SANADIN SHI 51-60

39 2 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*51-60*

Jum!Wasi tayi tana kallona tama kasa yin Koda motsi,wai Ahmad nike so,so fa to wani irin so nike mashi?shin anya kuwa ba hannu Ahmad ya saman ba,ya za'ayi zance Ina son Ahmad bayan nasan waye shi,nasan k'asungumun dan'iska ne mazinace dan tasha,gaskiya ruwa baya tsami banza akwai wata a kasa ,banza bata kai zomo kasuwa girgiza ta nayi Ina kwabe fuska nace.

"Haba mana Wasi ya na kawo maki damuwata kin kuma sani gaba baki ce komai ba sai kace kin samu tv." Sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa.

"Dole na zarara maki Ido Hauwa,abun naki ne ai naga kamar bana hankali ba gaskiya."

"Kamar ya ba na hankali ba?ni karda nayi kuka dan Allah ki bani shawara mafita nike nema,wallahi ji nike Ina sonshi fa." rintse idonta tayi tana bude shi tana cewa."Hauwa kanki d'aya kuwa."? D'aga mata kai nayi Ina cewa."kwarai kuwa ras nike."girgiza ni tayi tana cewa."Anya kuwa kanki d'aya Hauwa'u Abdullah jibir." Full name dina ta fada,sake d'aga mata kai nayi kawai bance mata komai ba,itama bace man komai sai da ta kusa 10min sannan ta fara cewa.

"Tambaya d'aya zan fara yi maki anan,Hauwa mai kika gani a wajen Ahmad da har kika ji kina son shi."? Dan shuru nayi Ina duba character dinshi,sai kuma nace.",Gaskiya ni babu nidai kawai hakanan naji sonshi fa." Murmushi tayi tana kama hannuna tace."Dan Allah Hauwa ki rufamana asiri ki fidda son bawan Allah nan a zuciyarki,Kinga dai bai da hali ke infact ba sai na tsaya gaya maki waye shi ba kinsan dai waye shi baku dace da juna ba sam,karda ki biye ma so ki dawo kina da na sani,ki zab'a ma yaranki uba nagari dan Allah."

Shuru nayi kawai Ina kallonta,jikina mutuwa yayi da tace na zab'a ma yarana ubana ma gari karda na biye ma son zuciya,yanzun idan na auri Ahmad ya dawo yana aikata halinshi ko kuma yayi fiye da haka.duk abunda kayi sai anyi ma naka kenan duk wanda Ahmad yayi ma fyade sai anyi ma yaran da na haifa dashi!?zuface ta keto man take naji ya fice man a rai,dan inason yarana suyi alfahari da uban da ya haifesu,ba suyi kuka da dana sanin haihuwarsu ba.

Cigaba da cewa Wasi tayi.."tun wuri kiyi ma kanki karatun ta natsu ki watsar da soyayyar Ahmad tun dare baiyi maki ba wallahi,bance kiso Yaya Auwal ba tunda baki sonshi ba'a dole shima nasan ba zaiso ki aure shi baki sonshi ba, dan haka sai ki natsu kiyi mashi magana ta hankali ki nuna mashi ba zaki samu damar aurenshi ba dan baki sonshi ba,yayi hakuri Allah ya bashi wata,kema yayi maki addu'a Allah ya baki wani haka ya dace kiyi a gani na."

Murmushi nayi Ina cewa."Allah ya zab'a mana abunda yafi alkhari,Wasi ki sani zan bar Ahmad ba dan ban son shi ba,zan barshi da zab'a ma yarana ubana na gari,shi kuma Yaya Auwal maganar gaskiya Wasi na kasa jin sonshi a zuciyata da gaske nike maki,dan haka bayan bikin Yaya Teemarh zanyi magana da shi zan gaya mashi gaskiya kawai karda a kama wasa babu murmushi."

Furzar da iska tayi tana cewa. "Allah ya zab'a mana abunda yafi alkhari,sai dai ba zan boye maki gaskiya ba Hauwa,naso ki da Yaya Auwal naso ace kin zama mallakin shi *DA'IMAN ABADAN* ,ba dan komai ba sai dan kyaun halayenshi da natsuwarshi da kirkinshi,Hauwa wallahi banson kizo daga baya kina cizon yatsa na rashin mutumin kirki,nidai da zaki bi shawarata da kin kara bashi dama kin gani ko zuwa gaba za'a dace banson ayi lost din mutumin kirki irin Yaya Auwal gaskiya."

DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)Where stories live. Discover now