SANADIN SHI 91-100

37 1 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*NO EDITING*

*91-100*

Koda na shiga gida room dinmu na shige nayi wanka na fito nayi sallah,sannan na zauna muka hau fira da su Yaya Teemarh,da yake ban nan suka shigo kallonta nayi Ina cewa.
"Masha Allah,Yaya Teemarh kinyi kyau kin chanza kamar ba ke ba,nikam bai Momy ke baki da kika je birnin kebbi kika sauya haka."?
Murmushi kawai tayi tana cewa.."ni ai naga kamar ma kin fini yin fresh din Kulu maiye sirrin."? Dariya duka akayi ana cewa ai ba Wanda ya Kai amarya kyau da shek'i kuwa,haka muka kusan kwana Muna fira nidai d'aya nayi na dare na kwanta dan ba zan iya wanann doguwar firar ba.
Washe gari aka tashi da hada hadar daurin aure karfe biyu na rana aka daura auren Fatima Abdullahi Jibir da angonta Abubakar Sadiq Aliyu akan sadaki naira dubu dari biyu.
Bayan an daura aure aka fara shirin daukar amarya sosai gidan ya dauki harami na biki ga kuma kukan da amarya take na rabuwa da gida,har damu wajen kuka dan had'a kai mukayi waje d'aya dani da ita da Meenat muna kuka dakyal aka banbareta daga jikinmu aka shiga mota da ita.

Sai da na tabbatar da duk wanda zashi kai amarya ya shiga mota,sanann na koma bayan gida na dauko dinku nan mu na dinner da yake ba'ayi komai ba a biki sai da dinner da za'ayi itama da ace anbi ta son rain Yaya Teemarh to ba'ayi ba.
Fitowa nayi naji wayata tana ringing fiddowa nayi Ina duba mai Kirana bakuwar number ce,burus nayi ban dauka ba na cigaba da tafiyata wani Kiran ne ya Kara fitowa a karo na biyu sai da ta kusa zama misscall sannan na dauka Ina Kara wayar a kunne nayi shuru.

"Kina Ina."?

Tambayar da akayi man kenan,lumshe idonu nayi Ina bude su dan nayi missing din shi sosai bama kamar voice din shi,rabona dashi tun jiya da muka dawo daga wajen cin abinci .

"Gida."

"Okay ba zaki je gidan amarya ba."?

"Zani na tsaya daukar kayana ne wanda zan saka da anjima idan zamu dinner."

"Okay Ina bakin gate idan kin gama ki fito sai na kaiki."

Murmushi kawai nayi Ina kashe wayar na koma cikin gida a room na dauko takalmi da jikka sai kuma sarkar gold da yanhannu da zobe da Mama ta saya mana muyi kwaliyar biki.
Jingine na tadda shi bakin motarshi yana danna waya,karasowa wajenshi nayi Ina sallama,kallona yayi yana aika man da wani irin kallo mai wuyar fassara sai kuma can yace.

"Madam yau dai na hukuntu." Turo baki nayi Ina cewa.."da akayi maka mai." Hararar wasa yayi man yana bude back seat ya ajiye kayana sanann ya kama hannu ya shigar dani mota ya zagayo ya shiga muka tafi.

"SP yau har kusan kuka sai da nayi fa."

"Ayya PP waye wannan mai tsotsayin da ya kusa saka man kai kuka."?

Langwabar da Kai yayi yana cewa.."Uhmm!Allah sarki ni dan bawan Allah,Sp ai kinsan wanda ta tab'a ni dai."
Murmushi nayi Ina cewa.."nidai kam ban sani ba sai an gaya man nayi mashi hukunci." Samun waje yayi bakin titi yana parking maido hankalinshi yayi wajena yana nuna man zuciyarshi yace.

"Zuciya bata da jumurin rashinki ko da minti d'aya ne Sp amman kuma kikayi punishment dina da rashin ganinki ko?yanzun da ban kiraki waya ba da shikenan ba zaki nemaini ba."

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now