💖💫RUDANI💖💫 3

317 63 17
                                    




⚠️
DRINKING IS INJURIOUS TO HEALTH
Alcohol can cause high blood pressure, which increases your risk of having a heart attack or stroke.)


Mey zata gani? Gawan Baa ne kwance a tsakiyar dakin jikokinshi na kanshi, nan hankalin kowa ya dawo kanta jin alamun an shigo "Aaaaa ba gaskia bane, Baa be rasu ba, dazu na rabu dashi" ita kadai take sumbatu "Baa ka tashi, dan Allah ka tashi ka fada musu gaskia, Yaa Abu dan Allah mana" ta fada tana kokarin tashi taje wajen Yaa Abu, tashin daza tayi ne wani jiri luuu ya kwasheta tuni Anwaar dake kusa da ita ya riketa tare da kiran "Ilhaaaaam" wanda rabon da yayi hakan ya manta, Dr. Shareef da yazo jin labarin rasuwan Baa ne yayi treating nata saboda yau Dr. Anwaar is very weak, ba'a gama wannan ba aka kira Yaa Mahfouz sanar dashi rasuwan Mami sakamokon poison da taci wanda 'yan sanda suke bincike akai yanzu "Innalillahi wainna ilaihi raji'oun" kawai ke tashi a dakin, su Xeenerh abun tausayi ita da Ashphert, kuka kaman zasu cire ransu..... Bayan sati biu aka gama bincike yanda aka tabbatar mai aikin su ne tasa mata poison a abinci kuma anyi-anyi da ita ta fadi wa ya sata tace ta gwammaci ta mutu akan ta fada, nan 'yan sanda suka kamata.

Rayuwa ta cigaba kasan cewar Allah ya samana mantuwa, Ilhaam ta ware ta fara rayuwanta kaman yau da kullum, Ashphert kuwa ta cigaba da kule kulen samaruka dan batasa ran bari ba, Xeenerh da Aameen kuwa soyyayyarsu suke xubawa kaman ba gobe, Anwaar kuwa sun rokeshi kar ya koma harsai anyi bikinsu kuma ya amince

****
Zaune suke cikin wani mini living room wanda ya mugun haduwa da kuma kamshin da yake fitarwa, vintage sheepskin armchair ne ke wajen sai one 4 seater, Walton marble fire daga mazaunin sa, sai modern rustic rugs a kasa, coffee table daga gefen Anwaar, double hung windows da blackout curtains, J- Geiger windows daga dayan bangaren sai frames da kuma Samsung led TV dake mazaunin sa, saidai ba wanda yaba TV'n mahimmanci, tadi suke wanda Anwaar sai sunyi goma yake fadin daya "Dr yau ba zuwa clinic kenan?" Aameer ya tambaya dan shi tuni ya nemi hutu saboda bikin kaman shine angon "I wanna rest, sai bayan biki in Allah ya nuna mana"
"Oh yessss! Koh kaifa amma kullum kayita fita koh time naka fa bamu samu" Xeenerh amarya ta fada da fara'anta "Nikam ma when are you coming back to Nigeria completely?" Ta sake fada "Allah Xeenerh kapp gidan nan ba wanda ya kaiki neman magana, kema kinsan ae an koreshi ah gidan nan" Ashphert ta fada sarcastically, mai Aameen zaiyi in ba dariya ba, dan yanda Ashphert ta zage tayi neman tsokanan, kallon su da suke ta faman dariya Anwaar yayi baice komai ba ya cigaba da danna wayansa dan ba yau suka saba ba, ana cikin haka Ilhaam tayi sallama ta shigo, tun daga jin muryanta ya mike zai fita "Ahh basai ka fita ba, im not here to sit and chat with you guys, abu zan karba na wuce" wani kallon banza ya watsa mata ya fice abunsa irin itane zata basa umarni? "Kaji dashi dai" ta fada not minding yaji koh kar yaji "Wai baza kibar wannan banzan halin bako?" Aameen da Aameer suka fada in unison dan sun zata abun ya wuce fa "Laifi na kenan?" Ilhaam ta tambaya surprisingly "No guys kun sani fa ba laifin Ilhaam anan, zata hanasa yin abunda ya ga dama ne? mutum da shegen jiji dakai haka wa zai iya dashi" Ashphert tayi supporting Ilhaam "Kuma fa kar kusha mamaki wancan yarinyan ne tazo yasa kuka ga haka dan naji suna waya zata zo" Xeenerh ta sanar dasu, daga ido kawai Ilhaam tayi ta kalli Aameer wane zatayi kuka, ganin haka yasa ya tashi da sauri ya kama hanunta sukayi waje, to her surprise in kuwa Anwaar ta gani da Teemerh sai labari take basa amma koh kallonta baya yi, hankalin sa nakan waya kaman baisan tana yiba "Hey Aameer ina wuni" Teemerh tayi saurin fada ganin zai wuce danshi bai ganta ba Ilhaam ne kadai ta ganta "Oh Teemerh how're you doing?"
"Lafiya qlau"
"Baki zuwa sai yana nan ae" yayi maganan yana riko hanun Ilhaam ganin zata tafi abunta "Ilhaam sorry I was carried away talking to Aameer mun yini lafiya?" Teemerh ta tambaya tana binta da wani makirin murmushi "Kinzo lafiya?" Ilhaam ta amsa sama-sama tuni ta kwace hanunta gun Aameer tayi daki, hakan yasa ya bita, Anwaar kuwa dake zaune baice dasu kala ba dan in Teemerh da Ilhaam na abu ba'a shiga

