💖💫RUDANI💖💫 79

49 23 51
                                    


Ae da gudu Leemerh tayi wajen Mummy takai mata bayani "Ta ture Ilhaam ah ina?" Abbas ya tambaya da sauri sannan ya tashi ya fita, girgiza kai Mummy tayi dan abun Asmah ya fara yawa, harta tashi ta koma ta zauna tama rasa mey zatayi "Kira mun ita" juyawa Halimah tayi ta fita dan kiran Asmah. "Mummy gani" ta fada sannan ta zauna "Miye Ilhaam ta miki da zaki mata irin wannan hukunci?" Mummy ta tambaye ta "Daga dakinta fa naga Najeeb ya fito" ta fada da bacin rai "Toh wae Yaa Najeeb in dan ke kadai akayi sa? Sai mun sake masa aure da wasu uku sai ku zama ku hudu aikin banza" Billy da shigowan ta kenan ta fara bayani cike da bala'i "Bilkisu kimun shiru tukunna naji dalilan ta" shiru Asmah tayi dan wae tana ganin mutuncin Mummy ne amma jira take ta tashi tayi maganin sisters din Najeeb "Ilhaam passed out, kuma duk saboda rashin hankalin tane" Billy ta sake fada, da sauri Mummy ta tashi jin wae suma Ilhaam tayi "Yaa Najeeb da Yaa Abbas sun tafi da ita asibiti" dan ajiyan zuciya ta sauke ta koma ta zauna "Mey Ilhaam ta miki Asma'u? Bazaki bari taji da abunda yake damunta ba sai ki sake sata cikin wani tashin hankali? Akan wani dalilin zaki ture mun 'ya?", "Ae bawani dalili daya wuce naga Najeeb ya fito dakinta" ta bata amsa, shiru Mum tayi ta rasa abunyi sai girgiza kai take "Da kika ga Najeeb ya fito dakinta sai mey? Yarinyan nan fa idda take" Mummy ta mata bayani, juyawa tayi irin koh a jikinta "Allah ya shiryeki" ta fada ganin abunda Asmah tayi sannan ta tashi ta fita "Miye kuka zuban ido? Ayi ah aurar daku mu huta, yara sai rashin kunya" girgiza kai Billy tayi kafin ta dauketa da mari "Wa Mummy kike bada wa'innan attitudes in? Toh barin fada miki koh Yaa Najeeb din bai isa yasa hanu ah jikina saboda na mare ki yau ba, wawiyan banza da wofi" rike fuskan tayi da sauri dan koh a mafarki batayi tunanin haka ba dan bata tab'a ba "Ni kika mara?" Ta tambaya da mamakin dai "Dole Najeeb ya dawo ya zaba koh ni koh ku wlh" tabe baki Leemerh tayi ganin yanda ta zage, toh in bai zabe su ba koran su zaiyi? Ganin duk sun shareta ta tashi dan rainin kam bata kaunan sa koh kadan. Tashin suma sukayi suka fita suka fara zaman jiran su dan kowa da damuwan sa kuma, sun kwashe 2hrs suna zaune ba abunda sukeyi kafin Najeeb ya shigo dauke da Ilhaam dan ta musu bacci, Abbas ya biyo bayansa da Hijab da takalmin ta "Yaa Najeeb is she fine? Ina Mummy?" Bai kulasu ba ya wuce da ita Abbas yace "Mun ganta lokacin da zamu shigo wai zata wajen Ammaah, amma bazata dade ba" dan ajiyan zuciya Billy ta sauke kafin tabi su Najeeb Abbas ma ya bita, Najeeb na ajiyeta ta bude ido ta fara kuka ita bazata zauna ba "Ilhaam Asma'u is sorry, bazata sake ba" Najeeb ya bata haquri "Yaa Najeeb that woman will never be sorry, batada hankali koh kadan, ka ajiye mahaukaciya ah gida wae mata, ade duba lamarin" kallonta kawae yayi bai amsa ba, this Asma'u and his sibling's relationship keeps him in awe, tashi Ilhaam tayi ta zauna zata amsa kira amma ganin Anwaar ne ta sake maida wayan gefe "Answer it, he must want to know how you are, if not you then he wants to know about his baby" kallon juna Billy da Leemerh sukayi "Is she pregnant?" Mummy da shigowan ta kenan ta tambaya "She is, the doctor just confirmed it" Najeeb ya amsa, Abbas na gefe yana tunani danshi gaskiya san Ilhaam yake "Mum she must be shy to tell you that she