💖💫RUDANI💖💫 47

107 24 30
                                    



Saida tayi kukan ta kafin tayi bacci, da asuba bayan ya dawo daga masallaci ya dubata, tana kwance koh sa ran tashi batayi ba dan dama jiya ba wani baccin kirki tayi ba, ah nitse ya karasa ya tashe ta "Get up and pray" dakai ta amsa sannan ya juya ya fita, koma wa bacci abunta tayi, ya barta da bakin cikin daya sata jiya mana amma sai yazo ya dagata bacci bai isheta ba. Ba Teemerh ta tashi ba sai karfe takwas, sallah tayi da wanka ta fito, Anwaar is not around, abincin da ta gani kan dining ta zauna ta ci kafin ta kira Habeey dan yanzu ne taji zata iya saboda jiya duk kuka ta yini yi "Hey babes, kin koma ne?" Habeey tace "Aa Tee sai next week, bana yita kiran ki kina mun ra'ayi ba?"... "Hm sorry zaki samu kizo?" Dan shiru tayi kafin tace "Send me the address, kinsan ranan ban samu nazo ba, that Ahmad guy sai ah hankali".... "Will text it right now" tana gamawa ta mata sending address in. In less than 12mins saiga Habeey "Amarya mey ya samu idonki haka?" Ta tambaya tana sake bin Teemerh da kallo "Anwaar mana" ta amsa ta "Dukan ki yayi?" Teemerh tace "In duka ne da sauki ae" nan ta mata narrating dukkanin abunda ya faru, dariya Beey ta fara har ta bawa Teemerh haushi "Ke toh ae yazo gidan sauki tunda jiya su Mummy suka wuce Niger kan ita Ilhaam in" gyara zama Teemerh tayi dan ita ta manta da tace a koma wajen shi "Kince wai ah koma saboda ya hana Ilhaam haihuwa koh?" Saurin gyada kai tayi "Shine wai har su Mum sun wuce? Lalle basu daukan abu da sanyi" Teemerh ta fada tana rike baki "Yau kika sani? Yanzu kam ma yau ae nasan suna hanya dan tace bataso Daddy ya dawo basu nan, kinsan baisan sun tafi ba, Yaa Xee ma tace na gaishe ki" Teemerh tace "Ina amsawa, amma inace ke ba Chad zaki koma ba?" Tace "Haka Abba dai yakeso, amma zaiyi wuya" Teemerh bata sake cewa komai ba ta fara tunani, dan in ta kasa gane kan Anwaar dole taje wajen mutum chan da kanta ta fayyace masa abunda yake damunta "Ni na zata ma zaki ce mun wani abu ya sameta ne fa".... "Toh ina zan sani ma yanzu kam" ta fadi tana biting finger badan komai ba sai tunawa da tayi da cin mutuncin Anwaar "Ke ni bazan iya haqura bama, barin kirasa ae in akwae matsala zai fada" Habeey tace "Ywwer kirasa" nan tadau waya