****
"Toh mai amfanin hakan?" Aameer ya tambaya angrily "Bakomai sorry" ta fada tanaso ta wiping hawayen dake kokarin sauko mata "Ki fada mun gaskia you love him still?"
"Aa I don't know the reason I used to shed tears whenever they are together Aameer, kasan fa Teemerh-" bata karasa ba ta fara kuka, beckoning nata yayi "Shhh is ok I got you Baby" saida ya tabbatar tayi shiru sannan ya bata space dama already suna da wajen zuwa shida Aameen, yana fita yayi daki, fridge ya bude ya ciro wani bottle wanda da gani kasan vodka (alcohol) ne ah ciki. Tass ya shanye kafin ya ajiye, ji yayi bazai iya fita ba hakan yasa ya kwanta daga karshe dai Aameen shi kadai ya fita

***
"Kai amma mutum mara zuciya baiyi ba wlh,Teemerh indai ba dole bane ki tashi ki tafi mana, kin gama surutun naki an kira sallah ya tashi ke kina nan kaman ba'a musulunci aka haife ki ba haba mana kiyi fadawa kanki" Ashphert ta fada cike da takaici "Toh in banda abunki Ashphert mace ce fa, ina ruwanki da rashin sallah'n ta? She might be on her period"Xeenerh ta fada tana dariya
"Mchew, nifa baku isheni kallo ba, ae sai ku bari in shi wanda yakai nayi dashi ya dawo sai muyi baku kananan kwari ba" nan Teemerh ta fada ta cigaba da danna waya, Ashphert bata ce da ita komai ba ta dau remote ta changing channel, nan fa Teemerh daba kallo takeyi ba ta tashi da sauri ta fauce remote in "Har kin isa ina kallo ki changing channel?" Teemerh ta fada da isa "Aa Teemerh banson fadan rashin gaskia bafa kallo kike ba" Xeenerh ta fada dan duk abunda ke faruwa a idonta "And waya sa bakin ki? Ki mun shiru" Teemerh ta fada tana dallawa Xeenerh harara "Dole tayi shiru ae tunda ba gidan uba ta kike zo ba" nan fa Teemerh taji haushi sai ji kuke Tauuuu a fuskan Ashphert "Nazo gidan naku, kuma na dake ki me kika iy-" ae bata rufe baki ba Ashphert ta rama, Xeenerh ma ta kara mata ta dayan side in, abunka da fara tuni wajen yayi ja, harta dago zatayi bala'i kawae taga Anwaar hakan yasa ta zube a kasa tasa ihu, da sauri Munnirah ta fito jin ana ihu wanda shima Anwaar da sauri ya karaso dan ganin abunda yake faruwa "Kawo mata ruwa" yace wa Munnirah ganin yanda Teemerh ta zage tana ihu, da toh Munnirah ta amsa bata jima ba ta dawo da ruwa "Drink some water" ya bata ruwa amma dake Teemerh ta iya munafurci kadan tayi sipping kardai yace batasha ba, buge ruwan tayi bata sani ba ya zubewa Anwaar a jiki "Oh sh*t" ya fada sannan ya mike ganin abunda Fatima ta masa
"Meya same tane?" Ya tambayi su Xeenerh ganin sune a wajen "Nima yanzu muka fito jin tanata ihu" Ashphert tayi saurin fada, da mamaki Teemerh ke kallonta jin ta samu wanda ta fita, zatayi magana Anwaar ya tsaidata "I've to change, make sure she's fine" ya fadawa Munnirah sannan ya duba yanda rigansa ya jike yayi sama, Munnirah ce tazo zata dagata tace "Don't you dare" sannan ta mike da kanta Ashphert sai dariya takeyi

