💖💫RUDANI💖💫 1

687 74 32
                                    


All thanks be to Allah The Almighty, for granting me the knowledge and privilege to think and start this story, may He prosper and give me the ability and opportunity to see its end.




Abuja, Nigeria📍

      Albaaz Residence.

Jikin wani gida ne naga an rubuta Albaaz mansion, hakan ya bani daman shiga domin naga abubuwan dake gudana ah cikinta, gidane babba, dan yanda aka tsara gidan kaman ah abroad.

Parlor ne Babba wanda zai iya daukan kujeru set uku zuwa hudu, manyan electric incense burners na turaren wuta a kowani angle, kamshi ne kawae ke tashi a wajen da ya hadu da sanyin Ac, takun takalmin akeji qwas-qwas na saukowa daga sanan bene alamu mace ce "Aameer as I said I'm sorry bani sake bata lokaci, amma karka hanani zuwa wajen Mami" tayi stating kaman zatayi kuka, sai anan yadan tsaya hakan yasa na kare masa kallo, lalle Aameer saurayine dogo mai kyau'n gaske kuma yanada haske sosai, koh wata budurwa zataso ace Aameer nata ne halan shiyasa yake ra'ayi "Xeenerh ni driver'n kine?" Ya fada jin yanda ta dage sai ya kaita gun Mami, kuma fa sarai chan zashi daukanta ne baison yi "No you're not, and you will never be"ta fada tana dan murmushi dan ta gane ra'ayi kawae yake mata amma zaije da ita, fara ce tanada kyau sosai ajin farko wanda koh wani namiji zaiso, tana da shape Ma'sha Allah, hanci har baka, ga gashi har gadon baya, kasancewar ba dan kwali a kanta, veil ne tayi rolling kuma ba me kauri ba hakan ne ya bani daman ganin gashin kan nata, cigaba da tafiya yayi sannan ta bishi ah baya saidai kafin sukai ga exit door yaji ance "Hey Mr. Aameer" ta fada tana sa ribbons akanta, fara ce tanada kyau sosai ga gashi dan naga da kyar take kamasa cikin ribbon in, wasu kan ce tafi Xeenerh kyau saboda farin fatarta yafi na Xeenerh fita, while wasu kan ce Aa Xeenerh ta fita kyau "Hell no" ya furta a hankali dan yasan itama shiriritan zata masa sannan ya juyo calmly yace "Any prob?" Ya fada fuska ba yabo ba fallasa "Erm.. where are you guys heading to? naga sai sauri kuke" ta fada sannan ta karasa wajen fridge ta ciro bottle water "Ina ruwanki?" Ya tambaya yana binta  da dirty look "Ashphert gidan Mami zamu, you can talk on when we are back" Xeenerh ta fada sannan ta fice "Yanzu gidan Mami zaku shine you don't bother telling me despite cewan da nayi zanje tun jia" ta fada tana kallon Aameer kaman zatayi kuka "Look im sorry Ashphert, koh jiya ma ba k'i nayi ba kawae aiki ne yamun yawa" ya karasa wajenta tare da rike hannayenta guda biu "Yanzu kije ki shirya, we're waiting for you in the car and don't be late kinji?" Kai ta gyada masa sannan ya mata peck ya fita. Yana fita parking lots ya samu Xeenerh tsaye dan batason which of the cars zai dauka ba, saboda motoci ne gidan har rumfa uku and each contains 5 making it 15, tsaki yaja ganin tana tsaye danshi gani yake tasan motan dazai dauka, dan kuwa tunda yasai Jeep avenger ya dame su dashi, bayi daukan koh wani mota sai shi "Aameer baka mun adalci ba, cewa kayi fa kar na bata maka lokaci, amma yanzu dake Ashphert ce ta tsaya yi maka magana ae gashi kai kasa nayita jira, ana adalci dai" ta fada tana pouting mouth "Matsayin Ashphert daban naki daban" ya fada sannan ya shiga motan, tsaki taja ciki-ciki a yayinda ta bude gaba ta shiga, shiga taga yayi amma bai ja motan ba a hakan bakinta bayi shiru ba take ce masa su tafi mana nan fa yace mata Ashphert yake jira ae itama zataje "Lalle Aameer ka raina mun hankali, wlh toh ni ba yanda zanje" ta kama handle in mota zata bude yasa lock "Zuwa ya zama dole" ya fada da witty smile, shiru tayi kawae ta fara hawaye amma koh a jikinshi, ita kuma abunda yafi kona mata rai shine fadan da yayi ta mata wai ta bata lokaci sai gashi yanzu Ashphert take jira, mutumin da ya tsani jira a rayuwanshi fiya da komai, shiru tayi batace komai ba nan hawaye ya taru idonta daidai da shigowan Ashphert tana basu haquri as she's a bit late, koh kallon ta Xeenerh batayi ba, nan securities suka bude musu gate suka fice, hakan ya bani daman karewa gidan kallon dan ba karamin mai kudi bane yayi gidan duba da yanda securities ke kai kawo cikin gidan.

Maiduguri
              8:14pm
Kofa ne yayi kara kasancewar sa security door hakan ya bani daman ganin wata ta shigo tana tafiya kaman baza tayi ba "Sannu da dawowa" wata rike da basket na Apple ta mata, kai kawai ta gyd'a sannan ta haura sama "Kyaji dashi dai, mutum kullum halin yau daban na gobe daban" Munnirah ta fada ciki-ciki sannan tayi kitchen dan ajiye basket in dake hanunta, bayan ta shiga daki ta fara rage kayan jikinta, tana gamawa ta nufin yanda towels ke rataye ta dau blue one ta shige toilet bada jimawa ba ta fito, tana da kyau sosai dan she's not comparable to Xeenerh and Ashphert saboda duk ta fisu kyau dan gashin kanta ma yafi nasu cika da tsayi, nida an barni zance ba kasar mu daya ba lol, shafa manta tayi cike da kwanciyar hankali sannan ta dau khumra tabi jikinta dashi back to body sprays, and after wearing spongebob nightgown nata ta dau perfumes nata masu tsada ta feshe jikinta dasu, daukan sleeping mask nata tayi har zata sa ta fasa nan ta ajiye sa gefe, kan comfy California bed nata ta hau nan ta dau waya tayi dailing wani number ba da dadewa ba aka daga "Hello Babe" Xeenerh dake cikin mota suna hanyan dawowa ta fada daga dayan bangaren "Hi" ta amsa cikin siririn muryanta mai dadin sauraro "How are you guys there? will be coming back tomorrow In Shaa Allah" ta fada kaman wacce batasan magana "Yayy, Ilhaam are you sure?" Xeenerh ta tambaya, Ashphert kuwa jin ance Ilhaam da sauri ta fauce wayan hanun Xeenerh ignoring dirty look in da Xeenerh ke binta dashi "You cried?" Ashphert ta tambayi Ilhaam jin muryanta yayi wani iri, ignoring question in Ilhaam tayi sannan tace "Ash zan dawo gobe In Shaa Allah, I missed you all" tayi maganan cikin murya mey dadi "Ilhaam baki amsa..." Ashphert bata karasa ba Ilhaam tace "Im hanging" nan ta kashe wayan abunta, mikawa Xeenerh wayan tayi tare da cewa "It's like Ilhaam has cried Xeenerh" karba Xeenerh tayi tare da amsawa "I thought so, ashe bani kadai bace" Ashphert zatayi magana Aameer ya katse su "Kun fiye gulma, banda iyayi daga kiran waya kuce tayi kuka?" Ya fada still ba walwalan kirki a fuskan sa "Toh Aameer kar mu fadi gaskia?" Ashphert ta fada tana murguda karamin bakinta "Yau ta saba kuka over silly things? so meyasa zaku damu?", "Barrister bamu sakewa" Xeenerh tayi saurin fada ganin ransa nason baci. Koh da suka karasa gida Aameen kadai suka gani zaune ah main parlor dama sunyi tunanin ya dawo "Guys daga ina haka?" Ya tambaya yana daga one of his eyebrows daya cika da gashi kaman na mace so Masha'Allah "Daga wajen Mami" Xeenerh ta fada calmly sannan duk suka karaso suka zauna "Ummi bata dawo ba koh?" Ya sake tambaya "Eh bata dawo ba tukunna" Ashphert ta amsa masa "Ke gimme some coffee" Aameer ya fada yana wani yamutsa fuska, kallonsa Xeenerh tayi kaman zatayi kuka, ganin haka Ashphert tace "Xeenerh rest, barin basa" nan ta mike dan sarai ta lura Xeenerh ce baiso ta huta "Toh wai yaushe waccen yarinyan zata dawo, duk ba ita ta dau Munnirah ba" Aameen ya tambaya "She called, tace zuwa gobe dai" Xeenerh ta amsa "Sun fasa yin week in kenan?" Aameer ya tambaya jin wai gobe zata dawo "Toh wai Aameer harka tambaya, after knowing the fact ba shiri suke da Aunty Khadie ba?" Tashi Aameer yayi yabi Ashphert kitchen leaving Xeenerh da Aameen dan bayida amsan tambayan nata "Im missing you Babe" Xeenerh ta fada ganin Aameer ya tashi sannan ta dawo kusa dashi "I missed you more" Aameen ya amsa "Yau throughout ban ganki ba" ya sake fad'a "Mami tace na gaishe ka, tunda kaki zuwa", "No zanje mana, 2 days aiki yamun yawa ne", "Toh lovers, ina magana kun shareni" Ashphert ta fada saboda neman magana "Bawani maganan da kikeyi yanzu kikazo ae naganki" Xeenerh ta amsata, Aameer ne ya zauna yana sipping coffee nasa nan yace "Captain, Doctor zai shigo gobe fa" kafin Aameen ya amsa Ashphert ta chapke "Dama yayi zaman sa, zai dawo ya fara yiwa mutane anyhow" kallonta Aameer yayi bai amsa ba "Kai Ashphert, Anwaar fa baida matsala kawae dai baku shiri ne" Xeenerh ta fada tana dariya "So Xeenerh tell me dawa Anwaar yake shiri ah gidan nan? Bayi shiri da kowa ah duk duniyan nan sai waccen 'yar iskan yarinyan" Ashphert ta amsa da bacin rai "Kun gane? In zagin Teemerh zaku fara anan ku tashi ku bani waje" Aameer ya fada fuskanshi ba yabo ba fallasa yana mai cigaba da sipping coffee nasa, wani kallo Ashphert ta bishi dashi hakan yasa shi yin murmushi dan yasan abunda take nufi, dariya sosai both Aameen da Xeenerh suka fara suma, haushi taji ta tashi tabar wajen nan Aameer yayi saurin tashi ya bita, aka bar Xeenerh da dariyan situation in, ah daki ya sameta tana kwance abunta "Look Ashphert..." bai karasa tace "Out of my room" maimakon ya fita sai tsayawa yayi folding arms nasa yana kallonta, tashi tayi duk tunaninta ya fita sai gani tayi yana kallonta, zatayi maganan yace "Shh" bata rai tayi "Do you love Teemerh?" Ta tambaye sa "You know I don't, like how can I?" Ya fada da dan murmushi "Ae naga yanda kake backing nata ne" ta fada tana hararansa kasa-kasa "Im not backing her Ashphert, amma yanda kike mata is too much, ba ita ta causing komai haka ba" ya fada sannan ya karasa "Just put it in mind cewa bazan taba san Teemerh ba Aameer" ta fada masa gaskiya "Okay, I understand how you feel" ya fada dan ya calming nata down, karasowa tayi sannan tayi hugging nasa "You are the best" ta fada a hankali, hugging nata back yayi kafin a hankali tayi breaking hug in "See you later" ya fada sannan yayi waje, murmushi tayi kafin tayi bathroom danyin wanka, bayan ta fito taga missed call nan tayi calling back, ce mata yayi gashi ah compound in gidan su tace toh gata fitowa.