Koda ya koma wajen Ilhaam bai kulata ba, ta gaida sa ma amma bai amsa ba, ganin haka bata sake ce masa komai ba itama ta bisa daki, dama fa kiran Yaa Sabeerah tayi ta kai mata k'aran Anwaar, ba abunda ta boye mata har rashin kunyan data masa, amma maimakon tabi bayanta sai tayi siding Anwaar, zagi iri da kala ba wanda bata yiwa Ilhaam shiba sannan tace ta basa haquri "Erm... nifa kawae naga ya dace kaje wajen Teemerh ne" bai amsa ba ya fita hakan yasa ta tabe baki ta zauna, tana zama taji wayan sa ya fara ringing, kaman ance ta duba, ganin mey kira tayi saurin dauka "Hello Babe?" Taji muryan Teemerh "Matar Anwaar ke magana" ta amsa boldly "Tell him his new wife want to talk to him" ta bawa Ilhaam amsa badai da fada ba saidai cike da nuna isan itama matan sane "Toh yace bayison magana dake ana dole ne? Teemerh ki haqura ki gane cewan Anwaar is mine"..... "Don't brag, Anwaar bazai cigaba da zama naki ba, this is my promise" da har Ilhaam zata kashe taji Teemerh ta fada mata magana ta fasa "Toh ae nike yanke hukunci abi, in naga dama sai kinyi sati baki gansa b-" bata karasa ba taga Anwaar yasa ta kashe tayi shiru "In kin gama neman fadan sai ki bani wayana" ya fada extending his hand, ba musu tasa mishi wayan "In ke keda iko dani sai ki hanani fita ae" shiru tayi, da ita ta hanasa fita ne? In yaga dama ya fita kar ya dawo "And you better call and apologize, wa Fatima'n zaki wa rashin ji? Always remember that she's my wife and you have no right to treat her that, ban zo nan saboda nuna miki soyyayyah ba" kallon mamaki ma ta masa, itane zata kira Teemerh ta bata haquri? Ae bata fadi abunda ba dai-dai ba, so takeyi ta b'ata ran Teemerh kuma tayi "In dagaske ne abunda kake fadi toh mey kakeyi anan? Go back to your wife, your bride" yace "Ke kike yanke hukunci ba? Toh sai ki yanke yanzu ta hanyan maidani" ya bata amsa "Cewa fa tayi-".... "Shut up and go and put on your hijab, we are going out" yana fada ya fita, samun waje tayi ta kwanta dan tasan wajen Dr Zahra zasu, yanzu ita taji sauki sosai dan duk komai da takeji yanzu da sauki, tana zama tayi tadi da Aameer dan koh dazu ya kira ya mata warning cewan ba ruwanta da matan Anwaar, shima bata barsa ba dan dama Aameer kam sun saba, yakai 15mins yana jiranta bata fito ba kafin ya dawo dakin, to his ultimate surprise Ilhaam na kwance, bafa bacci takeyi ba, kawae fitan ne baza tayi ba kuma bazata iya ce masa bazata ba, tana ganin sa ta tashi ta fara kame-kame "Wait duk ba abunda na tambaye ki ba kenan, zakije ne koh Aa?" Shiru tayi ta kasa magana ganin ransa ya baci "Zanje, dama kaina ke ciwo" ta fada tana rike cike kuma, ganin kallon da yake mata tayi saurin maida hanun kai "Ke baki ma jin kunyan karya, ciwon kai ya koma ciki koh?" Girgiza kai tayi ganin zai fara mata fada ta fita da gudu ta sako hijab in, shi jiran Ashphert yakeyi kawae ya koya mata hankali dan duk ita tasa ya kasa gane kan matan sa. Saida ya bari ta dauko Hijab in yaga dai ta gama shiri kafin yace ta koma ya fasa, Doctor Zahra zatazo "Shine kasa na wahala? Nifa ban iya halin ka, tun wuri a gyara dan bazan dauka ba" ita kanta batasan maganan ya fito ba, jin ta riga ta fada ba halin maidawa kawae tasa gudu, share abun yayi dan tunawa yakeyi she's a heart patient yasa yake binta ah hankali kar yana mata fada yayi worsening ciwon nata dan ita kanta batasan dashi ba, samun waje yayi ya zauna ya karanto wa Ashphert laifinta bayan ya kirata, ita wai tunani take, wato Anwaar ya zata ma zata rectifying abubuwa ne koh? Toh wlh saida ta sake zugata, ita farin ciki tayi ma ae Ilhaam tadau shawaran ta, haka kawae baza'a kashe mata er uwa ba. Yana zaune Ilhaam ta dawo "Zan fita" shifa yasan for sure if not she's Ilhaam toh da sai ya ballata, banda haka wa yake masa magana haka "Anwaar ina magana ne fa kamun shiru, cewa nayi fa zan fita zani wajen Ashphert dan ban gane bayanan da tamun ah waya ba, wai ma akan wani dalili zaka sata kayita mata fad'a, ae ba laifinta bane nawa ne sai amun" shiru ya mata dan ya lura ya biye mata zata haukata sa, sunan sa ta sake kira kafin ta fadin abunda zata fada yace "Out" kawae tasa kuka "Ae in an hanani fita ita zatazo" tana fada ta fita dan zuwa cigaba da kukan. Bai bita ba saida ya gama abunda yakeyi, kuka tsakani da Allah tayi kafin ta share hawayen, tana ganin ya shigo ta juya masa baya "Na manta ban fada miki ba bansan yawo" tace "Anwaar nifa am not in need of whatever you have in store, all I need is you leaving my house. I want to be alone" yace "I love you, but please make peace with Fatima, ita ma bazata neme ki da fada ba" share sa tayi dan yanzu abunda Anwaar bayi so shi zatayi, ganin batada niyyan amsa shi ya fita mata ah dakin, karan da wayanta yayi ne yasa ta duba- a message from Aameer, tasan fad'an da dazu ya mata yasa yake bata haquri, koh bai fada ba tasan the last sentence was to make her feel better. The message is;

💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now