***
Shiga daki yayi, dakin so calm and fresh dan komai na zaune mazaunin sa, ba abunda ya raba dakin dana Aameer sai yanayin paint, ba abunda yafi daukan hankali kaman bean bag chair dake ah gefe, ciren rigan nasa daya jike yayi dan chanza wani, hakan ya bani daman ganin wani tattoo dake jikinsa an rubuta Ilhaam cikin wani stylish rubutu da hearts haka, hakan ba karamin Rudani ya jefani ba, so what about the hatered he showed her? Yana cikin sa wani rigan Teemerh tayi knocking saidai bai bata izinin shiga ba ta shiga abunta, jin kamshin da dakin yakeyi ya sata lumshe ido, she just love everything about Anwaar, dakin nasa kullum so tidy, barin tunanin tayi da sauri tace "Babe im disappointed"
"For?" Ya tambaya bayan ya gama da rigan nasa "Ace wai sisters naka su cimun mutunci ah gidan nan amma koh tambaya baza yi ba? duka na fa sukayi"
"Mai kika musu toh da zasu dake ki?" Ya tambaya ba tare daya kalleta ba, haushin tambayan taji hakan yasa tayi saurin cewa "Anwaar shin kana sona ma kuwa?" Sai a lokacin ya dago ya kalleta jin abunda tace "You are not serious, dama ni na taba ce ina sanki?" Ya bata answer yana tunanin yaushe yace yana santa, haushi taji amma sam bataso ta nuna masa bacin ranta saboda gudun kar nasa ya baci hakan yasa tace "Toh Ilhaam kakeso?" Ta fada tana tsoron amsan dazai bata "I despise her" ya fa a tsawace "And don't you ever say her name again" "That's a lie Anwaar you love her more than anything else and you know what? Ilhaam has moved then why can't you?"
"Fatima out of my room" ya mata nuni da waje "And bear it in mind koh inson Ilhaam koh bani sonta I will never marry you, in kinada mutunci zakizo dakina? im not ur muharram after all, sai kai koyi da ita halan ki samu dacewa" kuka kawae Teemerh ta fashe da ta fita adakin tana kuka dan tunda har ta bari Anwaar ya furta bazai aureta ba toh nata ya kare, tana mutuwan san Anwaar amma sai abunda yaga dama yake mata, ita kuma ta kasa haqura, tazo sauka kasa ta bege Ashphert, ita ko bata damu ba tace oho dai, dan ita har abada bazata taba san yarinyar nan ba.

⚠️
DRINKING IS INJURIOUS to HEALTH
Alcohol can cause high blood pressure, which increases your risk of having a heart attack or stroke.


Team Ilhaam OR Teemerh guys?

#ilhaam
#teemerh

DON'T forget to vote please

Always remember that you can be ILHAAM or TEEMERH

Team#RDN

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now