SANADIN SHI 61-70

48 2 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*61-70*

Turaruka ne ciki masu kyau da tsada da kuma sanyaiyen kamshi sun Kai guda goma.fiddosu Meenat tayi tana jerawa d'aya bayan d'aya tana rike baki dan ba karamin kudi Yaya Auwal ya kashe ba wajen turaren dan ba na kasa da dubu dari,rasa abun cewa mukayi mu dukanmu sai dai kallo.

Rasa ta cewa nayi sai dai tashi kawai da nayi jin Mama na cewa Yaya Muhammad sun taso, Meenat ma had'a turarukan tayi waje d'aya tana cewa.."gaskiya Yaya Auwal ya kashe kudi da yawa kusan million daya da rabi ya kashe maki Yaya Kulu, wannan turare sunyi yawa a san dai yanda za'ayi."

Murmushi kawai nidai nayi na cigaba da gyaran parlo,haka ma Mama batayi magana ba sai Yaya Bash yace."zan mashi magana ya bar kashe mata kudi haka da yawa,kashe kudin sunyi yawa mai zatayi da turare har na kusan million biyu?haba mana ai ba'a haka gaskiya wato an hanashi kawo kudi sai ya koma kawo kaya ko?zan mashi magana ya rage ba'a hanashi yi mata kyauta ba,amman yayi wanda hankali zai dauka mana."

Anan Mama tayi magana tana cewa."ya dace dai kam ayi mashi magana,ya rage kashe kudi nan haka gaskiya, yarinyar da ba ma sonshi take ba yake ta yi ma barnar kudi haka,nidai ba ruwana idan Babanku ya dawo yaga wannan turarukan bansan wani irin fad'a zaiyi ba daman ya hana ana ansar mashi Koda naira biyar tunda ba'a tsada rana ba,akan mai zai kashe kudi har haka."?

"Nima abunda na gani kenan Mama,dama ace tana sonshi da sauki amman ita Jiddarh ta fito fili ta gaya mana gaskiyarta Kinga bai dace ba ta dunga ansar mashi abu idan ba son banza bane irin nata na bansani ba."

Turo baki nayi ina kallon Yaya Bash sai kuma nace."amman Yaya Bash ai bance ya kawo man ba ko?kuma sai da nace ban ansa ya ajiye ya tafi ya zanyi dashi?daman ai nema yake dole ya kashe kudi dan ya samu." Kama baki Yaya Bash yayi yana kallona sai da ya gama kallona sannan yace.

"Gaskiya ne Jiddarh kince wani abu,to dan ubanki idan kika cigaba da ansar mashi abu to wallahi sai ki aureshi ko kina so ko baki so,ki rubuta wannan ki ajiye."

Yanda yayi maganar with so serious sai na gama kaina ban yarda na sake cewa komai ba,dan nasan waye Yaya Bash ba sauki bane dashi ga saurin zuciya,nasan ba karamin aikinshi bane ya zuga Baba ya aura man Yaya Auwal ko Ina so kuwa ko ban so,dan Baba yana jin maganar Yaya Bash ,idan suka had'a Kai suna magana sai ka rantse kace mai tsabar yarda da juna da sukayi sun ma zama abokai.

Ina gama gyara parlon na dauko gyale na nabi Yaya Bash zuwa airport dauko Yaya Muhammad,Muna Isa jirginsu na sauka bamu dade ba suka fara saukowa da gudu naje na tareshi Ina cewa.

"Oyoyo Yaya Muhd welcome back." Murmushi yayi yana rikoni ya kalleni yace.."Masha Allah Kulu kice kika koma haka."? murmushi nayi Ina rufe fuskata dan rabon da ya ganni yanfi shekara Tara ta goma ake dan tunda ya tafi karatu bai dawo ba sai da ya gama sanann yau Allah yayi mashi dawowa,jan hancina yayi yana mikama Yaya Bash hannu suna hunging din juna, kallon shi Yaya Bash yayi yana cewa.

"Broth nayi missing dinka sosai da sosai."

Murmushi Yaya Muhd yayi yana cewa.."Nima Bash nayi kewarka har bansan ya zan kwatanta kewarka ba Ina Manu."?

Dariya yayi yana daukar jikarshi muka nufi mota yana cewa.."yana can yana ta tukuburi wai anbarshi ban taho dashi tararka ba."

Girgiza kai yayi yana cewa.."maiyasa baka taho dasu ba dukansu sai ka taho da Kulu kadai."?kallona Yaya Bash yayi yana cewa.."har ka manta wacece Kulu kenan?dan banzan naci ne da ita ka ganta ne,sai da nace ban zuwa da kowa in fito na ganta kofar gida tsaye tana jirana rashin abun ce mata nayi shiyasa kawai na bude mata ta shigo mu wuto karda ta mutu kafin mu dawo."

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now