SANADIN SHI 131-140

38 2 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*WANNAN PAGE DIN NAKI NE KHADIJA GOMBE ALLAH YA HUCE GAJIYAR TAFIYA*

*MY BOOKS*
*NANA JAWAHEER*
*GIMBIYA HAKIMA*
*SANADIN LINK*
*A GIDAN HAYA*
*B'ARAWO NE PAID 300*
*IZZAH KO MULKI*
*SADAUKIN BURHAAN PAID 400*
*A SANADIN SOYAYYAR SHAN MINTI*
*BAYI MA Y'AY'A NE*
*BAN SAN IN DA SUKE BA PAID 400*
*DAUKAR FANSAR BUDURCINA PAID 500*
*BANI BACE PAID 500*
*ALQALAMI*
*HAKA ALLAH YASO*
*BAKIN JININA YA JAMAN*
*QADDARATA*
*LOKACINE*
*BUD'ARDIYAR SOYAYYA PAID 500*
*NIDA UWAR MIJINA PAID 500*
*AND KNOW*
*DA'IMAN ABADAN*

*131-140*
Wani haske ya gauraye man Ido, bansan lokacin da na saka hannu ba na k'are haske Ina mai rintse idona sosai,dan rabon da naga haske ko ya yake har mantuwata ta manta dan ban san ta ko wace hanya aka biyo  aka shigo dani dakin da aka ajiye ni dakine mai dahun bala'i....Tun a cikin motar suka daureman hannu da Ido ba abunda nike gani,dan a rana d'aya sau d'aya tak ake bani ruwa shima ba dan na koshi ba dan ana bani na fara sha bani makalwa biyu zuwa ukku za'a anshe ruwan kafin kuma mai kawo man ruwan ya fita sai ya watsa man ruwan sanyi mai masifar sanyi inajin har da kankara a jikinshi haka zai watsaman sanann ya ficewarshi.

Ba dai a tab'a buguna ba tunda aka kawo ni kuma ba wanda ya tab'a kama Koda da hannuna ne amman kullun rana sai an watsaman ruwan kankara sau hudu a rana duk mura tabi ta kamani ga ba abinci dan sau biyu ake bani abinci a sati.

Cire hannuna akayi daga saman fuskarta ana haskeman fuska da wata irin fitila mai bala'in hasken tsiya cikin wata irin kaukausar murya mutumin da ke tsaye gabana yace.."maza taso."

Tasowa nay Ina mai yin kasa da kaina dan ko kallonshi bani son nayi saboda wani irin basamudan gardi ne gashi baki jikinshi ba ya wuce tunanin mai tunani sai kace ana shafa mashi bakin mai tsabar baki...Tsaki yayi yana yin gaba,tsaye nayi ban dai bin shi ba kuma ban motsa daga tsaguwar da nike ba,waigowa yayi yana buga man wata muguwar tsawa yana cewa.

"Idan har kika kuskura nazo wajen nan sai nayi kuli kuli dake a wajen nan."

Da sauri nabi bayanshi ina  mai  dode kunnena haka na kama bin bayanshi wasu kofofi ne muka kama fitowa Ina lissafawa sai da muka wuto kofar tara a ta gomance na ganni cikin wani katon parlo cike yake da kujeru royals sai kuma wata katuwar plasma da take manne a bango tana aiki ita d'aya...Shuru parlon yake ba abunda ke tashi sai sanyi Ac da kuma karar Tv,wata kofa ya nuna man yana cewa.

"Bayi ne maza shiga kiyi wanka minti goma na baki."

Ya ida maganar yana duba agogon hannunshi ba,da sauri na nufi kofar da yake nuna man na tura na shiga a hankali babban toilet ne wanda ba abunda babu na amfanin toilet a ciki kayana na cire Ina had'a ruwan zafi na fara gasa jikina dan wani irin sanyi nike ji ga kuma mara da nike fama da ita.

Ido k'afe yake babu hawaye ko d'aya,dan nayi kukan har na daina na bar ma Allah lamarina,brush na gani sabo fal aikuwa na dauka na matsa makali na wanke bakina tas sanann nayi wanka na wanke jikina tas sai kamshi nike.

Wani irin dadi naji ya mamaye ni da nayi wanka kayana ma maida Ina fitowa,ko kallona baiyi ba yayi gaba Ina binshi a baya wata hanya ta daban ya bi dani nidai nawa Ido Ina addu'a a zuciyata,dai dai wata kofa ya tsaya yana cewa.

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now