SANADIN SHI 111-120

30 2 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*111-120*

Bayan na gama sallah na bude data ta na dan duba whatsapp nan naga Wasi ta turoman pictures din da akayi mana jiya,duba pictures din nayi naga muyi kyau sosai ba wanda bamuyi kyau ta bayan nagama yi mata godiya nayi ma Yaya Haidar forwarded dinsu da su Yaya Teemarh ya Muhd da dai duka yan gidanmu masu yin whatsapp harda freind dina mata na primary dana unguwa da kuma yan course mate dinmu.

Bayan na gama tura masu na kashe data na na dan kwanta dan baki d'aya ni jina nike wani iri duk da Ina cikin farinciki yau zan kammala karatuna na degree amman lokaci lokaci Ina jin gaba na faduwa tun jiya Koda na gaya ma Wasi cewa tayi naita inalillahi karda na sama kaina damuwa..ko yanzun da na gama shiryawa na fito parlo danyi breakfast na dan k'ara duba karatuna da yake sai 2pm muke da exams din again gabana faduwa kawai yake.

Daurewa kawai nayi Ina bin kowa da Ido yana ta rayuwarshi hankali kwance cikin walwala..ni kuwa tawa zuciyar bansan abunda ya samaita ba sai karaya take kuma ba abunda akayi man ba fad'a nayi da Yaya ba balle ba abunda aka man ban ma kowa laifi ba amman sai faduwa gaba nike fama dashi tun jiya.

Jin karatun ya fice a raina yasa na ture littafin gefe muka cigaba da fira da su Yaya Bash da yake kowa na gida banda Yaya Teemarh da take gidan miji,ita kuma Meenat bata da exams sai next week dan wani irin interval suke samu a wannan semester din.

Kallonsu ina murmushi na kamo hannun Autarmu Rukky nace.."inasonki Rukky." Murmushi Rukky tayi tana jan kumatuna tace.."Nima Ina kaunarki Yaya Jiddarh." Dariya akayi duka parlon sai kowa ya koma yana cewa inasonki wance haka muka kama Mama sai dariya take mana sai a lokacin na danji saukin faduwar gaban da nike fama da ita,suma sunji dadi da sukaga na sake na koma kamar yanda nike a da dan na gaya masu faduwar gaba nike ji tun jiya,suma addu'a sukace nayi karfe Sha biyun rana Yaya Bash yace na tashi na koma room dinmu na dan k'ara duba karatuna kafin one tayi sai na fara shirin tafiya school din.

Tashi nayi banyi mashi gardama ba duk da banso ba,naso ya barni a karasa firar dani sanin hali yasa na mike cikin mutunci da sallama na shige room dinmu Ina shiga na dauko waya na kira Yaya haka kawai naji inason jin muryarshi dan tunda mukayi waya da asuba bamu sake ba,sai dai munyi chating da na tura mashi pictures din da mukayo jiya nida Wasi.

Sau biyu Ina karanshi bai dauka ba nasan bai kusa ko yana theater ila ya bar wayar a office cigaba nayi da kallon peper ban dan ina ganewa ba haka dai nai ta dubawa har lokacin sallah yayi nayi sallah na kuma yi wanka na shirya fitowa nayi na dan zuba jallop rice din kadan sai uban salad da na zuba mai yawa na kuma Kara bama a sama ma zauna na cinye duka nasha zobo sannan naje nace ma Mama ma tafi.

Har gida na tadda Wasi muka gaisa da Mami sannan ta saka hijab dinta muka tafi yau Yaya Auwal bai samu damar zuwa kaimu ba saboda wani aiki da aka tureshi a lagos a wajen aikinsu.

Cikin ikon Allah sanda Daya da minti hamsin zatayi muna cikin exams hall,kowa ka kalla fuskarshi kumshe take annuri banda ni da yanzun naji gabana ya dawo da faduwa faye da ma sai da na dafe kirjin Ina inalillahi idan ta lafa na cigaba da karatuna.

Biyu daidai invigilator suka shigo nan aka fara raba answer sheet muka fara last exams Alhmdulh duk da ba wani karatun natse nayi ma course din ba saboda yanayin da nike ciki ya ansa duka da yake answer three questions ne cikin question biyar na samu masu sauki wanda na iya nayi answering three hour ne  da yake three credit unit ne course bamu fito ba exmas ba sai 5pm.

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz