💖💫RUDANI💖💫 35

160 24 27
                                    


Ah washegari Ummi ta dawo, kaman yanda sukace kuwa Ilhaam ta koma wajenta, batayi fada jin za'ayi auren cikin sati biyu ba, murna ma tayi abunta dan kuwa tafi kowa san abun, abunda bataso guda daya shine maganan UK nasa, nan fa ta kasa haquri ta aika ah kirasa, zuwa yayi kaman kullum cike da ladabi ya zauna daga ta k'asa, saidai fa kana ganin sa zaga gane cewan yana cikin farin ciki, badan komai ba kuwa sai dan Ilhaam will be his own in few days "Anwaar amma dai kasan tanada hakkin sanin ba'a nan zata zauna ba koh?" Tayi maganan very calm as usual "Erm.. Ummi dama ita Ilhaam bazata yarda ta bar nan daga aure ba, she is not her absolute self har yanzu, tana cikin en uwa zaifi" kallon sa da mamaki tayi jin abunda ya fada "Ban gane abunda kake magana akai ba, dan shiru yayi yana rephrasing maganan sa, sai ah lokacin ya gane abunda ya fada tuni ya hade mata karya "Ummi dama saboda tace bazata bane as she don't like going overseas kuma kinsani, shiyasa nake ga ya dace abari sai lokacin da ta yarda" kallon sa kawai Ummi tayi amma ta gane sarai karya yakeyi dan kuwa tana ganewa idan Anwaar yana karya "Toh kai kuma ya stand naka achan?" Tayi maganan still glaring at him "Yanzu in na koma zanyi resigning na karbo transfer" ya fada ah takaice "Da yafi, amma ace zaman ka kanen acan, gwanda ma yanzu da zakayi aure" shiru yayi bey sake cewa komai ba "Zaka iya tafiya" ta fada sannan itama ta tashi tayi sama, tashi yayi zuwa daki, dan kuwa tunda Ilhaam ta dawo toh fa shima ya dawo, yazo shiga yaga Ilhaam, yana kiranta taki tsayawa kawae tasa gudu, beyi kokarin binta ba ganin tayi dakin Ummi, saboda yasan koh yaje ba shiryawa zasuyi da Ummi ba dan Ilhaam ta fishi samun waje cikin zuciyan Ummi, yana komawa daki yaga several missed calls na Fatima, he wonder what she wants telling him haka, zama yayi kan womb chair yayi calling back, tana dauka ta fashe masa da kuka, dan rufe ido yayi ya bude a nitse dan bayisan kukan mace "Fatima" ya kira sunanta a nitse "When are you coming? We need to talk" ta fada cikin kukan "Before any of that calm down" ya fada a nitse, shiru tayi tana jiran taji mey zaice "Tell me now, mey ya sameki?" Ya tambaya jin tayi shirun kaman yanda yace, kasa magana tayi tana tunani rainin hankali irin na Anwaar, shiru tayi kawae ba magana sai jin an fauce wayan tayi, tana dagowa taga Mum ta kashe wayan, a razana ta mike "Ke Fatima mey yasa baki abu da tunani?" Shiru Teemerh tayi tana fiki-fiki da ido "Baza ki sake kiran saba harsai anyi aikin nan, in kuma so kike ki bata mana shiri sai ki fada naji "Bazan sake ba Mummy" ta fada cikin nutsuwa, harara Mum ta watsa mata kafin ta juya zata fita sai ganin Lily ta turo kofa tayi "Miye ne wai?" Teemerh ta fada a tsawace "Munerah is here to see you" harara Teemerh ta watsa mata "Wai ke baki iya kiran sunan kowa ba sai naku koh? Munnirah ce ta zama Munerah?" Shiru Lily ta mata dan bawani fahimtar mey Teemerh tace tayi ba, saboda batasa English ba "Tell her am coming" ta fada ganin Lily tayi shiru tasan bata fahimci Hausan sosai ba, dan sunkuya wa tayi tace "Okay Miss" sannan tayi waje, haushi sosai Teemerh taji yanda Lily ta addressing nata da Miss, da Anwaar ba dan rainin wayo bane da yanzu saidai Mrs, ta fannin Anwaar kuwa jin ta kashe wayan bey sake bi ta kanta ba, alwala ya dauro ya wuce masallaci


