanann kukan,kayi mata addu'ar Allah ya Kareta daga sherinsu,mu zage muyi addu'a Allah ya shiga tsakaninta dasu ba wannan kukan ba wallahi rabona da bacci tun shekaran jiya haka abinci mai nauyi sai da tea Kulu ce kawai a raina baiwar Allah."

Shidai shuru kawai yayi yana share hawayen shi bai son yawan magana daman ya lafiyar kura balle,daman can Yaya Haidar bai da yawan magana idan anga yayi magana mai tsawo to ina tare dashi ne amman family kowa yayi mashi shidar shi din missikilne na karshe nima da kallon da nike mashi kenan ya cika miskilancin banzan da kuma girman kai da jiji da Kai kamar wani basarake.

Amman tunda muka fara soyayya dashi na gane ba haka bane shi mutumin so simple yana da dadin zama da dadin hulda bai da damuwa ko kadan sai da yana zafin zuciya da saurin daukar fushi kuma ni sheda ce yana da zafin kishi..kishinshi ya wuce duk yanda zan gaya maku shi ance maza sunfi mata kishi ada ban yarda da wanann maganar ba sai da Allah ya hadani da Yaya Haidar anan na yarda dan shi Yaya Haidar ko a cikin maza samun mai irin kishinshi sai an tona ko antona din dakyal a samu biyu a cikin goma.

Idan yana nuna kishin shi watarana har tsoro nike ji ina jin anya zan iya aurenshi ba?ba dan komai na nike wannan tunanin sai yanda yake da zafin kishi irin masu kishinshi basu cika zaman aure da matansu ba...abunda yasa nace haka suna da saurin zargi magana zakayi da wani namijin zasu aiyana ma kansu wani abu daban to shima haka yake.

Dan sai da nayi da gaske dashi sannan ya hakura ya barni ina cigaba da gaisawa da Yaya Auwal sai da yaga da gaske akan hakan zan iya hakura dashi sanann ya barni ba dan yaso ba,amman idan har yaga muna magana da takai minti biyar sai yayi tsugumi yace har yanzun Ina son Yaya Auwal ai da nasan Ina sonshi da na aureshi haka nike fama dashi akan Yaya Auwal.

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now