SANADIN SHI 41-50

44 3 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Editing❌*

*41-50*

Ina mai neman afuwarki da yafiyarki akan abunda nayi maki a school Hauwa,nayi nadama sosai marar adadi ni yanzun har bansan da wani ido zan kalleki ba akan wanann lamarin,sai dai kawai nace kiyi hakuri Ina mai k'ara baki hakuri dan ni mai laifi ne a wajenki ba zan tab'a gajiyawa ba wajen baki hakuri Hauwa,daga karshe zan ce maki Allah ya zab'a maki da abunda yafi alkhari ya baki miji na gari Jidda dan ni ban cancanci na zamo miji a gareki ba,kamillar mace kamar ki sai kamilin namiji na barki lafiya daga mai kaunarki Ahmad Bala mato Gusau.

Na dad'e Ina sake maimata karanta message din Ahmad,ni tsoro ma ya kamani mai ya faru mai zafi haka da har Ahmad yayi sauri saukowa daga alkwashin da ya dauka?Anya kuwa ba wata gadar zare yake kullaman ba?nasan halinshi fah nasan waye Ahmad ko kadan bai da kirki ban dauka kowa da mutunci inba iyayenshi ba,tabbas ruwa baya tsami banza ban yarda da tuban ba,wannan ba tuban Allah na Annabi bane nasan haka kawai ba zai yadda makaman yak'inshi ba dan kawai Baba sunje gidansu.

Wata zuciyar kuma raya man tayi ai yana jin maganar iyayenshi kuma baison b'acin rainsu,maybe sune suka nuna mashi fushinsu shiyasa yayi nadamar abunda yayi kamar yanda yake fadi,Indai na shiga kokanto komai tsayaman cak!yayi da na saka wanann sai na kaucen na kulla wanann.

Ina a cikin jimamin message din Ahmad su Mama suka dawo nik'i nik'i da kaya,dan sayaiya sukayi ba karama ba kudi suka kashe iya kashewa kamar ba'a so,sannu da zuwa nayi masu Ina shiga kitchen na kawo masu ruwa mai sanyi,na zuba ma kowa a cup na mika masu,ansa sukayi suna sha,sai da suka gama sha Yaya Teemarh ta kalli tace.

"Allah yayi maki albarka Jiddah." Murmushi nayi Ina cewa."Amin Amarya ko a k'ara zubo maki."d'aga man kai tayi tana sauke ajiyar zuciya, murmushi nayi kawai na k'ara zuba mata wani  nan ma na zuba ma Mama k'ari sai da suka sha cup biyu na ruwa sannan suka dawo dai dai.

Dukawa nayi wajen kayan Ina kallo sai na kallesu nace."gaskiya kunsha kasuwa tun safe." Murmushi Meenat tayi tana cewa."ai dole mu jima a kasuwa Yaya Jidda,karki so kiga yawan da mukayi sai da muka kewaye kasuwar nan dukanta Ina jin,sai da muka saya komai sauran kayan ai suna dakunan baya ai Mama tasa aka kaisu."

Daga kayan nayi Ina kallon wasu glass cup da sukayi man kyau sosai,gaskiya kam sun kashe kudi abunda ke kudi,sai da na gama ganin kayan na gama yabawa sannan na tashi na shiga kitchen na dauko masu abinci na ajiye masu gaban su a tsiyar Parlo dan ko dinning ban nufa dashi ba,saboda nasan ba zasu iya hawa dinning ba Koda na Kai masu dan a gajiye suke sosai.

Kallon Abincin Mama tayi tana cewa."ajiye abincin nan gefe Kulu bari mu dan watsa ruwa mai maido karfin jikinmu mu kuma yi sallah sai mu dawo ma abincin,dan muna iya ci kuma jikinmu ya mutu mu kasa tashi muyi wanka da sallar kuma."

Daga Kai nayi Ina cewa."hakane kuma , ku tashi to kuje ku kintsi yummy better na jiranku." Kallon food flasks din Meenat tayi tana cewa."gaskiya kam Yummy na jiranmu wannan iyayen flasks din duk abinci ke ciki."? d'aga mata kai nayi Ina cewa."sai ma kin dawo idonki zai gane maki dadinki da ke ciki." Dariya tayi tana bin bayan su Mama da sukayi gaba,gyara kayan nayi na kaisu dakin Baba na ajiye sannan na fito ya kulle dakin na kunna kallo,ganin waka aka saka a channel din da ake kallo na maida wata tasa suna haska wildlife nan na zauna na fara kallo dan bani gajiya da kallon wild bama kamar a saka na zagikuna da giwaye to ban sanin iya adadin da zan bata a wajen kallonsu.

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now