Sauka tayi ta samu Munnirah dake zaune zaman jiranta "Ke da nace kizo jiya?" Dan juyawa Munnirah tayi, ganin ba kowa ta bude baki zata fara magana Teemerh ta tsaidata "Ke in zaki zage kimun magana ina jinki, kap gidan nan ba wanda ya isa ya samun kunne in zanyi magana" ta fada tana hararan ta "Toh yanzu dai Ilhaam ta koma wajen Ummi, shi kuwa Yaa Anwaar ya bita" Teemerh kaman tasa hanu akai tayi ihu saboda kishin abunda Munni ta fada "Wai miye Ilhaam take da wanda bani da?" Ta tambayi Munnirah ba tare da jiran jin amsa ba ta cigaba "Toh wlh saina koya mata hankali" ta fada tana huci cikeda kishi "Ni yanzu ki fada mun miye ya kawo ki dan na fara shiri zamu Niamey" ba tare da sanin mey zasuje yiba Munnirah tace "Kinada Visa?" Wani kallo Teemerh ta watsa mata "PR visa nake da" ta fada cike da isa, banda Munnirah da rainin hankali Visa Niger har wani wahalan samu nema dashi "Toh ke kuma miye ya hadaki da Niamey?" Kallonta Teemerh tayi jin yanda take wani tambayanta kaman zata bata sako "Toh wai ke ina ruwan ki ne? Shikenan ba za'a je duba 'yan uwa ba?" Teemerh ta fada cike da nadaman fadawa Munnirah zasuyi tafiya "Naga dai ita Mum er T-Chad ce, toh mey ya hadaki da Niamey?" Ta sake tambaya "Eh lalle Munnirah kin samu kai, toh tun wuri ki fita idona na rufe" ta fara masifan da baida amfani "Allah ya baki haquri, toh yaushe ne tafiyan naku?" Tace "Next week dai" ta fada tana wani yamutsa fuska "Yanzu duk effort in da nayi making ya tafi a banza sai ma santa daya karayi" Teemerh ta fada harda biting finger "Haquri zakiyi ae, dama tare kika gansu, sai kiyi addu'a koh a ta biyu ki shiga" Munnirah ya fada ah takaice "Munnirah ga kofa fa" Teemerh ta fada tana mata nuni dashi "In lokacin tafiya na yayi ae zan tafi" ta fada kasa-kasa gudun kar Teemerh ta jiyota "Keda zaki sympathizing ina kina fada mun maganan banza" ta fada, ganin Rocky (Dog pet) nata da tayi ne yasa ta yin shiru sannan ta dauke sa "Missed you Rocky" ta fada tana masa wasa "Woo, Teemerh Rocky na nan?" Munnirah ta tambaya da mamaki "Yana nan mana, I posted him yesterday" ta amsa this time a nitse "This is adorable, just as Yaa Anwaar's cat" Munnirah ta fada a nitse tana murmushi ganin yanda Teemerh keyi da karen, saurin dagowa tayi ta kalleta jin abunda ta fada "Anwaar has a cat?" Ta tambaya da mamaki dan bata taba sani ba "Yeah he had Rabab" ta bata amsa
"Toh yanzu fa?" Teemerh ta tambaya tana shafa gashin jikin Rocky mey laushi "He gifted it to Ilhaam, after their break up ta kaiwa Ummi ita kuma, so kinsan Ummi na tsoro ita kuma...." Nan Munnirah taja tayi shiru "Sai akayi yaya kuma?" Ta tambaya jin Munnirah bata karasa ba "With Maa Suhaila I think" kallonta Teemerh tayi sannan ah hankali ta maimaita sunan "Rabab" kallon Munnirah tayi ganin yanda take bin Rocky da kallo "He also like dogs?" Girgiza kai Munnirah ta fara alamun Aa dan kuwa ta gane wa Teemerh take nufi, tsaki Teemerh tayi jin wae haryanzu Anwaar baisan kare, hanu tasa ta zare chain in dake wuyan Rocky tare da sauke sa kasa a nitse "I love you Rocky, but I love Anwaar the most" ta fada sannan ta wani juya, kin tafiya Rocky yayi ya fara tsalle yanaso Teemerh ta daukesa amma sai folding arms nata tayi "Munnirah in kinaso ki dauka" baki sake ta tsaya kallon Teemerh da neman karin bayani, baki na rawa tace "Teemerh kina nufin bakiso kuma?" Dakai Teemerh ta bata amsa tare da maimaita wa Munnirah in tanaso ta dauka "They hardly like dogs" kallonta Teemerh tayi sannan tayi murmushi jin abunda ta fada "Shi yasa nace ki dauka, I will be one of the Albaaz soon, tunda basu