SANADIN SHI 81-90

35 1 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*EDITING NO❌*

*71-80*

"Auwal Ishaq." D'agowa kawai Yaya Auwal yayi yana kallon shi bai ce komai ba,amman kacokam ya maida hankalinshi wajenshi yasan magana ce zaiyi mashi mai mahinmamci tun da har ya kira full name dinshi to tabbas yasan magana ce zai mashi ba ta wasa ba,yana fatan yaji alkhari dan jikinshi har yayi sanyi ganin yanda Yaya yayi kasa da kanshi yak'i yarda su had'a Ido sam.

Katse shurun Yaya yayi da cewa.."Daman zuwa nayi da wata alfarma wajenka,duk da nasan ba'ayi maka adalci ba,sai dai inason ka sani komai ya faru daga Allah ne."

Shuru yayi yana maida ajiyar zuciya,ruwa Yaya Auwal ya dauka  yasha yana goge zufar goshin shi,dan haka nan yaji maganar da Yaya zai gaya mashi ba dadinta zaiji ba dan gabanshi sai faduwa yake dam.sai kace wanda yayi gudun ceton rai murmushi ya kirk'ira yana cewa.

"Hakane kam Muhammad maganarka gaskiya ce komai nufi na Allah ne ba bawan da ya isa ya tsallake qaddararshi fatanmu Allah ya bamu ikon yarda da qaddararmu."

"Amin."

Tare suka ce Amin, duk su duka jikinsu yayi sanyi ba kamar Yaya Haidar da yake jin da ya san Muhammad zaiyi ma Auwal wanann maganar to da ba abunda zai shigo dashi office din Auwal da wani ido zai kalle Auwal,so yake ya tashi ya bar masu office din amman baisan wani excuse zai dauka ba,dubara ce ta fado mashi ya tashi yana cewa.

"Am Auwal ba toilet ne a office din nan."? Dan murmushi yayi yana cewa."eh akwai sai dai tap din kamar ya dan tsaya jiya kuma ba'a shigo an gyara ba har yanzun."

Nufar kofa yayi yana cema Yaya.."No problem bari na dan je na dauko ruwa a mota." Daga haka ya fita yana daukar wayarshi, murmushi Yaya kawai yayi yana maida hankalinshi wajen Yaya Auwal yace.

"Auwal nasan kasan matsayinka a wajena wallahi har gobe haka kake,kai ba iya abokina bane ka zama dan'uwa,ka gafarceni akan maganar da zan maka kuma inason ka fahimceni Ina fatan hakan."

Cigaba da cewa yayi.."Daman maganar ba ta kowa bace face Jiddarh,nazo ne muyi maganar Jidda dakai,maganar gaskiya Auwal anyi ma Jidda Miji tunin dadewa a birnin kebbi,sai yau naga turarukan da ka kawo mata nike tambayarta har yanzun kuna tare tace man eh,nace tana da interest akan aurenka ta nuna man A'a ni kuma ba zan zuba Ido ba nasan ba aurenka zatayi ta kama b'ata maka lokaci shiyasa nace zan gaya maka Ina fatan ka fahimceni dan Allah."

Kasa Yaya Auwal yayi da kanshi baice komai ba sai inalillahi wa'innalaihirajiun da yake ta maimaitawa sai yayi ya kusa sau biyar sai ya d'ago yana kallon Yaya idanunshi jajir harta jijiyoyin fuskarshi sun tashi tsabar shiga tashin hankali,AC ce kunne a office din tana buso masu sanyi,amman shi take yaji ya jike sarab da zufa ta ko Ina zufa keto mashi take,hawaye ne yaji suna zubowa a saman kyawkyawar fuskarshi,ya kasa tsadasu haka ya sake kallon Yaya yana cewa.

"Wallahi Muhd na fahimceka kuma na yarda da kaddarata daman banda rabon da rayu da Jiddah *DA'IMAN ABADAN*,haka Allah yaso kuma wallahi naji dadi ka gayaman matsayina a wajen Jiddarh duk da tuni naso na gano hakan,kuma wallahi na bar mata wanann turarukan da kazo dasu inace ko babu soyayya ni mai kawo ma turaruka ne saboda kanwarka kanwatace,kuma wallahi matsayinka yana nan yanda yake Muhd har abada Muna tare akan rashin samun Jidda ba zai taba shafar zumincinmu ba har *ABADAN*."

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now