****
Karasawa tayi wajenshi suka gaisa cike da nishadi, yanada kyau sosai, da ganin sa kasan kudi zasuyi magana "Ashphert ya kamata ki shawo mun kan Ilhaam, kullum sai cewa kike nayi haquri" haushi taso ji dan ta lura baida haquri "Ahmad meyasa bakada haquri ne? Ilhaam fa er uwatace ni kadai nasan halinta saboda haka ka bata space zata fara sanka a hankali lokaci ne baiyi ba, you know I can't force her" ta fada masa gaskia dan ba yanda za'ayi tayi forcing soyayyah "Ashphert a gaskia in ban auri Ilhaam ba banajin zan iya wani aure arayuwa ta" tace "Toh ka shigo ciki muyi magana, su Aameen suna ciki" kallonta yayi yace "Ilhaam ta dawo kuwa?" Girgiza kai ta fara alamun Aa "Nope" ta bashi amsa saidai batace masa zata dawo gobe ba "Look sauri nake, tunda bata dawo ba kawai shikenan" ya fada yana kokarin shiga mota yaji tana magana "Toh ka kara haquri Ahmad" yace "Kullum haka kike fada amma koh daukan wayana batayi, inda tana dauka da zanna dauke mata kewa har randa Allah zaisa ta fasa sona" murgud'a baki tayi ta hade rai "Toh karka yi haquri, force her if you can, yanzu ni zanje na yi bacci dan inada abubuwan yi da yawa in Allah ya kaimu gobe" ta fada sannan ta juya "Haka matan Maiduguri ke yiwa guest nasu koh zaman Abuja ya bata mana ku?" ya tambaya, gane neman magana yakeyi batace komai ba tayi murmushi "Goodnight" ya fada sannan Ashphert tace "Take care" nan ya daga mata hanu, tana juyawa taga Aameer na karasowa, a very busy someone da bayi zama waje daya, bata bi ta kansa ba ta wuce abunta "Hey Man me kakeyi yi anan?" Cewar Aameer lokacin ya karaso, hanu Ahmad ya basa suka gaisa "Wai duk matan da suke cikin gidan nan sai ka bisu da kalmar so ne?" Aameer ya tambaya eager to know wajen wa Ahmad yazo "Ilhaam was the one before and now Ashphert?" Ya sake tambaya "No Barrister ba abunda kake tunani bane, haryanzu Ilhaam nakeso na kira Ashphert saboda tamun convincing Ilhaam me, believe me Aameer I really wanna marry her" Wani shedanin dariya Aameer yayi "Kuma kana tunanin Ilhaam in zata soka har ta aure ka koh?" Aameer ya tambaya still yana dariya "With time, ni nasan hakan zai faru" Ahmad ya fada with courage "Ahmad inaga kaman ka manta ni Ilhaam takeso koh?" Aameer ya fada yana nuni da kansa, Ahmad ne yayi wani witty smile yace "That was then Aameer, wake up and face the world, Ilhaam bata sonka" Aameer yace "Koh ka manta Ilhaam qanwata ce koh? I will just tell our elders Ilhaam nakeso na aura, shikenan sai a mana aure, kallonsa Ahmad yayi sannan Aameer ya cigaba "Karka damu inso kakeyi ka auri Ilhaam I can make a way for you, I will play and ditch her again saboda na tabbatar maka da cewa no matter how many times I go back to her, she will accept me saboda ni kadai takeso duk duniya" Ya fada yana kama kafadan Ahmad, dan dariya Ahmad in yayi sannan yace "Then let's make a deal, ni nasan Ilhaam bazata so ka ba, kota soka bazata aure ka ba saboda there was someone before you a rayuwan ta" smirking Aameer yayi yace "And that someone will marry someone else not her" Aameer ya fada da murmushi "Okay fine sai na jika" Ahmad ya fada yana mamakin yanda suka maida Ilhaam kaman ball, wannan ya buga tanan wannan ya buga ta can.


How's this page guys?💖🩵


Guys team Ahmad koh Aameer?

Team #RUDANI!



PS: am not a writer, just writing RUDANI as it is one of the books I want to read but it's not yet been written. You might see the fragments of yourselves from it. Always remember that You can be Ilhaam, Ashphert, Teemerh, or Xeenerh- it's always a choice to be good💫💖

_The Confusion💫💝

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now