so mey zanyi dashi?" Ta fada harda hararan Rocky koh miye nasa oho "Ya Allah" Munnirah ta fada ganin Ikon Allah "Teemerh ki dauki Rocky naki, yana sanki" ta fada ganin yanda Rocky kebin Teemerh "I will always love Rocky Munnirah, amma sai ki fahimta, tunda na rabu dashi ba wanda bazan iya rabuwa dashi akan Anwaar ba, I will get a cat and name him/her Rabab too" ta fada harda murmurshi "Duk kina yin haka saboda Yaa Anwaar ne? Toh bey ma san kikayi ba" tunani ta fara tun farko ma mey takeyi da kare ba kuliya ba? Chan ta girgiza kai "Koma miye ki fada, I will get a cat, bazai yiyu ace Ilhaam nada ni bani da ba" ta fada factly "Itama fa yanzu Rabab is not with her, as I told you na gidan Ummi" wani harara Teemerh ta watsa mata tana tunanin ya za'ayi Anwaar yaji yana san wata wanda ba ita ba "Gani fara sol Munnirah" tayi maganan tana nunawa Munni hanunta "Ba abunda banida shi" sa hanu tayi ta zame hulan dake kanta, dogon gashin ta mey kamshi da kyalli ne ya sauka gadon bayanta, sannan ta mike tsaye ta fara juyawa a gaban Munnirah dake binta da ido, saida ta gama shirmen ta kafin ta nemi waje ta zauna "I lack nothing Munnirah, amma bansan meyasa ya maqalewa Ilhaam ba, yarinyan da batada pride yanzu ma, gani nidai ba abunda ya ragu a jikina" ta fada kaman mey shirin kuka "You are beautiful Teemerh, so as Ilhaam, kuma duk abunda kike dashi itama tanada, haske kawae kika fita shima ba sosai ba, tunda ita nata bey fito sosai ba, kuma ke farin ki ae ba irin na mutane bane" wani kallon banza Teemerh ta bita dashi "She still get pride?" Teemerh ta tambaya sai kuma ta fara dariya "Teemerh, shifa Yaa Anwaar indai kina Ibada toh kin gama masa komai" shiru Teemerh tayi tana so taji sauran gist in "Shawara zan baki, koh da ace zaki samu ki shiga gidan nasa toh fa sai kin rike addini, make sure kina tsafta, yess I knw kinayi amma sai kin kara, yana san koh ina da kamshi dan koh kitchen ya shigo yaji bayi kamshin daya kamata toh sai yayi fada" dan murmushi Teemerh tayi "Toh ae yazo gidan sauki, kinsan dai turare ba kallan wanda ba mu dashi, harna tsafi in yana so sai na nemo masa, maganan Ibada kuma ae sallah ce, akwae Muslim da ya isa yace bayi sallah?" Ta tambayi Munnirah da tayi shiru kaman mumina, kallonta kawae Munnirah tayi dan tasan Teemerh bazata fahimci abunda akeso ta fahimta ba dai tayi witnessing, tasan karshe Teemerh will end up suffering indai ta biye na Anwaar "Teemerh kin iya girki?" Kallonta Teemerh tayi ta yamutsa fuska dan kuwa bata iya ba "Toh wa zai na muku abincin?" Dan kama baki Teemerh tayi, duk ita ta manta ana girki wa miji, abunda ya kara tsaya mata arai shine Anwaar is a complete private person, zaiyi wuya aga maid gidan sa saboda bayison wannan, he want to be alone "Toh ae dole na koya, dan Allah koh Anwaar yanaso koh bayiso sai ya soni nima" tana fada ta jawo waya dan shiga YouTube duba recipes and so on "Ni zan tafi" Munnirah ta fada sannan ta mike "Ke wannan saurin har ina?" Ta fada sannan tasa hanu ta dauki Rocky da har lokacin yana wajen "Baki so koh?" Ta kara tambayan Teemerh, gyada mata kai Munnirah tayi sannan ta fara tafiya "Driver'n zai dawo ya dauke ki ne koh cab zaki hau?" Teemerh ta tambaya ganin da gaske tafiya zatayi "Taxi indai, bance ya dawo ba" daga kai tayi kan wayan ta kalli Munnirah "Toh ki tsaya na sauke ki, zan fita" ta fada sannan ta mike da Rocky tayi sama, bada jimawa ba ta sauko ita kadai sai veil nata

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now