is pregnant" Billy ta matsa kusa da Mum ganin abun ya dameta bata sani da wuri ba, kallon Billy Najeeb yayi jin abunda tace yana mamakin ina ta koyo iyayi "Ilhaam answer this call" Najeeb insisted ganin kiran ya sake shigowa kawae tasa masa kuka, saurin tashi kusa da ita yayi Mummy ta zauna danshi bai iyawa da halin Ilhaam komai kuka "Toh in bazata amsa ba dole zaka mata ne kam?" Mummy ta masa tsawa ganin yanda ya dage "I am sorry" ya fada sannan ya fita "Kai kuma zaman mey kakeyi?" Ta fada ganin shi Abbas baida niyyan tashi ma, tashi yayi shima a nitse ya fita "Ilhaam ya jikin?" Tace "Da sauki, zan koma Abuja" ta fada kaman mey shirin sake kuka "Ba yanda zakije, Asma'u kuma zanyi maganinta in ta nemi matsa miki, mey ma zakiyi da wani Najeeb" Mummy ta fada dan kwantar mata da hankali "Sleep and have some rest. Don't stress yourself and I will help you in taking care of your baby In Shaa Allah" ta fada sannan ta kwantar da ita "Ku fito ku barta ta huta" ta fada tana gyara mata hanun da aka nadesa da gauze bandage "Asma'u muguwa ce na karshe" Leemerh ta fada ganin hanun "Duk kuyi haquri" Mummy ta sake basu baki, Billy ce ta fara fita kafin Leemerh ta bita "Allah ya miki albarka" ta shafa kan Ilhaam kafin itama ta fita. Najeeb kuwa koda ya fita side nasu yayi, nan ya samu Asma'u nakan cika da batsewa, tana ganin sa ta tashi "Wlh yau Najeeb saidai ka zaba koh ni koh su Bilkisu" kallon mamaki ma ya bita dashi dan yanzu ya fahimci wannan rashin hankalin ta kara yawa yake, har wani hada kai zatayi dasu Bilqis? "Move out of my way" ya fada ganin ta tare masa hanya ta hanasa wuce wa "Allah Najeeb sai ka fadamun abunda ke tsakanin ka da wancan er iskan yarinyan da aka fake da auren tane ya kare aka kawota nan" girgiza kai kawae yayi "Ba abunda yake tsakanina da ita sannan kar ki sake rashin hankalin da kikayi yau, that girl is pregnant and you pushed her. Suma tayi fa, ga kuma ciwon da kikaji mata" ware ido tayi ta matsa baya "Najeeb fada mun tun yaushe kake tare da yarinyan nan da kuma cikin uban waye ah jikinta dan na kasa ganewa, zan iya rantsewa cikin shege ne" mamaki iya mamaki Najeeb ya fara shi "Yarinya ta fito daga gidan mijinta ki zauna kina fadin wasu shirme Asma'u?" Juya ido ta fara "Toh karya nayi? Nasani koh kai ka mata cikin mijin nata yaga bazai iya ba ya saukota shine ta zo ka raini abunka" jira yayi ta karasa sentence in nata kafin ya dauketa da mari, sake bata daya yayi ta dayan side in, ihu ta fara jin zafin marukan "Wlh sai ka gane ka mareni-" ta fada zata juya Najeeb ya sake rikota ya kara mata wani "Do your worst, and stick this to your stupid brain that the girl you are talking about is my cousin, inda so ake na aureta ae ansan da zaman ta nine bansani ba, kinga kenan da ita za'a ce na aura bake. Let me even ask you a question, who told you I married you for love? I Married you at my Mother's behest because I can't say no to her, you and your marriage are forced on me Asma'u, I tried my best to be the best husband for you not because I love you No, because I don't want to hurt you amma ke baki gani. I am not feeling your love but don't make me hate you for your enmity with my sisters. I love them and a poor laugh for you to think I will choose you over them. It's now left for you to decide whether to leave or stay" yana fada ya saketa ya wuce, kawai ta durgusa ta fara kuka.


💖💫RUDANI💖💫Where stories live. Discover now